Ana Jimamin Rasuwar Dutsen Tanshi, An Sanar da Mutuwar Fitaccen Sarki a Kebbi

Ana Jimamin Rasuwar Dutsen Tanshi, An Sanar da Mutuwar Fitaccen Sarki a Kebbi

  • Dan majalisar wakilai, Hon. Ibrahim Mohammed ya nuna alhininsa kan rasuwar Sarkin Bunza, Dr. Mustapha Muhammad Bunza
  • Marigayin ya rayu da sadaukarwa ga al’umma, musamman a fannin ilimi, inda ya rike mukamai da dama na ilimi da shugabanci
  • Ya yi mulki na tsawon shekaru 30 yana kare al’adu da ci gaban yankin Bunza, tare da ba da shawarwari ga mutane da dama
  • Hon. Mohammed ya yi addu'ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya kuma bai wa iyalansa da mutanen Kebbi ƙarfin jere rashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin-Kebbi - Ɗan majalisar wakilai daga Kebbi, Hon. Ibrahim Bello Mohammed ya jajanta bayan rasuwar Sarkin Bunza a jihar.

Hon. Ibrahim wanda ke wakiltar mazabar Birnin-Kebbi/Bunza/Kalgo ya ce rashin Dr. Mustapha Muhammad Bunza babban asara ce.

Sarkin Bunza ya riga mu gidan gaskiya a Kebbi
An sanar da rasuwar Sarkin Bunza a jihar Kebbi. Hoto: Hon. Ibrahim Bello Mohammed.
Asali: Facebook

Ɗan majalisa ya jajanta rasuwar Sarkin Bunza

Kara karanta wannan

'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi

Ɗan majalisar ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook a jiya Alhamis 3 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Ibrahim ya ce marigayin ya ba da gagarumar gudummawa wurin kawo ci gaba a cikin al'umma.

Sanarwar ta ce:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.
"Ina cikin matuƙar alhini da jin zafin rasuwar Sarkin Bunza, Dr. Mustapha Muhammad Bunza, da ya rasu, ina mika ta’aziyyata ga iyalansa, ƙaramar hukumar Bunza, majalisar masarautar Kebbi, gwamnati da al’ummar jihar Kebbi.
"Marigayi Sarkin Bunza ya rayu da sadaukarwa da hidima, a matsayin malamin ilimi, marigayin wanda ya shafe shekaru 80 a duniya, ya bar baya mai ɗorewa.
"Ya rayu da kishin al’umma, fasaha da nuna ƙwazo, wanda ya shafi rayuwar al’ummar Bunza da yankinsa.
"Ya taka rawar gani wajen kare al’adu da al’adar Bunza yayin da yake da barin duniya."
An rashin babban basarake a Kebbi
Sarkin Bunza a jihar Kebbi, Dr. Mustapha Mohammed Bunza ya rasu. Hoto: Legit.
Asali: Original

Gudunmawar da marigayin ya ba al'umma

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Allah ya karbi rayuwar malamin Musulunci, Idris Dutsen Tanshi

Rashin marigayin babban asara ce ga waɗanda suka san shi da salon shugabancinsa.

A tsawon rayuwarsa, ya rike karagar sarauta na tsawon shekaru 30, ya kasance tsohon shugaban Kwalejin Shehu Shagari kuma shi ne tsohon magatakarda na Jami’ar Sokoto.

Har ila yau, marigayin ya rike muƙamin tsohon Darakta na hukumar malamai ta Najeriya (NTI), hakazalika, ya zama jagora da mai ba da shawara ga mutane da yawa.

Dan majalisar ya ce:

"Ina tare da mutanen Bunza a wannan lokaci na kunci, Allah ya sa baya da ya bari ya ci gaba da amfani.
"Allah ya gafarta masa, ya kuma bai wa iyalansa da waɗanda suka rage ƙarfin zuciya da juriya."

Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya rasu

Mun ba ku labarin cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya riga mu gidan gaskiya a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ku ɗauki kowa a matsayin ɗan gida," Sarkin Musulmi ya tura saƙo ga gwamnoni

Wasu majiyoyi sun ce Sheikh Idris Abdulaziz ya rasu ne cikin dare a ranar Alhamis, 3 ga Afrilu, 2025 bayan shafe lokaci mai tsawo yana jinya.

Fitaccen malamin ya bayar da gudummawa sosai wurin koyar da al'ummar Musulmi addini da tarbiyya wanda za a ci gaba da cin moriya har lokaci mai tsawo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng