Kano: Manyan Abubuwa 4 da Suka Girgiza Jama'a a Makonni 2

Kano: Manyan Abubuwa 4 da Suka Girgiza Jama'a a Makonni 2

Daga kusan karshen watan Maris na shekarar 2025, Kanawa sun shika zullumi, alhini da fargaba a kan wasu manyan abubuwa da suka shafi jihar Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kisan wasu mafarauta ’yan asalin karamar hukumar Bunkure da wasu kananan hukumomi da ’yan bijilanti suka jagoranta a Uromi ya fi komai tayar da hankalin jama’a.

Fahd Muhammad
Kisan Hausa a Uromi ya girgiza jama'a Hoto: Abba Kabir Yusuf/Fahd Muhammad
Asali: Facebook

Legit Hausa ta waiwayi manyan abubuwan da suka tayar da hankali a jihar Kano cikin makonni biyu da suka wuce, da irin halin da ake ciki a yanzu.

1. Babbake 'yan asalin Kano a garin Uromi

A ranar 28 ga Maris, 2025, wani mummunan lamari ya girgiza al’ummar Kano da sauran Arewacin Najeriya, bayan bayyanar bidiyon kisan wasu Hausawa a jihar Edo.

Kara karanta wannan

'Ba zan yi sata ba': Ɗan majalisa ya cire tsoro a gaban ƴan mazabarsa bayan shan suka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa cewa, wasu da ba su da tausayi a Uromi, jihar Edo, suka kai wa matafiyan hari.

Rahotanni sun nuna cewa waɗanda aka kashe mafarauta ne kuma su ne ginshikin ciyar da iyalansu. Sun bar iyaye, mata da ƙananan yara cikin kunci da dimuwa.

Kabir
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sunusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Gwamnatocin Kano, Edo da Tarayya sun ce ba za su lamunci wannan aika-aika ba, kuma za a hukunta wadanda ke da hannu a kisan.

A ɓangaren tallafi, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya fara ba iyalan mamatan tallafin kuɗi.

A wata hira da Legit, shugaban ma’aikatan Sanata Barau, Farfesa Muhammad Ibn Abdallah, wanda ya jagoranci rabon Naira miliyan 16 ga iyalan mamatan, ya ce:

“Lallai wannan tallafi ya kasance wata ni’ima mai haɗe da baƙin ciki ga waɗanda suka amfana – domin suna cikin lokacin makoki na rasa masu ciyar da su, da aka hallaka kuma aka ƙone da ransu.”

Kara karanta wannan

Uromi: Barau ya yi alkawari bayan ziyarar iyalan Hausawan da aka kashe a Edo

Farfesa Ibn Abdallah ya ƙara da cewa sun tarar da iyaye da yara cikin mawuyacin hali, yayin da iyayen ke zubar da hawaye na baƙin ciki mara misaltuwa.

2. Rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Kano ta yi babban rashi bayan rasuwar ɗaya daga cikin dattawan masarautar Kano, Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, yana da shekaru 92.

Rasuwar tasa ta girgiza al’ummar Kano, har ta haɗa kawunan ’yan siyasa da ke adawa da juna, inda aka gan su tare a wurin jana’izar.

Idan za a iya tunawa, jam’iyyar APC ta Kano da gwamnatin Abba Kabir Yusuf sun yi ta takaddama bayan mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarki.

Amma yayin jana’izar Galadiman, an ga Gwamna Abba Kabir Yusuf ya halarta, kuma ya gaishe da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, cikin girmama wa.

3. Sarkin Kano ya yi 'hawan Sallah'

Kara karanta wannan

Uromi: An jibge jami'an tsaro a garin da aka hallaka Hausawa 16 a Edo

A cikin wani sabon salo da ya jawo ce-ce-ku-ce, Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci tawagarsa zuwa gidan gwamnati a lokacin hawan Nasarawa – amma ba tare da hawa doki ba.

A al’ada, Sarki da hakimai na fitowa a kan dawaki a lokacin hawan Sallah, cikin ado da al’adu masu kayatarwa.

Sai dai kamar yadda aka gani a shekarar bara, a wannan shekarar ma, rundunar ’yan sandan Kano ta haramta gudanar da hawan saboda abin da ta kira “barazanar tsaro”.

A ranar Idi, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ya hau doki don koma wa fadarsa da ke kofar Kudu, kuma a hanya ne wasu 'yan daba suka kai masa farmaki har aka kashe mutum guda.

4. 'Yan sanda sun gayyaci Sarkin Kano

Jami’an ’yan sandan Najeriya sun gayyaci Sarki Muhammadu Sanusi II domin yi masa tambayoyi kan fitowarsa yayin hawan Nasarawa ba tare da izini ba.

Wannan gayyata ta haifar da fushi da ce-ce-ku-ce a Kano, inda jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu mazauna na ganin gayyatar na iya janyo rikici da ƙarin tabarbarewar doka.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 4 na bibiyar hakkin Hausawan da aka kashe a jihar Edo," HRN

Sai dai a cikin awa 24 kacal, rundunar ’yan sandan ta janye gayyatar, tana mai cewa za ta aike jami’anta Kano domin su karɓi bayanan daga wajen Sarkin.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce:

“An janye gayyatar Sarki ne domin guje wa yuwuwar rikici da kare zaman lafiya a jihar, bayan tuntubar shugabanni da dattawan ƙasa.”

Tsohon Sanata ya shawarci masarautar Kano

A baya, mun wallafa cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana damuwarsa game da yadda lamarin masarauta wanda ke kara tsanani, inda ya bukaci sarakan da su warware matsalolinsu.

Tsohon Sanatan na Kaduna ya shawarci Sarki Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado, cewa su sasanta tsakaninsu da juna, su daina amfani da kotu ko ‘yan sanda wajen warware matsalolin.

Sanata Shehu Sani ya kara da cewa babban birni kamar Kano da ke da tarihi mai daraja da al’adu bai kamata rikici ya bata masa suna ko ya tozarta shi ba, saboda haka a yi sulhu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng