Gwamnoni 19 Sun Yi Maganar Rasuwar Babban Malami, Sheikh Idris Dutsen Tanshi
- A madadin gwamnonin jihohin Arewa 19, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Idris Abdul'Aziz Dutsen Tanshi
- Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa ya ce labarin rasuwar malamin ya girgiza shi domin rashi ne da ya shafi ɗaukacin al'ummar musulmi
- Gwamna Inuwa Yahaya ya roki Allah SWT ya gafarta wa Sheikh Idris Dutsen Tanshi, ya masa rahama, kuma Ya bai wa iyalansa haƙuri
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe - Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi alhinin rasuwar Sheikh Idris Abdul'Aziz Dutsen Tanshi.
Gwamna Inuwa ya miƙa sakon ta'aziyya bisa rasuwar fitaccen malamin addinin musulunci na Bauchi, wanda ya koma ga Allah a daren Juma'a.

Source: Facebook
Daily Trust ta tattaro cewa marigayin ya rasu a garin Bauchi bayan fama da jinya ta tsawon lokaci wanda ta kai ga dakatar da karatuttukansa.

Kara karanta wannan
"Mutane sun manta": Tinubu ya faɗi aikin da Sheikh Dutsen Tanshi ya yi wa Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi jana'izar babban malamin na sunnah da misalin karfe 10:00 na safiyar yau Juma'a, 4 ga watan Afrilu, 2025 a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas.
Gwamna ya yi alhinin rashin Dr. Dutsen Tanshi
Da yake ta'aziyyar rasuwar, Gwamna Inuwar Yahaya ya yi alhinin wannan rashi da muaulmi suka yi.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Gombe, Isma'ila Uba Misilli ya fitar da yammacin tau Juma'a.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce ya girgiza da ya samu labarin rasuwar malamin mara daɗi kuma abin takaici da jimami.
A cewarsa, Dr. Dutsen Tanshi malami ne mai ƙima kuma babban mai wa’azi, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaɗa ilimin addini da kuma tarbiyyar al’umma da kyawawan halaye.
Gwamnoni 19 sun yi ta'aziyyar Dutsen Tanshi
Gwamnan ya ƙara da cewa wannan rashi ba na iyalansa da mutanen jihar Bauchi kaɗai ba ne, rashi ne da ya taɓa duk wasu ɗaliban addini da ke amfana da ilimin marigayin.
“A madadin jama'a da gwamnatin jihar Gombe, da kuma gwamnonin jihohi 19 na Arewacin Najeriya, ina miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, gwamnatin Bauchi, da daukacin al’ummar Musulmi.”
- In ji Inuwa Yahaya.

Source: Facebook
Gwamna Inuwa Yahaya ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, Ya sanya shi cikin Aljannar Firdaus.
Shugaban gwamnonin Arewan ya kuma roƙi Allah SWT Ya bai wa iyalansa da masoyansa juriyar da za su iya jure wannan babban rashi.
Tinubu ya yi alhinin rasuwar Dutsen Tanshi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar shahararren malamin musuluncin nan, Sheikh Idris Abdul'Aziz Dutsen Tanshi.
Tinubu ya yabi marigayi Dutsen Tanshi bisa gudummuwar da ya bayar wajen yaki da tsattsauran ra'ayi na ƴan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas tun farko.
Shugaban ƙasa ya yi addu’a Allah ya jikansa, sannan ya roƙi iyalansa, almajiransa, da masoyansa su yi haƙuri da wannan rashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
