Wata Sabuwa: An Lalubo Laifuffukan Ministan Tsaro, Ana So Tinubu Ya Bincike Shi

Wata Sabuwa: An Lalubo Laifuffukan Ministan Tsaro, Ana So Tinubu Ya Bincike Shi

  • Kungiyar CRACON ta roki shugaba Bola Tinubu da ya kafa kwamitin bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa ministan tsaro
  • CRACON ta yi ikirarin cewa Muhammed Abubakar Badaru, yana ci gaba da gudanar da kasuwanci na sirri wanda ya saba wa doka
  • Kamar yadda aka binciki tsohuwar minista, Betta Edu, kungiyar ta nemi Tinubu ya binciki Badaru domin fito da gaskiya kan zarge-zargen

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar CRACON, ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin bincike na musamman kan zarge zargen da ake yi wa ministan tsaro, Muhammed Abubakar Badaru.

Kungiyar ta zargi ministan da amfani da cin zarafin ofishinsa da kuma yin kasuwancin da ya saba wa tsarin aikin gwamnati, wanda hakan zai iya keta dokokin kasa.

Kara karanta wannan

'Ka da ka jawo mana rigimar addini': 'Yan sanda ga malamin Musulunci a Gombe

Kungiya na so Tinubu ya binciki ministan tsaro.
Kungiyar CRACON na so Tinubu ya binciki ministan tsaro, Mohammed Badaru. Hoto: Ashiru Usman Sabuwar Gwaram
Asali: Facebook

Ana so Tinubu ya binciki ministan tsaro

A cikin wata sanarwa, Folashade Olumiya, shugabar CRACON, ta roki shugaban kasa da ya kafa kwamitin bincike don duba ayyukan ministan, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Folashade Olumiya ta jaddada bukatar ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatin, inda ta tuna da binciken da aka yi wa tsohuwar ministar jin kai, Betta Edu.

"Tun da har an kafa kwamitin bincike kan Betta Edu, to ya kamata a yi hakan kan ministan tsaro Muhammed Badaru," a cewar Folashade.

Kiran CRACON ya biyo bayan wani zargin da kungiyar YGA ta yi wa Badaru na ci gaba da gudanar da kasuwanci a sirrance, ciki har da gudanar da wani kamfanin canjin kudi, alhalin yana minista.

Abin da zarge-zargen Ministan zai haifar

Kungiyar ta bayyana cewa irin wannan aiki ba sabawa ka'idojin doka ya yi kadai ba, har ma yana iya cutar da martabar shirin gwamnati na yaki da cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

'A tabbatar da adalci duniya ta gani,' Abba Gida Gida kan kisan Uromi'

Haka kuma, CRACON ta nuna damuwa cewa idan ba a dauki mataki mai kyau akan wannan batu ba, zai iya rage yardar al'umma kan gaskiya da rikon amanar gwamnati.

"Rashin bincikar ministan tsaro kan wannan lamarim kamar yadda aka yi wa sauran jami'an gwamnati zai haifar da ra'ayin cewa ana zabar wadanda ake tuhuma ne kawai."

- Folashade.

'A tilastawa Badaru yin murabus' - CRACON

Kungiya ta nemi Tinubu ya binciki ministan tsaro, Badaru.
Ana so Badaru ya yi murabus idan an same shi da laifi a zargin da ake yi masa. Hoto: Defence Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

CRACON ta dage cewa bai kamata ya kasance hukumomi yaki da rashawa irin EFCC da ICPC ne kawai za su binciki Badaru kan wannan zargi ba.

A maimakon haka, sun ba da shawarar Shugaba Tinubu ya kafa kwamitin bincike mai 'yanci don tabbatar da cewa an gudanar da komai cikin gaskiya.

CRACON ta roki Shugaba Tinubu da ya dauki mataki cikin gaggawa, kuma idan zargin ya tabbata, ya tilasta wa Badaru yin murabus don a gudanar da bincike mai zurfi.

Kara karanta wannan

'Ka gaggauta daukar mataki': An fadawa Tinubu abubuwa 2 da ke barazana ga Najeriya

A karshe, kungiyar ta roki Shugaba Tinubu da ya nuna jajircewar gwamnatinsa wajen tilasta wa dukkan jami'an gwamnati bin doka, ba tare da la'akari da matsayin su ko tasirinsu ba.

Dalilin Tinubu na ba Badaru ministan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana dalilan da suka sa aka nada shi minista a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

A cewarsa, jajurcewa da ƙwarewa wajen tafiyar da al’amuran mulki ne suka ba shi damar samun wannan muƙami mai muhimmanci.

Badaru ya kara da cewa nasarorin da ya cimma a lokacin da yake gwamnan jihar Jigawa sun taka muhimmiyar rawa wajen jawo hankalin shugaban kasa gare shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel