Bayan Mummunan Hari da Bello Turji Ya Kai, Ƴan Bindiga Sun Kona Makaranta Kurmus

Bayan Mummunan Hari da Bello Turji Ya Kai, Ƴan Bindiga Sun Kona Makaranta Kurmus

  • 'Yan bindiga sun farmaki Rijiya da ke jihar Zamfara, suka kashe mutane takwas tare da kona wata makarantar firamare da ke garin
  • Shaidu sun bayyana cewa hare-haren sun faru da misalin karfe 4:00 na yamma, 'yan bindigar suka shiga kauyen dauke da manyan makamai
  • Cikin wadanda suka mutu, akwai 'yan sintiri biyu na CPG da kuma fararen hula guda shida da suka rasa rayukansu a harin miyagun
  • An ji cewa bayan kashe-kashen, 'yan bindigar sun kona makarantar firamare wadda ke zama matsuguni ga wasu daga cikin 'yan sintirin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai Rijiya da ke karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara ya yi sanadin mutuwar mutane takwas.

Bayan kai harin, maharan sun kuma kona makarantar firamare da ke Rijiya a birnin Gusau da ke Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

'Mun sha azaba': Janar Tsiga ya magantu, ya fadi dabbobin da suke kwana tare da su

Yan bindiga sun kai mummunan hari Zamfara
Yan bindiga sun kone wata makarantar firamare a jihar Zamfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda Turji ya fakaici ƴan ƙauyen Sokoto

Bayanan sun tabbatar wa Zagazola Makama cewa an kai harin da misalin karfe 4:00 na yamma, a ranar 3 ga Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan rikakken ɗan bindiga, Bello Turji ya kai wani mummunan hari a Sokoto ana bikin sallah.

Shahararren dan bindiga, Turji ya kai farmaki ne kan wasu manoma a garin Lugu da ke karamar hukumar Isa, a Sokoto.

Rahotanni sun ce Turji na dawowa ne daga wata ziyarar Sallah da ya kai a Isa lokacin da ya kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 11

Wasu mazauna yankin sun ce tun ranar Asabar aka samu labarin shirin Turji na kai ziyara zuwa gabashin Gatawa a karamar hukumar Sabon Birni.

Sun kara da cewa an mika bayanan sirri ga hukumomi domin su dauki matakin hana hakan, amma ba a yi komai a kai ba.

Kara karanta wannan

Matashi ya mutu, 1 kuma rai a hannun Allah bayan artabu kan budurwa a bikin sallah

Dan ta'adda, Bello Turji ya mai hari wani hari a Sokoto
Rikakken ɗan bindiga, Bello Turji ya kai hari da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a Sokoto. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun hallaka mutane 8 a Zamfara

Wani rahoto ya ce ƴan bindigar na dauke da AK-47 da makamai masu hadari, suka far wa kauyen.

Maharan sun bude wuta ba tare da kakkautawa ba, inda hakan ya yi sanadin mutuwar 'yan sintiri biyu na CPG da fararen hula guda shida a harin.

Baya ga asarar rayuka, 'yan bindigar sun kona wata makarantar firamare da 'yan sintirin ke amfani da ita a matsayin matsuguni.

Wannan hari ya jefa tsoro a zukatan mazauna yankin inda suke neman taimako daga hukumomi domin kawo karshen wannan hali da suka tsinci kansu a ciki.

An gwabza tsakanin Hausawa da Fulanin Zamfara

A baya, mun ba ku labarin cewa rigima ta barke tsakanin Fulani makiyaya da al’ummar Hausawa a Makarantar Firamare ta Dan Sokoto Model a Bungudu, Jihar Zamfara.

Wasu majiyoyi sun nuna cewa wani matashi mai shekaru 17, Abbas Sani, ya rasa ransa a rikicin bayan an tsinci gawarsa cikin jini wanda ya tayar da hankulan al'umma.

Jami’an tsaro sun kaddamar da farmaki a yankin da abin ya faru,suka cafke mutane 15 da ake zargi da hannu a haddasa rikici wanda ya yi sanadin rasa rai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng