Yan Najeriya Za Su Siya Fetur da Araha bayan Faduwar Farashin Gangar Mai

Yan Najeriya Za Su Siya Fetur da Araha bayan Faduwar Farashin Gangar Mai

  • Farashin danyen mai a duniya ya yi mugun faduwa zuwa $65 a kowace ganga daga $69.90
  • Man fetur zai iya sauka a Najeriya saboda hauhawar samar da danyen mai a duniya a halin yanzu
  • Farashin lita a wasu manyan wuraren ajiya ya sauka daga N920 zuwa N897 da N912 saboda yanayn kasuwa
  • Masu sayar da fetur na sa ran saukar farashi zai rage kudin sufuri da kayan masarufi da yanzu suka yi tsada

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Akwai alamun cewa farashin man fetur zai sauka a Najeriya, biyo bayan faduwar farashin danyen man Brent a kasuwar duniya zuwa $65 a ganga.

Ana amfani da danyen man Brent a duniya wajen daidaita farashin fetur, ciki har da sauran kayayyakin man fetur.

Farashin fetur ka iya faduwa a Najeriya
Yan Najeriya za su caba yayin da ake hasashen faduwar farashin fetur. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Musabbabin hasashen faduwar farashin mai

Kara karanta wannan

An yi albishir da saukar kudin sufuri da kayayyaki bayan karyewar farashin mai

Rahoton Vanguard ya bayyana cewa hakan ya biyo bayan sanarwar shugaban Amurka, Donald Trump, na sabon haraji da zai shafi tattalin arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya kara da cewa kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, OPEC+, ta yanke shawarar kara samar da ganga 410,000 a kullum daga watan Mayun 2025.

Wasu wuraren ajiya irin su Mainland, A.Y.M, da Ever sun rage farashin lita daga N920 zuwa N918 da N919 kowanne.

Haka kuma wuraren ajiya irin su Prudent, Eterna da Soroman sun rage farashin fetur daga N913 zuwa N912 da N897 da N915 kowanne.

Majiyoyi sun bayyana cewa masu sayar da fetur za su rage farashin man idan wannan yanayi na kasuwa ya ci gaba.

An yi hasashen faduwar farashin fetur a Najeriya
Akwai alamun man fetur zai rage farashi bayan faduwar kudin gangan mai a duniya. Hoto: Contributor.
Asali: Getty Images

Dillalan mai sun fadi alherin haka ga Najeriya

Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya ce tabbas hakan zai taimaka wurin rage kudin sufuri a Najeriya.

Ya ce:

"Muna sa ran rage farashin zai taimaka wajen saukaka kudin sufuri, kayan masarufi da sauran ayyuka."

Kara karanta wannan

'Inyamurai sun rufe shaguna': Halin da ake ciki a Sokoto kan kisan Hausawa a Edo

Kungiyar OPEC+ ta hadu a ranar 3 ga Afrilun 2025 don duba yanayin kasuwar danyen mai da kuma makomar farashinsa.

Kungiyar ta bayyana cewa za ta kara samar da ganga 411,000 a kullum daga Mayun 2025, kamar yadda suka amince a Disambar 2024.

Sun bayyana cewa wannan karin samar da mai zai iya dakatar ko sauyawa idan yanayin kasuwa ya sauya ko bukatar hakan ta taso.

Kungiyar OPEC+ ta kara da cewa wannan matakin zai ba kasashe damar biyan bashin mai da suka samar fiye da yadda aka amince.

Kungiyar ta tabbatar da cewa za su cike gibin mai da suka samar tun Janairun 2024 zuwa yanzu ta hanyar sabunta shirin biyan bashin.

Ta ce za ta gabatar da sabbin tsare-tsaren biyan bashin mai ga sakatariyar OPEC kafin 15 ga Afrilu 2025 kamar yadda aka bukata.

NNPCL ta kara kudin mai a Najeriya

Kun ji cewa Kamfanin NNPCL ya ƙara farashin fetur zuwa N925 a Lagos da kuma N950 a Abuja daga ranar 2 ga Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa farashin abinci ya kara yin kasa warwas a yankunan Arewa

Karin farashin na zuwa ne bayan dakatar da sayar da danyen mai a Naira da NNPCL ya yi a matatar Dangote.

An samu karin kudin ne sa'o'i bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke shugaban NNPCL, Mele Kyari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.