An Gano Dalilin da Ya Sa Farashin Abinci Ya Kara Yin Kasa Warwas a Yankunan Arewa
- Rahotanni sun ce farashin kayan abinci ya ragu sosai a yankin Arewa maso Gabas wanda shi ne karon farko tun bayan cire tallafin mai a 2023
- A kasuwannin Adamawa, Yobe da Borno, farashin masara, shinkafa, dawa da wake sun sauka sosai, amma farashin doya da dabbobi sun hau
- 'Yan kasuwa sun ce raguwar farashin ya biyo bayan karancin kudin jari, karuwar noma da kuma rarraba abinci kyauta a cikin watan Ramadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - An tabbatar da cewa farashin kayan abinci ya sauka sosai a yawancin kasuwanni da ke yankin Arewa maso Gabas.
Rahotanni na cewa wannan shi ne karon farko da farashin kayan abinci ya sauka a yankin tun bayan cire tallafin man fetur a shekarar 2023.

Asali: Getty Images
Yadda farashi yake a kasuwar Adamawa

Kara karanta wannan
Matashi ya mutu, 1 kuma rai a hannun Allah bayan artabu kan budurwa a bikin sallah
Bincike a kasuwannin Adamawa, Yobe da Borno ya nuna raguwar farashin masara, shinkafa, dawa da wake, cewar rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, an gano cewa farashin doya, dankali, kifi, nama, fulawa, sukari da taliya ko dai sun tsaya cak ko kuma sun tashi kadan.
A kasuwar Jimeta a Adamawa, buhun masara mai nauyin kilo 100 da ake sayarwa tsakanin N60,000 zuwa N65,000 a Oktoba da Nuwamba 2024, ya ragu zuwa tsakanin N50,000 da N53,000 daga Janairu zuwa Fabrairu bana.
Malam Isah Bala, wani dan kasuwa a Kasuwar Jimeta, ya shaida cewa yanzu buhun masara yana tsakanin N40,000 zuwa N45,000.
Ya ce:
“Haka nan, buhun shinkafa na gida da ake sayarwa tsakanin N60,000 zuwa N65,000 a baya, yanzu yana N45,000.
“Farashin buhun wake mai nauyin kilo 100, wanda a shekarar 2024 ake sayarwa N190,000, ya fara sauka zuwa N160,000 kuma yanzu ya sauka zuwa N95,000."
Sai dai farashin doya ya karu a kasuwar doya ta Ganye, wacce ke zama cibiyar hada-hadar doya a jihar.
A halin yanzu, guda daya yana tsakanin N2,000 zuwa N2,500, gwargwadon girman ta.
Malam Dunama Maigida, wani dan kasuwa a kasuwar dabbobi ta Ngurore ya ce kasuwannin suna jan hankalin masu saye daga Najeriya da kasashe makwabta kamar Kamaru, Benin da Nijar.
A cewarsa, farashin shanu ma ya tashi cikin shekaru uku da suka gabata.
Ya ce:
“Sa da ake sayarwa tsakanin N200,000 zuwa N300,000 a baya, yanzu yana tsakanin N400,000 zuwa N700,000, wasu kuma har N1m."

Asali: Facebook
Farashin abinci a wasu kasuwannin Yobe
A Yobe kuwa, buhun shinkafa na gida mai nauyin kilo 100 da a baya ake sayarwa tsakanin N57,000 da N60,000, yanzu yana tsakanin N40,000 zuwa N43,000.
Farashin buhun wake na kilo 100 ya ragu daga N105,000 zuwa N85,000, yayin da na gero ya sauka daga N60,000 zuwa N46,000.
Buhun alkama ma ya sauka daga N110,000 zuwa N77,000, yayin da waken soya ya sauka daga N95,000 zuwa N80,000, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan
'Ba zan yi sata ba': Ɗan majalisa ya cire tsoro a gaban ƴan mazabarsa bayan shan suka
Malam Haruna Bukar, wani mai sayar da shinkafa da hatsi a kasuwar Monday Market, Maiduguri, ya ce farashin shinkafa ta gida ya ragu sosai.
A cewarsa, a 2024, buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 yana kan N80,000 amma yanzu yana tsakanin N65,000 zuwa N64,000, gwargwadon ingancinsa.
Ya ce buhun shinkafa ta waje da ake sayarwa N97,000, yanzu yana N70,000, yayin da farashin masara ya ragu daga N55,000 a 2024 zuwa N38,000 a yanzu.
“Buhun wake mai kilo 100 yanzu yana kusan N100,000, yayin da a 2024 yake N180,000, amma doya har yanzu tana da tsada, domin guda daya yana tsakanin N2,500 zuwa N3,000.”
Wasu manoma sun ce raguwar farashi ya samo asali ne daga rashin sayen kaya daga kungiyoyin agaji da kuma karuwar noma na gida.
An kuma danganta saukar farashin da watan Ramadan, inda kungiyoyin agaji da masu hannu da shuni suka raba kayan abinci kyauta, lamarin da ya rage bukatar sayen abinci.
Kano: An yi bikin karya farashin abinci
Kun ji cewa an yi wani biki na musamman domin rage farashin kayan abinci a Kano saboda saukaka wa jama’a radadin matsin tattalin arziki.
Shugabannin kasuwanni tare da goyon bayan gwamnatin Kano ne suka shirya bikin tallafin kayan abinci a jihar kafin azumin Ramadan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng