'An Yi Babban Rashi,' Atiku Ya Yi Magana da Jin Labarin Rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana alhini bisa rasuwar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh AbdulAziz Dutsen Tanshi
- Atiku, wanda tsohon dan takarar shugaban kasa ne, ya nanata muhimmancin Sheikh Dutsen Tanshi wajen da'awa da kokarin yada zaman lafiya a Najeriya
- Ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babbar asara ba ga iyalansa kawai ba, har ma da sauran al'ummar musulmi a Bauchi da kasa baki daya
- Wazirin Adamawa ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa Sheikh Dutsen Tanshi, tare da sanya shi cikin bayinsa na gari da kuma azurta shi shi da aljanna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana jimaminsa da alhini game da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.
Atiku ya bayyana marigayin a matsayin mutum na gari, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi da neman zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Asali: Facebook
Wannan na kunshe a cikin sakon da tsohon mataimakin shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na X a safiyar Juma'a, yayin da ake jana'izar Malamin a jihar Bauchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya yi ta'aziyyar Dutsen Tanshi
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba iyalan Sheikh AbdulAziz Dutsen Tanshi ne kada suka yi rashinsa ba.
Ya ce wannan rashi ne babba ga dukkanin al'ummar Musulmi da ke jiha Bauchi, Arewa da kasa baki daya, duba da amfanin da ya ke da shi a cikin al'umma.
Atiku Abubakar ya ce:
“Rasuwar Sheikh Idris Abdulaziz babban rashi ne ga al’ummar Musulmi. Ya kasance malami mai zurfin ilimi da hikima, ina addu'ar Allah Ya gafarta masa, ya ba sanya shi a cikin bayi nagari."
Najeriya: Atiku ya fadi manufar Dutsen Tanshi
Atiku ya bayyana Sheikh Dutsen Tanshi a matsayin wani fitaccen malami wanda koyarwarsa da fatawoyinsa suka taimaka wajen gyara tarbiyya da ɗabi’un al’umma.

Asali: UGC
Ya bayyana cewa:
“Iliminsa da hikimarsa sun matuƙar amfanar da al'umma da dama. Wannan babban rashi ne ba wai kawai ga Bauchi ko arewacin Najeriya ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya."
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin, Ya sanya shi cikin Aljannar Firdausi tare da sauran bayinSa nagari.
Haka kuma ya yi addu’ar Allah Ya ba iyalan marigayin, almajiransa da mabiyansa haƙuri da juriyar wannan babban rashi.
Wasiyoyin Dutsen Tanshi kafin ya rasu
A baya, mun wallafa cewa Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, rasuwa bayan ya sha fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.
Dr. Idris ya bar wasiyoyi guda biyar da ya bukaci al’umma da su kiyaye, daga ciki har da haramta daukar hotonsa bayan rasuwarsa da hana shiga makabarta da takalmi idan za a birne shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng