An Shiga Firgici da Ƴan Bindiga Suka Sace Hadimar Gwamna, Sun Bukaci N30m

An Shiga Firgici da Ƴan Bindiga Suka Sace Hadimar Gwamna, Sun Bukaci N30m

  • Wasu 'yan bindiga sun sace Blessing Adagba, mai taimakawa Gwamnan Ebonyi, a unguwar Okposhi Eheku a karamar hukumar Ohaukwu
  • Blessing Adagba ta kasance shugabar cibiyar ci gaba ta Ngbo ta Tsakiya kafin sace ta da safe a ranar Alhamis 3 ga watan Afrilun 2025
  • Rundunar ‘yan sanda ta jihar ta tabbatar da sacewar, tare da bayyana cewa jami'an yaki da garkuwa da mutane sun fara aikin ceto
  • Masu garkuwar suna bukatar N30m a matsayin kudin fansa domin sako Adagba, kamar yadda bincike ya nuna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Wasu ‘yan bindiga sun sace mai taimakawa Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, mai suna Blessing Adagba, a cikin jihar a jiya Alhamis 3 ga watan Afrilun 2025.

Kafin a sace ta, Adagba ce shugabar cibiyar ci gaba ta Ngbo ta Tsakiya da ke karamar hukumar Ohaukwu ta jihar.

Kara karanta wannan

'A tabbatar da adalci duniya ta gani,' Abba Gida Gida kan kisan Uromi'

Yan bindiga sun sace hadimar Gwamna a Ebonyi
Wasu ƴan bindiga sun hadimar Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi. Hoto: Hon. Francis Nwifuru.
Asali: Facebook

Ebonyi: Gwamna ya sallami hadimansa 2

Jaridar Punch ta tuna cewa tsohon gwamna Sam Egwu ne ya kirkiro cibiyoyin ci gaba a kananan hukumomi domin tallafa wa talakawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya dakatar da wasu hadimansa na musamman kan zarge-zarge.

Gwamna Nwifuru ya yi suna wajen rashin daukar aiki da wasa, ya kori hadimansa guda biyu daga aiki bisa laifin rashin ladabi a bakin aiki.

Sakatariyar gwamnatin jihar Ebonyi, Farfesa Grace Umezurike ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 18 ga watan Maris 2025.

Gwamnan ya gargaɗi dukkan jami'an gwamnati cewa ba zai lamunci sakaci a bakin aiki ba ko saba dokoki da ƙa'idojin da aka shinfiɗa a gwamnatinsa ba.

An sace hadimar gwamna a Ebonyi
Rundunar yan sanda ta tabbatar da sace hadimar gwamna Francis Nwifuru a Ebonyi. Hoto: Francis Nwifuru.
Asali: Facebook

Yadda aka sace hadimar gwamna a Ebonyi

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, SP Joshua Ukandu, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Shugabannin musulmi sun tunkari Tinubu kan batun dakatar da Gwamna Fubara

A cewarsa, ‘yan bindigar sun sace Adagba da safiyar Alhamis a yankin Okposhi Eheku, karamar hukumar Ohaukwu.

Ya ce ‘yan sanda sun fara aiki kan lamarin domin ganin an ceto Adagba cikin gaggawa da lafiya inda rundunar ta bukaci al'umma su kwantar da hankalinsu.

Ya kara da cewa:

“Rundunar yaki da garkuwa ta riga ta fara aikin ceto. Ina da yakinin suna kokari wajen kubutar da ita.
“Eh, an sace Adagba a garin Okposhi Eheku da ke karamar hukumar Ohaukwu ta jihar."

Bincike ya nuna cewa masu garkuwar na neman N30m a matsayin kudin fansa kafin su sako ta wanda hakan ya tayar da hankulan al'ummar jihar.

Gwamna ya musanta cafke kwamishinoninsa a Ebonyi

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin jihar Ebonyi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Franics Nwifuru ta musanta wasu rahotanni da aka yaɗa a kanta.

Gwamnatin ta musanta cewa Gwamna Francis Nwifuru ya umarci a cafke wasu kwamishinoni guda biyar da ke aiki a ƙarƙashinsa.

Hakazalika, rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi ta bayyana cewa babu wani kwamishina da ta cafke da ke tsare a hannunta wanda ake zargin sun aikata ba daidai ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng