'Mun Sha Azaba': Janar Tsiga Ya Magantu, Ya Fadi Dabbobin da Suke Kwana Tare da Su
- Janar Maharazu Tsiga ya bayyana irin wahalar da ya sha a hannun 'yan bindiga bayan shafe watanni kusan biyu a tsare a daji
- Tsohon sojan ya ce an tsare su a cikin daji cike da macizai, kunama, da kuraye inda ta kusa kai musu hari a kan dutse
- 'Yan bindigar sun yi amfani da su a matsayin garkuwa yayin hare-haren sojoji, sun kuma saka bam a inda yake barci
- Tsiga ya gode wa Nuhu Ribadu da hafsan tsaro bisa kubutar da su, yana mai cewa tsaro hakkin kowa ne, ba wai gwamnati kadai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon Darakta-Janar na NYSC, Birgediya-Janar Maharazu Tsiga mai (ritaya), ya bayyana irin halin da ya shiga a hannun yan bindiga.
Janar Tsiga ya fadi haka ne bayan shafe kusan wata biyu a hannun 'yan bindiga da suka sace shi a Katsina.

Asali: Facebook
Wahalhalun da Tsiga ya sha a hannun miyagu
Tsiga ya ce sun kasance a wani daji mai girma, cike da dabbobi masu hadari da suka hada da kuraye, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon sojan ya ce tsira da ransa ba komai ba ne face ikon Allah wanda ya nuna girmansa.
Ya ce:
“An tsare mu tare da dabbobi masu hadari kamar kuraye, macizai, da kunama.
"Kafin a sake ni, wata kura ta fara zagaye mu tana neman abinci, menene abincinta? Mu ne!
“A kullum mu na zaune da macizai da kunama. Abu mafi tsoro shi ne yadda suke amfani da mu a matsayin garkuwa yayin hare-haren sojoji. Sun so jiragen yaki su kashe mu. Amma ikon Allah ya fi karfinsu.
"NSA da CDS sun riga sun fada na gari za su tsira, amma marasa gaskiya za su hallaka a karshe."

Asali: Twitter
Yadda Janar Tsiga ya sha da kyar
Janar Tsiga ya kuma tuna yadda 'yan bindigar suka so halaka shi da bam lokacin da yake hannunsu, cewar Punch.
Ya kara da cewa:
“Wani roka da aka harba bai fashe ba, sun dauke shi sun saka a inda na ke barci. Amma Allah ya kiyaye ni.”
“Sun yi kokarin kutsa kai gidana, amma ba su iya ba, sai suka tafi Kaduna suka tarwatsa gidan da bam.”
A madadin sauran mutum 18 da aka ceto, Tsiga ya gode wa Malam Nuhu Ribadu da hafsan tsaron Najeriya, yana mai cewa:
“Tsaro nauyi ne a kan kowa, kowa ya rika bayar da bayanai masu amfani domin kawo karshen ta'addanci."
Janar Tsiga ya tsira daga hannun yan bindiga
Kun ji cewa Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta kasa ta miƙa tsohon shugaban NYSC, Maharazu Tsiga, da wasu mutane 18 da aka ceto ga Nuhu Ribadu a Abuja.
Ana ganin kubutar da mutanen 19 wani ci gaba ne a yaƙi da 'yan bindiga, bayan Janar Tsiga ya shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa.
Nuhu Ribadu ya jinjinawa jami’an tsaro kan nasarar ceto Tsiga da mutane 18, tare da jaddada aniyar gwamnati na inganta yanayin tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng