‘Ba Mu San Shi ba’: ’Yan Sanda Sun Kama 'Ɗan Sanda' da Ya ce Zai Kashe ’Yan Kudu a Arewa

‘Ba Mu San Shi ba’: ’Yan Sanda Sun Kama 'Ɗan Sanda' da Ya ce Zai Kashe ’Yan Kudu a Arewa

  • Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta nesanta kanta daga wani mutumi Hadaina Hussaini da ake zargi da yin barazana a Facebook
  • Hussaini ya sanya kayan ‘yan sanda yana kuma barazanar maida martani kan kashe ‘yan Arewa 16 da aka yi a wani gari a Edo
  • Rundunar ta bayyana cewa an sallami Hussaini daga aikin ‘yan sanda na musamman shekaru biyu da suka wuce
  • An kama Hadaina Hussaini kuma za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa Hadaina Hussaini da ake kira Dan-taki ba dan sanda ba ne, kamar yadda ya bayyana a Facebook.

Hussaini ya sanya kayan ‘yan sanda yana kuma fadin kalaman da ka iya tayar da rigima inda ya yi barazanar ramuwar gayya kan kashe ‘yan Arewa a Edo.

Kara karanta wannan

Kamar a Jahiliyya: An tono gawa bayan mahaifi ya kashe, ya birne 'yarsa a Najeriya

Yan sanda sun nesanta kansu da matashn da ya yi barazanar kisan yan Kudu a Arewa
Yan sanda a Kaduna sun kama tsohon jami'insu kan barazanar kisan yan Kudu. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda, DSP Mansir Hassan, ya fitar wanda kakakin rundunar a Abuja, Adejobi Olumuyiwa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edo: 'Dan sanda' ya jefa kansa a matsala

Hakan ya biyo bayan furucin wani da aka ce dan sanda ne a Kaduna da ya yi barazanar daukar mataki kan ‘yan Kudu da ke Arewa bayan kashe ‘yan yankin 16 a Uromi da ke Edo.

Hadaina Hussaini Dan-Taki ya ce dole ne su dauki mataki cikin mako guda, inda ya ke cewa ‘yan Kudu suna zaune a Arewa ba tare da matsala ba.

An ce bayan suka kan furucinsa, Dan-Taki ya canza sunansa a Facebook kuma ya takaita damar ganin wallafarsa don gujewa karin matsala.

Yan sanda sun kama jami'in bogi kan barazanar kisan yan Edo
Yan sanda sun nesanta kansu da matashin da ya ce za su hallaka yan Kudu a Arewa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Martanini 'yan sanda kan barazanar Hadaina

Sanarwar yan sanda ta bayyana cewa an sallami Hussaini daga aikin dan sanda na musamman shekaru biyu da suka wuce.

Kara karanta wannan

An hukunta tsohon kwamishinan ƴan sandan Kano kan sukar matakin Tinubu a Rivers

Sanarwar ta kara da cewa:

"An kama wanda ake zargin kuma za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike bisa doka da oda."

Hussaini ya taba aiki a rundunar da ke Kaduna, amma an sallame shi saboda halayen sa da ba su dace ba.

Hassan ya kara da cewa hoton Hussaini da ke yawo yana sanye da kayan dan sanda tsohon hoto ne tun kafin a sallame shi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Mutane su rika duba katin shaidan aiki na ainihin dan sanda domin tabbatar da sahihancinsa kafin su amince.
"Rundunar ‘yan sanda ba za ta lamunci duk wani kalami ko barazana da zai haddasa tashin hankali ba."

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, CP Rabi’u Muhammad, ya bukaci jama’a su ci gaba da kwantar da hankalinsu su kuma kai rahoton duk abin da ke tayar da hankali.

Legit Hausa ta tattauna da ɗan gwagwarmaya

Kara karanta wannan

An kutsa gidan dan agajin Izala a Abuja, an sassara shi da makami har lahira

Wani shugaban kungiyar matasa ya ce abin takaici ne yadda mutane ke furta kalamai kara zube kam lamarin da ya faru.

Kwamred Mohammed Ali ya ce dole komai a jira doka ta yi aiki tun da an cafke wasu da ake zargi da kisan.

"Yawan maganganu zai iya kawo rigima tare da asarar rayuka da ba su ji ba kuma ba su gani ba.
"Ya kamata a bar hukumomi su yi abin da ya dace kafin daukar matakin gaba."

- Cewar Kwamred Ali

Abokan mafarauta sun sha alwashin daukar fansa

Kun ji cewa yan uwa da abokan aikin mafarautan da aka kashe sun yi gargaɗin ɗaukar fansa idan har ba a cafke waɗanda suka yi ɗanyen aikin ba.

Sun nuna cewa sun san hanyoyin da za su bi su je har Uromi domin zaƙulo waɗanda ke da hannu a mummunan kisan gillar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng