Bayan Rasa Rai a Bikin Sallah, Ƴan Sanda Sun Gayyaci Sarki Sanusi II zuwa Abuja

Bayan Rasa Rai a Bikin Sallah, Ƴan Sanda Sun Gayyaci Sarki Sanusi II zuwa Abuja

  • Rundunar ‘yan sanda ta gayyaci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, zuwa Abuja saboda rikicin da ya faru yayin bikin Sallah
  • Rikicin ya faru ne lokacin da Sarkin ke dawowa daga filin Sallah zuwa fada, inda wani dan sa-kai Surajo Rabiu ya bakunci barzahu
  • CP Olajide Rufus Ibitoye ne ya aika wa Sarkin takardar gayyata a madadin DIG na sashen bincike na hedkwatar ‘yan sanda a Abuja
  • An bukaci Sarkin ya bayyana gaban sashen bincike na ‘yan sanda a Abuja, ranar Talata 8 ga Afrilun 2025, da karfe 10:00 na safe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) ta gayyaci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ofishinta a Abuja.

Rundunar ya gayyaci basaraken ne domin amsa tambayoyi kan rikicin bikin Sallah da ya faru a jihar Kano.

Kara karanta wannan

An tafi da limamin da ya yi batanci ga Dr Dutsen Tanshi bayan an so masa duka

Yan sanda sun gayyaci Sanusi II saboda bikin sallah
Sarki Sanusi II zai amsa tambayoyi bayan gayyatar rundunar yan sanda. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Twitter

An rasa rai yayin bikin sallah a Kano

Rahoton Leadership ya bayyana cewa gayyatar ta biyo bayan rikicin da ya faru a ranar Sallah, lokacin da tawagar Sarkin ke komawa daga filin Sallah zuwa fada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani dan sa-kai mai suna Surajo Rabiu ya rasa ransa a rikicin, yayin da wani mutum daya kuma ya jikkata, wanda hakan ya bata farin cikin bikin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun tashin hankali a Kano, bayan haramta gudanar da bikin sallah na bana saboda matsalar tsaro.

Sai dai duk da hana hawan, tawagar motocin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ta ci gaba da gudanar da zagayen Sallah a rana ta uku.

Kwamishinan ‘yan sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kafa kwamitin mutane takwas domin gudanar da bincike na musamman kan rikicin da ya faru.

Musabbabin gayyatar Sarki Sanusi II zuwa Abuja

Takardar gayyata, wadda aka rubuta ranar 4 ga Afrilun 2025, na dauke da sa hannun CP Olajide Rufus Ibitoye a madadin DIG na Abuja, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kyawun alkawari: Barau ya raba miliyoyi ga iyalan Hausawan da aka kashe a Edo

Takardar ta bayyana cewa:

“An ba ni umarni daga IGP, ta hannun DIG, Sashen Bincike, na gayyace ka zuwa ganawa domin bincike kan rikicin da ya faru lokacin Sallah.”
Yan sanda sun dauki mataki kan Sanusi II game da bikin sallah
Bayan rasa rai yayin bikin sallah, yan sanda sun gayyaci Sanusi II domin amsa tambayoyi. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Facebook

Yaushe ake bukatar Sanusi II ya bayyana?

An bukaci Sarkin ya bayyana gaban Sashen Bincike na Abuja, dake gaban Hedkwatar ‘Yan Sanda, Area 11, Abuja, da karfe 10:00 na safe, ranar Talata 8.

A lokacin hada wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa daga fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, dangane da gayyatar da ‘yan sanda suka aikowa ba.

Sarki Sanusi II ya yabawa gwamna Abba

A baya, kun ji cewa Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ayyukan ci gaba da yake zuba wa a jihar.

Sarki Sanusi II ya ce ƙoƙarin da gwamnan ke yi na inganta harkokin ilimi, kiwon lafiya noma da tsaro a jihar Kano ya cancanci a jinjina masa.

Gwamna Abba Kabir ya jaddada godiya ga mai martaba sarkin bisa jagorancin da yake yi da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng