‘Allah Maka Albarka’: Bidiyon Marigayi Albany na Zuba Addu’o’i ga Dutsen Tanshi
- Marigayi Sheikh Muhammad Albany ya yabawa gwagwarmayar Malam Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi a yaki da Boko Haram
- A cikin wani tsohon bidiyon yabon da aka wallafa a Facebook ranar 4 ga Afrilu 2025, Albany ya jinjinawa marigayin
- Albany ya ce babu wanda ya kalubalanci tsohon shugaban Boka Haram, Muhammad Yusuf kamar Idris Abdul’aziz
- Ya bayyana yadda Idris ya caccaki Muhammad Yusuf har ya bayyana rashin hujjarsa tare da neman da ya tuba ya bi hanya mai kyau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zaria, Kaduna - Marigayi Sheikh Muhammad Adam Albany Zaria ya yabawa jajircewar Malam Idris Dutsen Tanshi a wani tsohon bidiyo.
Marigayin ya yi magana kan irin gwagwarmayar da Idris Abdul'aziz ya yi musamman wurin yaki da Boka Haram.

Asali: Facebook
Bidiyon marigayi Albany na addu'a ga Dutsen Tanshi

Kara karanta wannan
'Abin da Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya faɗa kafin rasuwarsa': Ɗalibinsa ya magantu
Hakan na cikin wani tsohon faifan bidiyo ne da Ibrahim Yusuf Muhd Sambo ya wallafa a safin Facebook a ranar Juma'a 4 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, marigayin ya yaba da yadda Malam idris ya ke kalubalantar shugaban Boka Haram, Muhammad Yusuf a wancan lokaci.
Sheikh Albany ya ce babu wanda ya yi abin da ya dace ga Muhammad Yusuf kamar marigayi Idris Dutsen Tanshi.
Marigayin ya ce a bidiyon:
"Idris Abdul'aziz na Bauchi Allah ya yi maka albarka, duk wadanda suka zauna suka kalubalanci Muhammad Yusuf kaf babu wanda ya yi wa Muhammad Yusuf abin da ya dace sai Idris Abdul'aziz.
"Shi ne idan aka buga idan magana ta yi magana sai a tashi a ci kwalar juna, eh to tun da karatu ya ki za ku yi rashin kunya.
"To sannan sai a zauna, sai a sake bude karatu, baya sake wa a bar 'mishiwari' daya, kwaya daya, sai ya ce a tsaya."

Kara karanta wannan
'A tsaye aka karɓi ta'aziyya ta': Sheikh ya fadi dattakun ɗaliban Malam Dutsen Tanshi

Asali: Facebook
Marigayi Albany ya yabi Dutsen Tanshi a bidiyo
A bidiyon, Albany ya ce Malam idris daga karshe ya kan tabbatar Muhammad Yusuf ba shi da hujja kawai bankaura yake yi tare da bukatar ya tuba.
Ya kara da cewa:
"Sai ya ce yanzu dai ka tabbatar kai batacce ne ba ka da hujja? to kai batacce ne ya rage naka ko ka tuba ko ka da ka tuba amma ba ka da hujja, ku kun ji ba shi da hujja."
Bidiyon Dutsen Tanshi yana magantu kan Albany
Mun ba ku labarin cewa a wani tsohon bidiyo, marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya koka kan halin da al'umma ke nunawa ga malamai tun suna raye.
Malamin ya ce wasu malamai sun rika sukar Sheikh Muhammad Adam Albany Zaria lokacin yana raye, amma suka zo jikinsa bayan ya mutu.
Marigayin a bidiyon ya bayyana cewa malaman sun ce Albany bai bar kowa ba har da Ahlus Sunnah, amma daga baya suka fara yaba shi bayan rasuwarsa.
A bidiyon, marigayin ya ce shi ba ya tsammanin za su zo jikinsa ko bayan ya mutu, yana nuna takaicinsa kan irin halin mutane.
Asali: Legit.ng