Kano: Gwamnati Ta Hada Tawagar da za Ta Bibiyi Diyyar Mutunen da aka Babbaka a Edo

Kano: Gwamnati Ta Hada Tawagar da za Ta Bibiyi Diyyar Mutunen da aka Babbaka a Edo

  • Gwamnatin Kano ta shirya tattaunawa da Gwamnatin Edo don tantance adadin diyya da za a biya iyalan mafarautan 16 da aka kashe a Uromi
  • Matakin na zuwa ne bayan gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya yi takakkiya zuwa Kano domin ta'aziyyar mutanen da aka kashe a jiharsa
  • Kwamishinan yada labaran Kano, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya tabbatar da cewa mataimakin gwamna ne zai jagoranci tawagar jihar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta ce nan ba da jimawa ba za ta shiga tattaunawa da gwamnatin Edo domin tantance adadin diyya da za a biya iyalan mafarautan 16 da aka kashe a Uromi.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya ne ya bayyana hakan, a karin bayanin da ya yi kan matakin da gwamnati ke dauka.

Kara karanta wannan

'A tabbatar da adalci duniya ta gani,' Abba Gida Gida kan kisan Uromi'

Gwamnati
Gwamnati ta kafa kwamitin bibiyar diyyar mafarautan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf/Fahd Muhammad
Asali: Facebook

A tattaunawar da ta kebanta ga jaridar Punch, Waiya bai bayyana adadin kudin da za a bai wa kowane iyali ba, haka kuma bai fadi ranar da za a fara ganawar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ya bayyana cewa, tawagar Kano za ta samu jagorancin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo don tattauna diyyar.

Za a biya diyyar mafarautan Kano

Kwamishina Waiya ya ce, a halin yanzu ba a tantance adadin diyya da za a bai wa iyalan mafarautan da gwamnatin Edo ta sako ba.

Ya ce:

“Za a kayyade adadin diyya yayin wani taro da za a yi da kwamiti na musamman da gwamnatin jihar Kano ta kafa karkashin jagorancin mataimakin gwamna tare da hadin gwiwar jami’an gwamnatin Edo.”

Gwamnati ta yi martani ga mafarautan Kano

Gwamnatin Kano ta yi magana a kan masu shirin daukar fansa kan kisan mafarutan jiharta a garin Uromi da ke jihar Edo a watan da ya gabata.

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas

A cewar Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya;

“Mun lura cewa da yawa daga cikin wadanda ke kira da a yi ramuwar gayya ba ’yan uwan mamatan ba ne kai tsaye. Ya kamata ’yan jarida su kula da irin mafarautan da suke zantawa da su.
Gwamnatin Kano da ta Edo sun kai ziyara tare zuwa yankunan da lamarin ya shafa a Kano, inda muka gana da iyalan wadanda aka kashe, muka yi musu ta’aziyya, tare da tabbatar musu da cewa gwamnati za ta bi musu hakki.”

Kwamishinan ya ce iyalan sun karɓi sakon gwamnati da hannu bibbiyu tare da nuna godiya, kuma sun yi alkawarin hada kai da hukumomi wajen tabbatar da zaman lafiya.

Wadanda za su bibiyi hakkin mafarautan Kano

Gwamnatin Kano ta kafa tawaga karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo domin bibiya da tattaunawa kan diyyar mafarautan jihar.

Tawagar na dauke da wakilai daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam, Kwamishinan yada labarai, da kuma wakilai daga yankunan da mamatan suka fito.

Kara karanta wannan

Abin da Sarki Sanusi II ya faɗa wa Gwamma Abba bayan ya yi hawan Sallah a Kano

Gwamna
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sunusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Gwamnatin ta ce za a kaddamar da tawagar nan bada dadewa ba, kuma ana sa ran za ta ziyarci jihar Edo domin ganawa da shugabannin al’ummar Hausawa da jami’an gwamnati.

Kwamred Waiya ya kuma bayyana cewa gwamnatin Edo ta amince da biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe, wani mataki da ya ce zai taimaka wajen rage radadin da suke ji.

'A yi wa Kanawa adalci,' Gwamna Abba

A baya, kun samu labarin cewa gwamnatin Kano ta bayyana jin dadin matakan gaggawa da aka dauka bayan kisan gillar da aka yi wa ’yan asalin Kano 16 a garin Uromi, jihar Edo.

A gefe guda, gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana alhini da damuwa kan wannan kisan, yana mai jaddada bukatar aiwatar da adalci tare da biyan hakkokin wadanda aka kashe.

Duk da ya gode kan matakan da gwamnatin Bola Tinubu da ta jihar Edo ta dauka kan batun, ya ce akwai bukatar a hukunta dukkanin wadanda suka aikata laifin, kowa ya gansu a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng