'Mene Amfanin Kwamishinan Ƴan Sandan Kano?' An Soki Gayyatar Sanusi II zuwa Abuja

'Mene Amfanin Kwamishinan Ƴan Sandan Kano?' An Soki Gayyatar Sanusi II zuwa Abuja

  • Fitaccen dan kasuwa, Atedo Peterside ya soki yadda hedkwatar 'yan sanda ta gayyaci Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, don bincike kan kashe-kashen Sallah
  • Atedo Peterside yace ya kamata ofishin 'yan sandan Kano su binciki Sanusi maimakon tilasta masa zuwa hedkwatar Abuja
  • Ya kara da cewa gayyatar da ta shafi tashi daga jiha zuwa wata na nuna tsangwama ne kuma bai dace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Atedo Peterside, wanda ya kafa bankin Stanbic IBTC ya yi magana bayan ƴan sanda gayyatar Sarki Sanusi II.

Babban ɗan kasuwar ya soki gayyatar Sarkin Kano wanda hedkwatar 'yan sanda ta yi adaga Abuja.

An soki matakin gayyatar Sanusi II a Abuja
Dan kasuwa ya soki yan sanda kan gayyatar Sarki Sanusi II zuwa Abuja. Hoto: Sanusi II Dynasty, Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Peterside ya bayyana haka ne a yau Lahadi 6 ga watan Afrilun 2025 a shafinsa na X inda ya ke sukar matakin.

Kara karanta wannan

Abin da mazauna Kano ke cewa da 'yan sanda suka gayyaci Sanusi II zuwa Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gayyatar Sanusi II zuwa Abuja

An gayyaci Sanusi ne saboda zargin hannu a kashe wasu a lokacin bikin Salla karama da aka yi kwanan nan a Kano.

A wata takarda da aka rubuta ranar 4 ga Afrilu, 'yan sanda suka umurci Sanusi da ya bayyana a Abuja ranar 8 ga Afrilu.

A lokacin Sallah, wasu daga cikin masu gadin Sanusi da ke cikin tawagarsa an ce an kai musu hari kuma an kashe su.

Sanusi ne ya jagoranci sallar Idi a filin salla na Kofar Mata da ke Kano tare da Gwamna Abba Yusuf da wasu jami'ai.

Rundunar 'yan sandan Kano ta kafa kwamitin mutum takwas domin gudanar da bincike kan kisan da ya faru lokacin bikin Sallah.

Kakakin 'yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne duk da haramta gudanar da bikin durbar a jihar.

An soki yan sanda kan gayyatar Sanusi II da aka yi
Dan kasuwa ya bayyana damuwa kan gayyatar Sarki Sanusi II da yan sanda suka yi. Hoto: @AtedoPeterside.
Asali: UGC

Sanusi II: Ɗan kasuwa ya soki ƴan sanda

Kara karanta wannan

Bayan rasa rai a bikin sallah, ƴan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi II zuwa Abuja

A rubutunsa a X, Atedo Peterside ya tambayi dalilin tilasta wa Sanusi II tafiya Abuja maimakon a bincikeshi a Kano kawai.

Ya ce abin mamaki ne idan kwamishinan 'yan sanda ba zai iya tambayar Sanusi a Kano ba, sai a tursasa masa tafiya.

Peterside ya kara da cewa irin wannan gayyata daga wata jiha zuwa wata hanya ce ta gallaza wa mutum, kuma bai dace ba.

A cikin sanarwar, Peterside ya ce:

"Me rundunar yan sanda ke ƙoƙarin mayar da Najeriya? Shin Najeriya ta zama ƙasar ‘yan sanda ne yanzu? Wace irin tambaya ce da Kwamishinan ‘Yan Sanda ba zai iya yi wa Sarkin Kano a Kano ba da wakilcin ubanninsa na Abuja ba?.
"A tura goron gayyata daga Abuja zuwa wata jiha, irin wannan mataki nau’i ne na ‘cin zarafi’ kuma ya kamata a daina irin wannan a ƙarni na 21."

Yan Kano sun soki gayyatar Sanusi II

Kara karanta wannan

'Mu na zaman makoki, su na hawan Sallah,' Sarki Sanusi ya fusata wasu

Kun ji cewa an ce Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zai gana da Sufeto Janar na ‘yan sanda a Abuja ranar Talata.

Hakan ya biyo bayan gayyatar Sanusi ne kan wani al’amari da ya faru a lokacin bukukuwan Sallah a Kano.

Wasu mazauna Kano sun soki wannan gayyata, suna cewa yana da nufin tayar da rikici a jihar da neman tuge Sarkin daga sarauta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng