'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa, Sun Hallaka Mutum 4 Tare da Sace Wasu Masu Yawa
- Ƴan bindiga sun kai hari a wani ƙauyen da ke cikin ƙaramar hukumar Dandume ta jihar Katsina da ake ta kukan rashin tsaro
- Miyagun sun hallaka mutum huɗu tare da yin awon gaba da wasu mutane kusan 50 a harin da suka kai a daren ranar Lahadi
- Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da aukuwar harin, inda ta ce jami'anta na ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kai hari a ƙaramar hukumar Dandume ta jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun kashe mutum huɗu tare da yin awon gaba da wasu aƙalla mutane 45 a garin Maikuma da ke ƙaramar hukumar Dandume ta jihar Katsina.

Asali: Twitter
Jaridar Leadership ta rahoto cewa harin ya faru ne a daren ranar Lahadi, lokacin da wata babbar tawagar ƴan bindiga ɗauke da makamai suka shigo garin a kan babura.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Katsina
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ƴan bindigan sun riƙa shiga gida-gida suna kai hari har na tsawon sa’o’i kafin su tsere zuwa dajin da ke kusa da yankin tare da mutanen da suka sace.
Shugaban ƙaramar hukumar Dandume, Basiru Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin.
"Ƴan bindigan sun zo da yawa, wata ƙila fiye da mutum 100. A bayyane yake cewa manufarsu ita ce su yi mummunar ɓarna."
"Sun kashe mutane huɗu sannan suka sace kusan mutum 43, duk da cewa wasu rahotanni na cewa adadin na iya kai wa mutum 45 ko fiye da haka."
- Basiru Musa
Ya bayyana cewa ya sanar da DPO da kuma kwamandan soji na yankin tun da wuri bayan samun bayanan sirri kan yiwuwar kawo harin na ƴan bindiga.
Sabiu Musa ya nuna damuwa kan yawan hare-haren ƴan bindiga, ya buƙaci hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro domin kare al’ummomin da ke fuskantar barazana a faɗin jihar.

Kara karanta wannan
"Abin tausayi": Mutane sun yi magana, an ji yadda aka kashe bayin Allah sama da 50

Asali: Facebook
Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin
Legit Hausa ta samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq-Aliyu, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya tabbatar da sace mutanen da ƴan bindigan suka yi a harin da suka kawo.
Ya bayyana cewa jami'an rundunar na bakin ƙoƙarinsu domin ganin sun kuɓutar da mutanen da aka sace.
"Eh lamarin ya auku, sun kashe mutum huɗu tare da sace wasu mutum 43, kuma jami'an mu na bakin ƙoƙari domin kuɓutar mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma kama waɗanda ke da hannu a harin."
- DSP Abubakar Sadiq-Aliyu
Ƴan bindiga sun kashe mutane a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun farmaki bayin Allah a jihar Ƙatsina
Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne cikin dare a ƙauyen Unguwar Doruwa cikin ƙaramar hukumar Kankia.
A yayin harin, ƴan bindigan waɗanda suka zo kan babura sun hallaka mutane tare da raunata wasu mutum biyu da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng