Uromi: An Barke da Zanga Zanga bayan Matakin ’Yan Sanda da Aka Kashe Hausawa

Uromi: An Barke da Zanga Zanga bayan Matakin ’Yan Sanda da Aka Kashe Hausawa

  • Yan sa-kai a Uromi da ke jihar Edo sun shiga zanga-zanga bayan 'yan sanda sun kwace musu makamai
  • Sun ce sun yi aiki tare da 'yan sanda shekaru da dama wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin na Uromi
  • Sabon Kwamishinan 'yan Sanda, Monday Agbonika, ne ya umarci a kwace makamansu har guda 2,000

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin-City, Edo - Yan sa-kai a Uromi dake jihar Edo sun fito zanga-zanga bayan matakin kwamishinan yan sanda a jihar.

Hakan ya biyo bayan matakin kwamishinan 'yan sanda na jihar, Monday Agbonika da ya yi umarni da kwace musu makamai.

Yan sa-kai a Uromi sun yi zanga-zanga a Edo
Yan banga sun barke da zanga-zanga bayan yan sanda sun kwace musu makamai a Edo. Hoto: Legit.
Asali: Original

Zanga-zangar na zuwa ne yayin da jihar Edo ke fama da matsalolin tsaro daban-daban da suka addabi al'umma a yankunan, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kisan Hausawa ya jawo maganganu a Edo

Kara karanta wannan

'A dawo mana da Fubara': Zanga zangar adawa da Tinubu ta barke a Rivers

Zanga-zangar na zuwa ne makonni kadan bayan yan sa-kai a Uromi sun kama wasu daga jihar Kano, suka yi musu kisan gilla.

Lamarin da ya jawo kisan wasu mutum 16 ya jawo maganganu ciki har da fushin manyan Arewa kamar kungiyar dattawa ta ACF.

Daga bisani, gwamnatin Edo ta tabbatar da tura wasu da ake zargi zuwa Abuja domin ci gaba da bincike da kuma hukunta su

Abin da ƴan sa-kai ke cewa a Uromi

Wani daga cikin yan sa-kan ya ce:

"Muna nan har sai an amsa bukatunmu, na shafe shekara 21 ina aikin sa-kai."

Sun bayyana cewa shekaru da dama suna aiki tare da 'yan sanda, musamman DPOs, wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Da yawa daga cikin yan sa-kan sun bayyana cewa gwamnati ta horar da su kan amfani da makamai da dabarun tsaro.

Sai dai bayan zuwan sabon kwamishina, Agbonika, ya umarci a kwace makaman domin sake tsara harkar tsaron jihar Edo.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan abubuwa 4 da suka girgiza jama'a a makonni 2

Yan sa-kan sun ce sun mika makaman lafiya, amma sai Kwamishinan ya bayyana a TV yana alfahari da kwace bindigu 2,000.

Yanzu haka suna cikin fargaba da tsoro saboda labaran cewa wasu fursunoni sun tsere daga hannun 'yan sanda.

Mai magana da yawunsu ya ce:

"Ba mu cikin tsaro yanzu, muna bukatar a dawo mana da makamanmu."

Wani daga cikinsu ya ce:

"Na kwashe shekara 21 a aikin, har yanzu akwai harsasai sama da 15 a hannuna."
An barke da zanga-zanga a Edo bayan kisan Hausawa a Uromi
Matakin yan sanda na kwace makaman yan sa-kai ya jawo zanga-zanga a Edo. Hoto: @babarh_.
Asali: Twitter

Matsalolin da ƴan sa-kai ke fuskanta a Edo

A wani rahoton da muka samu daga Sahara Reporters, wani mai zanga-zanga ya ce kwace makaman ya hana su taimaka wa 'yan sanda.

Ya ce:

"Tun farko muna aiki da DPO, duk inda aka kira mu, sai mu je mu taimaka wajen dawo da zaman lafiya.
"Mun fito lokacin rikicin Ikpoba-Okha don taimaka wa DPO wajen tabbatar da zaman lafiya.
"Bayan horo, gwamnati ta koya mana dabaru sannan ta ba mu takardar shaidar kammala horo."

Kara karanta wannan

An shiga firgici da ƴan bindiga suka sace hadimar gwamna, sun bukaci N30m

Abokan mafarauta sun magantu kan ɗaukar fansa

Kun ji cewa abokan aikin mafarautan da aka kashe sun yi gargaɗin ɗaukar fansa idan har ba a cafke waɗanda suka aikata kisan gillar ba.

Matasan sun nuna cewa sun san hanyoyin da za su bi su je har Uromi domin zaƙulo waɗanda ke da hannu a kisan gillar.

Hakan na zuwa bayan kisan gilla da aka yi wa wasu Hausawa a garin Uromi da ke jihar Edo a karshen watan Maris.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng