An Shiga Murna da Abinci Ya Sauko a Wasu Jihohi 2, Shinkafa Ta Koma N67,000

An Shiga Murna da Abinci Ya Sauko a Wasu Jihohi 2, Shinkafa Ta Koma N67,000

  • Farashin buhun shinkafa, musamman 'yar kasar waje, ya ragu zuwa N82,000-N85,000 daga tsohon farashinta na N95,000-N100,000
  • A Legas da Enugu, farashin garin kwaki da doya ya ragu sosai; doya daga N7,000 ta koma N3,000, garin kwaki fari ya koma N2,300-N2,500
  • Wake, dawa, gero da alkama duk sun rage farashi; ana sayar da robar wake yanzu a kan N1,000-N1,400 yayin da gyada ta koma N7,200

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - A hankali, farashin kayan abinci a Najeriya na ci gaba da sauka, bisa binciken kasuwa da aka gudanar a Legas da wasu manyan birane.

A makon da ya gabata, ana sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 (doguwar shinkafa 'yar waje) tsakanin N82,000 zuwa N85,000 a kasuwannin Ogba, Ile-Epo da Iddo a Legas.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya za su siya fetur da araha bayan faduwar farashin gangar mai

An ji farashin kayan abinci a jihohin Legas da Enugu
Farashin shinkafa, wake, doya da sauran kayan abinci ya sauka kasa warwas. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Farashin shinkafa ya sauka kasa

A karshen shekarar bara, rahotannin jaridar The Nation sun nuna cewa an sayar da irin wannan shinkafar tsakanin N95,000 zuwa N100,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, shinkafa mai gajeren jiki 'yar waje ta sauka tsakanin N65,000 zuwa N67,000 yanzu, yayin da a baya ta kai N80,000 zuwa N90,000.

Shinkafa 'yar gida kuwa, wadda a baya ake siyarwa tsakanin N90,000 zuwa N100,000, yanzu ta koma kusan N89,000. Amma shekaru uku baya, babu buhun shinkafa da ya wuce N50,000.

Farashin garin kwaki da doya ya sauka

A watannin baya na shekarar da ta gabata, doya ta yi tsada matuƙa, inda ake sayar da tushiyar doya ɗaya a kan N7,000, amma yanzu ta koma N3,000.

A yanzu, bokitin fenti na garin kwakwaki (ja) a Legas yana kai N3,000, yayin da farin garin kwaki ake sayar da shi kan N2,500.

A Jihar Enugu, ana sayar da farin garin a kan N2,300 yayin da ja yake N2,800. A wannan lokaci a bara, a Legas, an sayar da jan gari a kan N4,000 yayin da aka sayar da fari a kan N3,000.

Kara karanta wannan

An yi albishir da saukar kudin sufuri da kayayyaki bayan karyewar farashin mai

Wake, gero, gyada sun rage kudi

An samu faduwar farashin kayan abinci a wasu jihohin Najeriya
An samu faduwar farashin kayan abinci, kamar su wake, shinkafa, gero da sauransu. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Babu wanda zai manta da yadda wake ya yi tsada fiye da kima watanni biyar da suka gabata har wasu gidaje suka cire shi daga jerin abincinsu.

Kwano ɗaya na "D’Rica" da a baya ake siyarwa tsakanin N500 zuwa N800 ya tashi zuwa N2,000–N2,500, amma yanzu ana siyar da shi tsakanin N1,000 zuwa N1,400.

Robar fenti ta gero ko dawa da a baya ake siyarwa N4,500 yanzu ta koma N4,000. Robar fentin waken soya ya sauka zuwa N6,000 daga N6,500.

Haka kuma, robar fenti, cike da alkama da a baya ake siyarwa N5,500 yanzu ya ragu zuwa N5,000. Robar fenti ta sabuwar gyada yanzu ta koma N7,200, sabanin N7,500.

Dalilin faduwar farashin kayan abinci

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an samu saukar farashin kayan abinci irinsu shinkafa, dawa da wake a kasuwannin Adamawa, Yobe da Borno.

A yayin da aka bayyana dalilin saukar farashin kayan abincin, an ji cewa, a kasuwar Jimeta a Adamawa, buhun masara ya ragu zuwa tsakanin N50,000-53,000 daga N60,000-N65,000.

'Yan kasuwa sun ce raguwar farashin ya biyo bayan karancin kudin jari, karuwar noma da kuma rarraba abinci kyauta a cikin watan Ramadan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng