'A Dawo Mana da Fubara': Zanga Zangar Adawa da Tinubu Ta Barke a Rivers

'A Dawo Mana da Fubara': Zanga Zangar Adawa da Tinubu Ta Barke a Rivers

  • Matasa a jihar Rivers sun fito zanga-zanga, inda suka ce gwamnati ta tauye musu haƙƙi, tare da neman a dawo da Gwamna Sim Fubara
  • An ce 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Fatakwal da barkonon tsohuwa, sannan sun bugi wasu, har da ‘yan jarida
  • Masu zanga-zangar sun ce sun sanar da ‘yan sanda tun ranar 3 ga Afrilu, kuma zanga-zangar lumana ce don kare dimokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Rahotannin da muke samu a safiyar Litinin, 7 ga watan Afrilu, na nuni da cewa sabuwar zanga zanga ta barke a jihar Rivers.

An ce jami’an rundunar ‘yan sandan jihar sun harba barkonon tsohuwa a kan wasu masu zanga-zanga a filin Isaac Boro da ke Fatakwal.

Masu zanga zanga sun mamaye titunan Fatakwal, jihar Rivers
'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a jihar Rivers. Hoto: @PstDayoEkong
Asali: Twitter

Masu zanga-zangar da ke karkashin ƙungiyar 'Take It Back' sun taru da safiyar Litinin, misalin karfe 9:00am, amma suka yi kicibis da dandazon ‘yan sanda, inji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Matasa sun bijirewa ƴan sanda, sun mamaye titunan Abuja da wasu jihohi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rivers: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga

Matasa masu zanga-zangar sun ce:

“Ba wanda zai hana mu gudanar da gangami a ƙasarmu. Mu ‘yan jihar Rivers ne."

A yayin da matasan ke furta wadannan kalamai, da kuma dogewa a kan zanga-zangarsu, an ji 'yan sandan da ke wajen suna gargadinsu a kan su watse.

Ganin wankin hula na niyyar kai su dare, an ce ‘yan sandan sun fara fatattakar masu zanga-zangar tare da dukan wasu daga cikinsu, ciki har da ‘yan jarida da ke ɗaukar rahotanni.

Hakazalika, an rahoto cewa, 'yan sandan sun kuma yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar da ma masu nadar rahotannin.

Masu zanga-zangar sun shaida wa jami'an cewa sun sanar da rundunar ‘yan sanda game da niyyarsu ta gudanar da zanga-zanga cikin wasika mai kwanan wata 3 ga Afrilu, 2025.

Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya shaida wa manema labarai cewa:

Kara karanta wannan

Matasa sun rikita Abuja da zanga zanga, an fara harba barkonon tsohuwa

"Zanga-zangar lumana ce, domin bayyana korafe-korafenmu ga gwamnati, ba mu fito neman tashin hankali ba."

"A dawo mana da Fubara" - Masu zanga zanga

Masu zanga zanga a Rivers na so a dawo masu da Gwamna Siminalayi Fubara
Masu zanga zanga a Rivers sun nuna adawa da mulkin Tinubu, suna so a dawo da Fubara. Hoto: @YeleSowore
Asali: Twitter

Masoyin zanga-zangar ya bayyana wasu daga cikin korafe-korafensu da suka haɗa da dokar laifuffukan yanar gizo da kuma dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara.

Matashin ya kara da cewa:

"Yanzu haka, babu gwamnati a jihar Rivers. Wannan gwamnatin tamu ba ta wakiltar al’ummar jihar; ba bisa doka aka kafa ta ba.
Mun zo ne domin mu nemi a dawo mana da gwamnanmu, ya jagorance mu bisa yadda ya dace. Muna da kyakkyawar alaka da gwamna, ba mulkin kama karya muke so ba. Mulkin demokradiyya muke so."

Irin wannan zanga-zanga ta fara gudana a Legas, Oyo da wasu jihohi na Najeriya inda masu zanga-zangar ke adawa da gwamnatin Bola Tinubu.

Masu zanga-zanga sun mamaye Abuja, Legas

A wani labarin, mun ruwaito cewa, masu zanga-zanga sun mamaye titunan babban birnin tarayya Abuja da kuma birnin Ikeja, na jihar Legas.

An ce Omoyele Sowore, jagoran kungiyar 'Bring It Back' da ke gudanar da zanga zangar da lauyan kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju, sun shiga zanga-zangar a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.