Tsohon Shugaban Majalisa Ya Dura kan Tinubu da Shettima Saboda Ficewa Najeriya

Tsohon Shugaban Majalisa Ya Dura kan Tinubu da Shettima Saboda Ficewa Najeriya

  • Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Adolphus Wabara, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima
  • Sanata Adolphus Wabara ya caccaki mutanen biyu ne saboda ficewa Najeriya zuwa ƙasashen waje a lokaci guda
  • Ya bayyana cewa barin Najeriya da suka yi babu shugaba, sakaci ne babba da kuma raina hankalin mutanen da suke mulka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Adolphus Wabara, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima kan tafiya zuwa ƙasashen waje.

Adolphus Wabara ya bayyana mamaki da ɓacin ransa kan tafiyar da suka yi a lokaci guda, inda ya bayyana hakan a matsayin babban matakin raini da rashin mutunta tsarin mulki.

Wabara ya caccaki Tinubu da Shettima
Adolphus Wabara ya caccaki Tinubu da Shettima Hoto: @DOlusegun, @KashimShettima
Asali: Facebook

Ficewar Tinubu da Shettima ta jawo magana

Jaridar Vanguard ta ce tsohon shugaban majalisar dattawan ya zargi Shugaba Tinubu da mataimakinsa da barin Najeriya ba tare da shugabanci ba.

Kara karanta wannan

'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana wannan lamarin a matsayin tsananin sakaci da aiki da kuma rashin girmama ƴan Najeriya.

Idan ba a manta ba yayin da Tinubu ya tafi ƙasar Faransa domin wani ziyarar aiki na makonni biyu, Shettima ya tafi Dakar, ƙasar Senegal, inda ya wakilci Shugaban Kasa a bikin cika shekaru 65 da samun ƴancin kai na ƙasar a ranar 4 ga Afrilu

Adolphus Wabara ya caccaki Tinubu, Shettima

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa duk da shugaban ƙasa na da ƴancin yin tafiya zuwa ƙasashen waje idan ya zama dole, ya kamata ya miƙa mulki ga mataimakinsa a matsayin muƙaddashin shugaba.

Saboda haka, ya jaddada cewa sam bai dace ba a ce mataimakin shugaban ƙasa wanda yakamata ya zama muƙaddashin Shugaba, shima ya fice daga ƙasar alhali shugaban ƙasa baya nan.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ya ƙara da cewa idan har dole ne a wakilci Najeriya a Senegal, yakamata a miƙa aikin ga jami’in gwamnati da ya dace, a wannan yanayin ministan harkokin waje, maimakon barin ƙasar babu shugaba.

Kara karanta wannan

APC ta yi bayani kan shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Sanata Wabara, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce abin yana da matuƙar ban mamaki ganin yadda shugaban ƙasa da mataimakinsa suka bar aiki suka tafi ƙasashen waje a lokaci guda.

Wabara ya nuna ce ba wannan ba ne karon farko da Tinubu da mataimakinsa ke fita daga ƙasar nan a lokaci guda ba.

Wabara ya caccaki Shettima da Tinubu
Adolphus Wabara ya caccaki Tinubu da Kashim Shettima Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Ya ce hakan na nuni da irin rainin da ake yi wa ƴan ƙasa waɗanda suka zaɓe su domin su riƙe muƙaman da suka ke da matuƙar muhimmanci.

Ya ce barin ƙasar a irin wannan lokaci da ake da muhimman matsalolin da ke bukatar kulawar shugaban ƙasa da mataimakinsa abu ne da bai dace ba, kuma tozarci ne ga Najeriya da kuma ofisoshin da suke riƙe da su.

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya shawarci Shugaba Tinubu da mataimakinsa da su daina wasa da makomar ƴan Najeriya kuma su mayar da hankali kan shugabanci.

Kara karanta wannan

An bar kasa ba kowa: Shettima ya shilla kasar waje bayan Tinubu ya kwana a Faransa

Tinubu ya fusata kan kashe-kashe a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna takaicinsa kan kashe-kashen da ƴan bindiga suka yi a Plateau.

Shugaba Tinubu ya jajantawa Gwamna Caleb Mutfwang kan ta'addancin da ƴan bindigan suka yi wa bayin Allah.

Ya umarci jami'an tsaro da su tabbatar da cewa sun zaƙulo waɗanda suka aikata ɗanyen aikin domin su fuskanci hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng