Ana Fargabar Fulani Sun Farmaki Garuruwa 5 a Filato, Sun Hallaka Mutane da Dama

Ana Fargabar Fulani Sun Farmaki Garuruwa 5 a Filato, Sun Hallaka Mutane da Dama

  • Aƙalla mutane 10 aka kashe a ranar Laraba sakamakon hare-hare da aka kai a ƙauyuka biyar na ƙaramar hukumar Bokkos, jihar Filato
  • A cikin wata sanarwa da kungiyar BCDC ta fitar, an ce yankin na fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda da ke yunƙurin mamaye ƙasarsu
  • Sanarwar ta ce wadanda suka farmaki garuruwa biyar din na magana da Fulatanci, wanda ya sa ake zargin ko Fulani ne suka kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Akalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu a ranar Laraba sakamakon hare-hare da aka kai kan garuruwa biyar a ƙaramar hukumar Bokkos da ke jihar Filato.

Wadannan hare-hare sun faru ne kwana shida bayan makamancin hakan ya faru a garin Ruwi, inda aka harbe mutum goma har lahira, kamar yadda muka rahoto.

Kara karanta wannan

Musulmi sun ba Hausawa shawara kan kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Kungiyar BCDC ta magantu da aka kashe mutane 10 a hare-haren da aka kai garuruwan Filato
An kashe akalla mutane 10 a hare-haren da aka kai garuruwa 5 na jihar Filato. Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Bayanin hare-haren da aka kai kan garuruwa biyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar raya al’adu ta Bokkos (BCDC) ta fitar, wacce jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan ta'adda na barazana ga Bokkos" - BCDC

Sanarwar mai dauke da sannun shugaban BCDC, Farmasum Fuddang ta ce mutanen yankin Bakkos na cikin barazanar ‘yan ta’adda da ke yunƙurin ƙwace ƙasarsu don kafa sabuwar daula.

A cewar sanarwar:

"A cikin mako guda kacal, mun rasa rayukan fiye da mutum 20 sakamakon hare-haren wadannan ‘yan ta’adda da ke ci gaba da yi wa garuruwan nan biyar kisan kare dangi.
"A ranar 2 ga Afrilu kawai, sun kashe fiye da mutum 10. Wadanda suka tsira sun bayyana cewa maharan suna magana ne da harshen Fulantanci, shi ya sa ake zargin ko Fulani ne.
"Wadanda suka tsira sun bayyana cewa maharan sun kai hari da tsakar rana a garin Mangor Tamiso, sannan suka zarce zuwa Daffo da Manguna (Tagai), sannan suka shiga Hurti da Tadai."

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Yadda Edwin Clark da fitattun ƴan siyasa 4 suka mutu a 2025

Jinjina ga jami’an tsaro da kira ga 'yan Bokkos

An nemi mazauna Bokkos su sanya ido tare da daukar matakan kare kai daga 'yan bindiga
Kungiyar BCDC ta nemi mazauna Filato su tashi su kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kungiyar ta BCDC ta jinjinawa jami’an tsaro bisa saurin mayar da martani ga kiran gaggawa da ake yi masu, wanda hakan ya rage yawan hasarar rayuka a hare-haren.

Haka kuma, an shawarci al’ummar yankin da su kasance masu sa ido, tare da haɗa kai da jami’an tsaro domin dakile barazanar hare-haren da ake kai musu.

Channels TV ta rahoto sanarwar ta kara da cewa:

"Kada mutanen Bokkos su yarda ana yanka su kamar kaji, kuma kada su dogara kacokan ga jami’an tsaro na gwamnati, domin ba za su iya kasancewa a kowane wuri ko kare kowa ba.
"Akalla, dole ne ‘yan ƙasa su mallaki makamai da ba a haramta ba domin dakile maharan idan sun kawo farmaki har sai agaji ya iso. Idan ba haka ba, kullum sai an rasa rayuka."

'Yan ta'adda sun farmaki Bakkos, Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu miyagu da ake kyautata zaton cewa 'yan bindiga ne sun farmaki kauyen Budel da ke yankin Tangur a Bukkos, jihar Filato.

Shugaban ƙaramar hukumar Bukkos, Monday Kassah, ya ce maharan sun shiga garin da daddare, suka ƙona tare da lalata gidajen bayin Allah.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng