An Samu Matsala a Gwamnatin Tinubu, Hakeem Baba Ahmed Ya Yi Murabus daga Muƙaminsa

An Samu Matsala a Gwamnatin Tinubu, Hakeem Baba Ahmed Ya Yi Murabus daga Muƙaminsa

  • Dr. Hakeem Baba Ahmed ya yi murabus daga muƙaminsa na mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa
  • A watan Satumba, 2023, Bola Tinubu ya nada Hakeem, tsohon mai magana da yawun NEF a cikin mashawarta
  • Bayan amincewa da nadin, Tinubu ya tura shi aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa watau Sanata Kashim Shettima
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa tun mako biyu da suka wuce, Hakeem ya miƙa takardar nurabus daga kan kujerar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Dr. Hakeem Baba-Ahmed, mai ba wa shugaba ƙasa shawara kan harkokin siyasa, ya yi murabus daga mukaminsa.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa tsohon mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa (NEF) ya mika takardar murabus dinsa kusan makonni biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

APC ta yi bayani kan shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Hakeem Baba Ahmed da Tinubu.
Dr. Hakeem Baba Ahmed ya yi murabus daga mukaminsa a fadar shugaban kasa Hoto: @yabaleftonline
Asali: Twitter

TABLE OF CONTENTS

Me yasa Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus?

Sai dai, babu cikakken bayani kan dalilan da suka sa ya yanke shawarar yin murabus, in ban da cewa ya ce yana da dalilai na kansa, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da ko fadar shugaban kasa ta amince da murabus dinsa ba.

An nada Hakeem Baba-Ahmed a matsayin mai ba wa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shawara kan harkokin siyasa a watan Satumba 2023.

A cikin watanni 17 da ya yi a ofis, ya wakilci fadar shugaban kasa a wurare da dama, ciki har da wani babban taron kasa kan inganta dimokuradiyya da aka gudanar a watan Janairu 2025 a Abuja.

Sabanin Baba-Ahmed da Matawalle

Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya sha suka a wasu lokuta a fadar shugaban ƙasa, musamman daga Ƙaramin Ministan Harkokin Tsaro, Bello Mohammed Matawalle.

A watan Afrilu 2024, Matawalle ya soki Hakeem Baba-Ahmed bayan ya kare kungiyar NEF, wadda ministan ya bayyana a matsayin “kungiyar da ba ta da tasiri a siyasa."

Kara karanta wannan

Gwamna ya ciri tuta, jam'iyyar APC Ta ba shi tikitin takara a zaɓen 2027

Wannan na zuwa ne bayan da ƙungiyar NEF ta fitar da wata sanarwa cewa yankin Arewa ya yi kuskure da zaben Shugaba Tinubu a 2023.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya mayar da martani, yana mai cewa zai fi dacewa ministan ya bayyana irin gudunmawar da ministocin Arewa suka bayar a gwamnatin Tinubu, maimakon sukar NEF.

Hakeem Baba Ahmed.
Hakeem Baba Ahmed ya yi murabus daga muƙaminsa a fadar shugaban kasa Hoto: Dr. Hakeem Baba Ahmed
Asali: UGC

Matawalle ya caccaki Hakeem Baba-Ahmed

A martaninsa, Matawalle ya jaddada cewa dole ne duk wani hadimin gwamnatin Tinubu ya kare martabar gwamnatin da yake yi wa aiki.

Ya kuma ce duk da Hakeem Baba-Ahmed yana da alaka da NEF, amma dole ne ya kare gwamnati daga “wannan irin suka da wasu ke yi suna fakewa da son kai da kabilanci.”

Ya zuwa yanzu, babu cikakken bayani kan makomar Baba-Ahmed bayan murabus dinsa.

Asalin dalilin korar shugaban NNPCL

A wani rahoton, kun ji cewa wasu jami'ai a fadar shugaban kasa sun yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa Bola Tinubu ya sallami shugaban NNPC, Mele Kyari.

Kara karanta wannan

'Magagin faduwa zabe bai sake shi ba,' Fadar shugaban kasa ta tankawa Peter Obi

Sun bayyana cewa korar ta samo asali ne daga yadda suke tafiyar da ayyukansu da gazawa wajen cimma manufofin samar da mai a ƙasar nan.

Wani jami'i, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa saboda ba a ba shi izinin magana kan lamarin ba, ya ce Tinubu ya yi haka ne domin yana shirun aiwatar da wasu abubuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel