Kwana Ya Ƙare: Allah Ya Karbi Rayuwar Malamin Musulunci, Idris Dutsen Tanshi
- Allah ya karbi rayuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi wanda aka tabbatar da rasuwarsa a jihar Bauchi
- Wasu majiyoyi sun ce Sheikh Idris Abdulaziz ya rasu ne cikin dare a ranar Alhamis, 3 ga Afrilu, 2025 bayan shafe lokaci mai tsawo yana jinya
- Fitaccen malamin Musulunci, Umar Shehu Zaria ne ya sanar da rasuwar Sheikh D/Tanshi, ya roki Allah gafarta masa kuma ya kyautata karshenmu
- Rashin lafiya ya sa shehin ya dakatar da karatuttuka da hudubobi wanda dalibansa suka ci gaba da jagoranci a masallacin Juma'a da ya saba yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa Allah ya karbi rayuwar Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi bayan ya sha fama da jinya mai tsawo.
Wasu majiyoyi sun ce shehin malamin ya rasu ne da daren yau Alhamis 3 ga watan Afrilun 2025 a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan
'A tsaye aka karɓi ta'aziyya ta': Sheikh ya fadi dattakun ɗaliban Malam Dutsen Tanshi

Asali: Facebook
An sanar da rasuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fitaccen malamin Musulunci, Umar Shehu Zaria ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
"Innaa lillahi wa innaa ilaihi raji'un.
"Yanzu nake samun labarin rasuwar Sheikh Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi.
"Allah ta'ala ya gafarta masa kuma ya kyautata namu bayan nashi."
Rahotanni sun tabbatar da cewa kafin rasuwar Sheikh Dutse Tanshi ya dauki lokaci mai tsawo yana jinya.
Hakan ya tilasta shi dakatar da karatuttukansa da kuma huduba a masallacin Juma'a da ya saba yi inda aka wakilta dalibansa.

Asali: Facebook
Dutsen Tanshi: An fadi lokacin sallar jana'iza
Har ila yau, shafin marigayin da ke yada karatuttukansa, Dutsen Tanshi Majlis Bauchi ya tabbatar da rasuwar Sheikh Idris a cikin wata sanarwa a Facebook.
Shafin ya bayyana cewa za a yi sallar jana'izar marigayin a gobe Juma'a da misalin karfe 10:00 na safe.

Kara karanta wannan
"Yana da abin al'ajabi da kura kurai," Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan Dutsen Tanshi
Sanarwar ta ce:
"Sallar jana'izar babban limaminmu, Imam Dr. Idris Bauchi (Rahimahullah) karfe: 10:00 na safe.
"Za a gudanar da sallar a masallacin Idi da ke 'Games Village' a Bauchi."
Al'ummar Musulmi da dama sun yi alhinin rasuwar marigayi Sheikh Idris Dutsen Tanshi da ya yi bankwana da duniya bayan fama da jinya.
Mafi yawan wadanda suka yi jimami sun tabbatar da cewa an yi rashin malami da ke tsage gaskiya komai dacinta ba tare tsoron kowa ba ko domin ya burge wani.
Legit Hausa ta yi magana da masoyin malam
Wani dalibin ilimi kuma masoyin marigayin ya fadawa Legit Hausa irin rashin da aka yi a Najeriya.
Ustaz Muhammad Umar ya ce tabbas an yi rashin malamin Tauhidi wanda ya tsaya tsayin daka kan haka.
"Malam ya yi nasara tun da har ya bar duniya yana kan akidarsa ta kaɗaita Allah shi kaɗai."
- Cewar dalibin

Kara karanta wannan
Bayan jana'izar Dr Idris, wani limami ya ja sallar Juma'a a masallacin Dutsen Tanshi
Daga ƙarshe, ustazun ya yi addu'ar Allah ya yi wa Malam rahama ya sanya shi gidan aljannar Firdausi.
Malamin Musulunci a Yobe ya kwanta dama
A baya, kun ji cewa rahoton da muka samu ya tabbatar da rasuwar Shugaban Majalisar Malamai na Ƙungiyar Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen jihar Yobe, Sheikh Imam Muhammad Khuludu Geidam.
Fitaccen malamin addinin Musuluncin ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025 wanda ya yi daidai da 26 ga watan Ramadan, 1446AH.
An ce Malamin ya ba da gudummuwa sosai ga al'umma ta fuskar wa'azi da ilimantar da jama'a hanyar rayuwa mai inganci bisa koyarwar addinin Musulunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng