Akpabio ne Ya Kulla Makircin da Aka Kori Wasu Sanatoci 5 daga Majalisa? An Ji Gaskiya
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta zargin cewa shi ne ya sa hannu aka kori wasu sanatoci biyar daga majalisa ta 10
- Godswill Akpabio, ta bakin mai taimaka masa, Hon. Eseme Eyiboh, ya ce zargin Sanata Ishaku Elisha Abbo ba shi da tushe balle makama
- Hon. Eseme ya ce Sanata Abbo ya taba janye irin wannan zargi a 2023, inda ya amince cewa babu hannun Akpabio a tsige shi da kotu ta yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta zargin da Sanata Ishaku Elisha Abbo, ya yi masa kan korar wasu sanatoci biyar daga majalisar ta 10.
Abbo, wanda kotun daukaka kara ta tsige daga kujerarsa, ya yi ikirarin cewa Akpabio yana tafiyar da majalisa “kamar mulkin gidansa” tare da muzgunawa wadanda suka saba masa.

Kara karanta wannan
'Ba zan yi sata ba': Ɗan majalisa ya cire tsoro a gaban ƴan mazabarsa bayan shan suka

Asali: Facebook
A martaninsa, Akpabio, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Hon. Eseme Eyiboh, ya ce wannan zargi “ba shi da tushe balle makama,” inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Eseme Eyiboh ya kuma ce shugaba majalisa ba zai bari wasu maganganu marasa tushe su raba masa hankali daga aikin da ya sanya a gaba ba.
Martanin Akpabio ga kalaman Sanata Abbo
Sanarwar ta bayyana cewa Sanata Abbo yana neman a jefa laifin matsalarsa kan Akpabio, bayan da hukuncin da kotu ta yanke ya tabbatar da cewa bai cancanci kujerar Sanata ba.
A cewar sanarwar:
“Abbo ya taba janye irin wannan zargi a shekarar 2023, inda ya yarda cewa ya yi gaggawar yin furuci ba tare da cikakken bayani ba.”
Sanarwar ta kara da cewa bayan wata tattaunawa da suka yi da Akpabio a bara, Abbo ya yarda cewa shugaban majalisar “ba shi da hannu” a hukuncin kotu da ya cire shi daga majalisa.

Kara karanta wannan
Ana cikin dambarwar Natasha, tsohon sanata ya yi sababbin zarge-zarge kan Akpabio
“Abin mamaki ne yadda Abbo ke dawowa kan irin wannan zargi da kansa ya janye a baya," inji Hon. Eseme.
- Hon. Eseme.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Akpabio ba shi da wata hujja da Sanata Abbo zai jingina korarsa ga shugaban majalisar, bayan da ya yarda da hukuncin kotu a baya.
Zargin rashin biyan hakkokin Sanata Abbo
Sanata Abbo ya kuma yi zargin cewa an hana shi hakkinsa na albashi, alawus, da motar aiki bayan kotu ta tsige shi daga mukaminsa.
Sai dai sanarwar ta ce Akpabio ba shi da ikon ya fitar da kudi sai dai idan an tantance bukatar daga sashen kula da harkokin kudi na majalisa.
“Idan har bukatar Abbo ba ta isa ga teburin shugaban majalisa ba, hakan yana nufin ba ta cika ka’idojin da ake bi ba.”
- Hon. Eseme.
Har ila yau, sanarwar ta ce korafin da Abbo ke yi kan rashin biyan kudaden tafiye-tafiye da wasu hakkokinsa, shiryayyun makirce-makirce ne kawai da ba su da tushe.

Kara karanta wannan
Sanata: "Akpabio ya buɗe kofar kashe Natasha, kuma ba za a iya cire ta a majalisa ba"
'Shugaban majalisa ta aikinsa ya ke yi' - Eseme
Sanarwar ta ce Akpabio zai ci gaba da aikin gina kasa da jagorantar majalisa bisa tafarkin dimokuradiyya ba tare da wata tsangwama ba.
Eseme ya ce:
"Sanata Godswill Akpabio na ci gaba da mai da hankali kan aikin gina, gudanar da jagoranci mai ma’ana a majalisar dattawa, da kuma karfafa cibiyoyin dimokuradiyya – musamman 'yancin kotu."
Sanarwar ta kuma bukaci Sanata Abbo da ya daina yada jita-jita, ya kuma mayar da hankali kan farfado da mutuncinsa a siyasa.
"Akpabio ya bude kofar kashe Natasha" - Abbo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Elisha Ishaku Abbo ya zargi Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da nuna son rai kan Sanata Natasha Akpoti.
Elisha Abbo, wanda tsohon sanatan Adamawa ne, ya zargi Akpabio da bude kofar da za a iya kashe Sanata Natasha saboda dakatar da ita da janye mata masu tsaro da aka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng