Peter Obi Ya Tsoma Baki a Rikicin Sarautar Kano bayan Janye Gayyatar Sanusi II
- Tsohon dan takarar shugaban kasa Peter Obi ya jinjinawa rundunar ‘yan sanda bisa janye gayyatar da ta yi wa Muhammadu Sanusi II
- Obi ya ce akwai hikima a cikin matakin da 'yan sanda suka dauka, musamman ganin irin yanayin rashin kwanciyar hankali a kasar
- Ya kuma bukaci a bar manyan jami’an tsaro na jihohi da yankuna su rika warware irin wadannan matsaloli domin tabbatar da zaman lafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya bayyana jin dadinsa kan matakin da ‘yan sanda suka dauka na janye gayyatar Mai Martaba Muhammadu Sanusi II.
A cewar Obi, hakan ya nuna ana amfani da basira da hangen nesa wajen tafiyar da lamuran tsaro a cikin mawuyacin lokaci da ake fama da tashe-tashen hankali a sassa daban-daban na kasar.

Kara karanta wannan
'Masarauta ta girmi haka': Shehu Sani kan gayyatar Sarki Sanusi II, ya nemo mafita

Asali: Facebook
Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a X, inda ya jaddada cewa akwai jami’an tsaro da suka dace da irin wadannan ayyuka a matakin jiha da shiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya yaba da janye gayyatar Sanusi II
Peter Obi ya ce gayyatar da rundunar ‘yan sanda ta aikawa Sanusi II, a irin wannan lokaci mai cike da rudani, na iya tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin jama’a.
Obi ya ce:
“Na yaba da matakin janye gayyatar. A wannan yanayi na tashin hankali a cikin al’umma, gayyatar ba ta da muhimmanci,
"Kuma da za ta iya kara zafafa wutar rikici da tashin hankali.”
Obi ya jaddada cewa akwai cikakkun jami'an ‘yan sanda a matakin jiha kamar na Kano, wadanda ke da iko da kuma kwarewa wajen warware irin wannan lamari cikin hikima.
Bukatar barin jihohi su warware matsaloli

Kara karanta wannan
'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi
Obi ya bayyana cewa amfani da tsarin da ya bai wa jami’an tsaro a jihohi da yankuna damar warware matsaloli cikin ikon da doka ta basu, zai karfafa zaman lafiya.
Baya ga haka, Peter Obi ya kara da cewa hakan zai kara nuna amincewar jama’a ga hukumomin tsaro.
“Muna da kwamishinoni da AIG da ke kula da jihohi da yankuna. Su ya kamata su rika shawo kan wadannan matsaloli.”
Obi ya ce irin wannan tsarin zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsafta a tafiyar da mulki da harkokin tsaro.

Asali: Twitter
Peter Obi ya bayyana jin dadinsa bisa yadda rundunar ‘yan sanda ta nuna hangen nesa da kuma kulawa wajen janye gayyatar da aka fara aikawa Sanusi II.
Ya ce wannan mataki zai karfafa amincewa da hukumomin tsaro a zukatan jama’a tare da rage zaman dar-dar da tashin hankali a cikin kasa.
'Yan sanda sun kama mahaifi kan kisan kai
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta jihar Legas ta kama wani mahaifi bisa zargin kashe 'yarsa.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin mahaifin da kashe 'yarsa mai shekaru 27 tare da birne ta a wani rami.
Bayan tono gawar da daukan hoton wajen, 'yan sanda sun mika gawar asibiti domin bincike inda suka ce za su fitar da rahoto a gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng