Tinubu na Dab da Sakawa Shehu Sani, Omokri da wasu 'Yan Adawa da Mukamai

Tinubu na Dab da Sakawa Shehu Sani, Omokri da wasu 'Yan Adawa da Mukamai

  • Gwamnatin Tarayya ta fara tantance wasu 'yan siyasa domin cike mukaman jakadanci da manyan ofisoshin jakadu 22 a kasashen waje
  • Rahotanni sun bayyana cewa tsofaffin gwamnonin PDP, Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu, sun shiga cikin jerin wadanda ake tantancewa
  • Tsohon Sanata Shehu Sani, Reno Omokri, da Femi Fani-Kayode na daga cikin wadanda aka tantance a shirin tura su aiki kasashen waje
  • Bayan tunbuke dukkannin jakadun Najeriya a shekarar 2023, gwamnatin Tinubu ta nanata cewa ana kokarin samar da sababbin jakadu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fara tantance wasu 'yan siyasa a kokarinta na cike ofisoshin jakadanci 76 da manyan ofisoshin jakadu 22 da Najeriya ke da su a kasashen waje.

Kara karanta wannan

'Ana kulla wa Ribas makirci,' Kwamishinan Fubara ya hango sabuwar matsala

An bukaci wadanda aka zaba da su je ofisoshin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) mafi kusa da su domin tantancewar tsaro.

Tinubu
Gwamnati ta fara tantance wadanda za a nada jakadun Najeriya Hoto: Shehu Sani/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Eno Omokri
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard News ta ruwaito cewa tuni aka tuntubi wasu daga cikin wadanda aka zaba domin su gabatar da tarihin karatu da kuma ayyukan da suka taba yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya mai tushe ya tabbatar da cewa tsoffin gwamnonin Kudu maso Gabas guda biyu – Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu sun shiga cikin jerin wadanda aka fara tantancewa.

Shehu Sani zai samu mukami a gwamnati?

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa tsohon Sanata Shehu Sani, wanda kwanan nan ya koma APC, da kuma tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, na daga cikin wadanda aka tantance.

Majiyar ta kuma tabbatar da cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas, Femi Pedro, da tsohon Ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, suma sun wuce matakin tantancewa.

Rahotanni sun nuna cewa dukkaninsu an tabbatar da sahihancinsu kuma an shirya tura su zuwa aikace-aikacen gwamnati a matakin kasa.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan abubuwa 4 da suka girgiza jama'a a makonni 2

Gwamnatin Tinubu za ta yi sabbabbin nade-nade

A watan Satumba na shekarar 2023, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta tunbuke dukkannin jakadun Najeriya saboda dalilai daban-daban.

Kusan shekaru biyu bayan rushe, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa za a bayyana sababbin jakadu nan ba da jimawa ba.

A yanzu haka, ana tantance bayanan wadanda aka zaba, tare da raba bayanansu zuwa ga hukumomin da suka dace a cikin fadar shugaban kasa da kuma majalisar dokoki.

Tinubu
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya alakanta jinkirin da aka samu wajen nadin jakadu da rashin isassun kudi.

Jinkirin nada jakadin ya jawo kasashen waje da masu ruwa da tsaki da dama sun fara nuna damuwa kan gibin da ake da shi a shugabancin diflomasiyyar Najeriya.

Tinubu: 'Za a nada sababbin jakadu'

A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin Najeriya ta fara tantance mutanen da za su jagoranci ofisoshin jakadancin kasar fiye da 100 a ofisoshin Najeriya da ke kasashen waje.

Kara karanta wannan

An shiga firgici da ƴan bindiga suka sace hadimar gwamna, sun bukaci N30m

Wannan mataki na fara tantancewa yana zuwa ne bayan jinkiri da aka samu a nadin sababbin jakadun kasar, wanda wasu masu ruwa da tsaki ke ganin zai kawo cikas ga diflomasiyya.

Wasu rahotanni sun kara bayyana cewa gwamnati ta samu kalaman wasu daga cikin 'yan kasashen waje kan rashin wakilcinsu, kuma za a tabbatar da an dauki mataki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng