Hotuna: Yadda Musulmi Suka Yi Cikar Kwari a Wurin Janazar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Hotuna: Yadda Musulmi Suka Yi Cikar Kwari a Wurin Janazar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

  • Dubban musulmai ne suka samu damar halartar janazar marigayi Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi a jihar Bauchi a yau Juma'a
  • Babban malamin na sunnah, wanda ya shahara da karantar da tsantsar tauhidi ya rasu ne a daren Juma'a bayan fama da jinya ta tsawon lokaci
  • Tuni dai manyan malumma a faɗin kasar nan suka fara tura sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan marigayi Dutsen Tanshi tare da yin addu'o'i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - A daren Juma'a ne Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke jihar Bauchi, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi rasuwa.

Babban malamin na sunnah ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci, har ta kai ga ya dakatar da karatuttukansa.

Wurin janazar Dutsen Tanshi.
An sallaci gawar Sheikh Idris Dutsen Tanshi a jihar Bauchi Hoto: @Social_Ustaxx
Asali: Twitter

A wasu hotuna da jaridar Leadership ta wallafa a shafin X, an yi jana'izar marigayi Sheikh Idris da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Juma'a, 4 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Yadda Dutsen Tanshi ya dawo Najeriya daga Indiya duk da tsananin rashin lafiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hotunan sun nuna yadda jama'a suka yi dandazo a wurin sallar jana'iza domin roka wa malamin gafara da kuma yi masa addu'ar samun rahamar Allah.

Dubban mutane ne ta ko'ina a filin babu masaka tsinke kuma dukansu sun halarci wurin ne domin yi wa Marigayi Malam Idris Dutsen Tanshi jana'iza.

Malam Idris.
Yadda musulmi suka yi cikar kwari a wurin jana'izar Sheikh Idris Dutsen Tanshi Hoto: @Social_Ustaxx
Asali: Twitter

Karatun Malam Idris Dutsen Tanshi

Marigayin ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar Madina, da ke kasar Saudiyya, inda ya karanci fannin ilimin shari'a.

Bayan ya dawo Najeriya, Sheikh Idris ya yi digirinsa na biyu a Jami'ar Jos kafin daga bisani ya tafi ƙasar Sudan ya yi digirin digirgir.

Rasuwarsa dai ta taɓa zukatan musulmin Najeriya kuma tuni malamai da ɗaliban ilimi suka tura sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan'uwan malamin.

Hotunan wurin jana'izar Idris Dutsen Tanshi

Martanin jama'a bayan janazar Tutsen Tanshi

Wani mai suna Social Ustaz a shafin X, ya wallafa cewa:

Kara karanta wannan

'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi

"In dai ba gudun Islamiyya ka yi ba, ka na ganin irin wannan dubun-dubatar mutane kasan Mallam tasa ta yi kyau. Allah ya sa Aljannah ce makomarsa idan tamu tazo Allah Ya sa mu cika da Imani."

Ahmad Sulaiman ya ce:

"Muna rokon Allah ya saka wa malam da gidan Aljannah."

Ibrahim Aliyu ya ce:

"Allah Ya jikansa Dr, Allah ya gafarta kura kuransa mu kuma idan ta mu ta zo, Allah ya ba mu kyakkyawan karshe."

Aisha Ahmad ta ce:

"Ko wane rai zai ɗanɗani mutuwa, Allah Ya gafarta ma Malam Idris Dutsen Tanshi Ya haskaka qabarinsa, da dukkanin musulmai."

Atiku ya yi alhinin rasuwar Dutsen Tanshi

A wani labarin, kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwa bisa rasuwar Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana marigayin a matsayin mutum na gari, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi da zaman lafiya.

A cewar Atiku, wannan rashi ne babba da ya shafi dukkanin al'ummar Musulmi da ke jihar Bauchi, Arewa da Najeriya baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262