EFCC Ta Maka Akanta Janar a Kotu kan Zargin Gwamnatin Bauchi da Wawushe N8.3bn
- Hukumar EFCC ta gurfanar da babban Akanta na Bauchi a gaban kotu kan zargin halasta kudin haram da karkatar da dukiyar jama'a
- EFCC ta na zargin an yi amfani da wani kamfani mai suna Jasfad Resources Enterprise wajen almundahanar Naira biliyan 8.3
- Akanta Janar, Sirajo Muhammad da sauran wadanda ake zargi sun musanta tuhumar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar yaki da in hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da Sirajo Muhammad Jaja, babban Akanta na jihar Bauchi, a gaban kotu kan zargin karkatar da kuɗi har N8.3bn.
A ranar Litinin ne EFCC ta gurfanar da Jaja tare da wani mai gudanar da harkar canjin kuɗi, Aliyu Abubakar, da kamfaninsa mai suna Jasfad Resources Enterprise.

Source: Twitter
EFCC ta bayyana a shafinta na intanet cewa an gurfanar da su ne bisa tuhume-tuhume tara da suka shafi halasta kuɗin haram da laifukan da suka shafi karkatar da dukiyar jama’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana kuma zarginsu da karkatar da kuɗin gwamnati da kuma almundahanar kuɗi da darajarsu ta kai N8,380,626,430.95.
EFCC: An maka jami'in gwamnatin Bauchi a kotu
Jaridar The Cable ta wallafa cewa, an gurfanar da su ne a gaban mai shari’a O.A. Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Kunshin tuhumar da ake masu ya ce:
“Kai, Aliyu Abubakar, Jasfad Resources Enterprise (kamfanin canjin kuɗi), da Ibrahim Kashim (tsohon sakataren gwamnatin jihar Bauchi, ), wani lokaci tsakanin 5 ga Janairu, 2024, da 10 ga Disamba, 2024, kun aikata laifi na halatta kuɗin haram ta hanyar sauya fasali da tura kuɗi har N2,808,595,100.00 daga asusun kuɗi na gwamnatin jihar Bauchi da ke bankin UBA mai lamba 1022197086 zuwa asusun kamfanin Jasfad Resources Enterprise da ke wannan banki mai lamba 1023444660, kuma hakan ya saba da sashe na 18(2)(b) kuma hukunci yana ƙarƙashin sashe na 18(3) na dokar karewa da hana halasta kudin haramn ta shekarar 2022.”

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya a kan hanya, 'yan sanda sun dauki mataki
Sauran jami'an Bauchi da ake zargi a EFCC
EFCC ta ƙara da cewa wasu da ake zargi a cikin wannan batu sun haɗa da Ibrahim Kashim, tsohon sakataren gwamnatin jihar Bauchi; Aminu Hammayo, sakataren gwamnatin yanzu.
Sai kuma wani Saleh Mohammed da Balarabe Abdullahi wanda a yanzu haka suka tsere yayin da ake nemansu ruwa a jallo.

Source: Facebook
Dukkan waɗanda hukumar ta EFCC ke zargi da aikata almundahanar sun musanta laifuffukan da ake tuhumarsu da su a gaban kotu.
EFCC ta cafke Akanta Janar na Bauchi
A wani labarin, kun ji cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa ta cafke Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Muhammad Jaja, bisa zargin badakalar N70bn daga baitul mali.
An kama Jaja tare da wasu mutane biyu: Aliyu Abubakar, wanda ke gudanar da kamfanin Jasfad Resources Enterprise, da kuma wani mai sana’ar POS, Sunusi Ibrahim Sambo.
Binciken EFCC ya nuna cewa an fitar da N59bn daga asusun banki daban-daban da Sirajo Jaja ya bude a madadin gwamnatin Bauchi, zuwa ga Aliyu Abubakar da Sunusi Sambo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
