Covid-19: Gwamnatin tarayya ta raba wa talakan Najeriya garin rogo da sauran kayan abinci

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta raba wa talakan Najeriya garin rogo da sauran kayan abinci

Gwamnatin tarayya ta fara rabon tan 70,000 na kayan abinci iri daban-daban ga talakawan Najeriya, daga cikin kokarin da take yi na rage masu radadin rashin walwala a wasu jihohi.

Ministan noma da ci gaban kakkara, Sabo Nanono, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, a wajen taron mika sama da tan 12,500 na kayan abincin a Minna jahar Neja.

Ya ce tan 12,500 na kayan abincin sun hada da tan 10,000 na masara da tan 2,500 na garin rogo, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kara da cewar, an kaddamar da sakin tan 70,000 na garin rogo, masara, gero da dawa a fadin kasar.

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta raba wa talakan Najeriya garin rogo da sauran kayan abinci

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta raba wa talakan Najeriya garin rogo da sauran kayan abinci
Source: Facebook

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sakin kayayyakin abinci har tan 70,000 ga marasa karfi a Najeriya.

Hakan na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na saukaka wa mutane illar da dokar hana fita ya yi a wasu jihohin kasar, sakamakon annobar Coronavirus.

Nanono wanda ya mika kayan abincin ga ministar harkokin agaji, da hana annoba, Sadiya Farouq, ya ce hakan na daidai da amincewar shugaba Buhari.

Ministan ya ce duk wanda ya san kan garin rogo toh ya san abunda suka bayar mai inganci ne sosai.

Ministar harkokin agaji, Sadiya wacce ta karbi kayayyakin a madadin ma’aikatar, ta bayar da tabbacin cewa kayayyakin zai isa ga wadanda ya kamata a jihohin da abun ya shafa bisa ga tsarin rabon wanda ke kasa.

KU KARANTA KUMA: Majalisa ta tsawaita hutunta domin bin dokar hana zirga-zirga

Dr Suleiman Haruna, daraktan abinci da tsare-tsare a ma’aikatar gona da ci gaban kakkara ya bayar da tabbacin cewa kayayyakin abincin da aka saki na da inganci.

A wani rahoton kuma mun ji cewa mazauna unguwar Narati a garin Kaduna sun yi wawason kayan abincin da aka ajiye da niyyar raba wa marasa karfi a unguwa a suka bar yan kwamitin da aka daura wa alhakin rabon kayan abincin sun kallonsu babu yadda za su yi da su.

Kamfanin Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ne ta bayar da kayayyakin abincin domin a raba wa talakawa yayin da suke zaune a gidajensu sakamakon dokar hana fita da aka saka saboda coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel