"Bello Turji Ya Kusa Mutuwa," Dakarun Sojojin Najeriya Sun Yunƙuro da Zafi Zafi
- Rundunar Sojin Najeriya ta jaddada cewa kwanaki kaɗan ne suka rage wa kasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji a duniya
- Mai magana da yawun hedkwatar tsaro (DHQ), Manjo-Janar Markus Kangye ya ce nan ba da daɗewa ba Bello Turji zai haɗu da mahaliccinsa
- Ya kuma bayyana cewa ba su ji daɗin yunƙurin ficewar Jamhuriyar Nijar daga rundunar haɗin guiwa ba, ya ce za a ci gaba da tattaunawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar hedkwatar rundunar sojin Najeriya (DHQ), a ranar Alhamis, ta bayyana cewa kwanakin shahararren ɗan bindiga, Kachalla Bello Turji, sun kusa karewa.
Sojojin sun yi watsi da jita-jitar cewa sun rage kaimi wajen yaki da makiyaya, ‘yan ta’adda, da masu satar shanu, inda suka jaddada cewa suna nan suna farautar Bello Turji.

Asali: Twitter
Bello Turji ya kashe manoma 11
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan martani na sojoji ya zo ne kasa da sa’o’i 24 bayan da Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu, karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa Bello Turji na hanyar dawowa daga ziyarar Sallah ne a wani ƙauye da ke yankin Isa, lokacin da ya kai wannan hari.
Da yake amsa tambayoyi a taron manema labarai a hedikwatar tsaro, Daraktan Yada Labarai na DHQ, Manjo-Janar Markus Kangye, ya ce dakarun sojoji za su ci gaba da murkushe ƴan ta'adda.
Sojoji sun kusa tura Bello Turji lahira
A ruwayar Leadership, kakakin DHQ ya ce:
“Batun cewa sojoji sun tsame hannunsu daga yaki da masu satar shanu da wasu ‘yan ta’adda ba gaskiya ba ne.
"A yadda na karanto rahoto, dakarunmu sun kama wasu manyan motoci dauke da shanu, kuma har yanzu suna kokarin cafke manyan ‘yan ta’adda.
“Ina kuma son tunatar da ku cewa a cikin watanni ukun da suka gabata, mun kawar da wasu manyan ‘yan ta’adda. Dangane da Bello Turji, lokaci ne kawai, ba da dadewa ba zai hadu da mahaliccinsa.”
Jamhuriyar Nijar za ta janye dakarunta?
Game da janyewar Jamhuriyar Nijar daga Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasashen Yankin Tafkin Chadi (MNJTF), Manjo-Janar Kangye ya ce hakan barazana ce ga tsaro.
Ya bayyana cewa MNJTF tana da muhimmanci a hadin gwiwar tsaro na yankin, don haka dole ne a yi kokarin hana kowace kasa ficewa daga cikin rundunar.
“An dade ana tattaunawa a kan wannan batu, musamman lokacin da wasu kasashen ECOWAS suka yi yunkurin haɗa kawance da ficewa daga ECOWAS.
“Amma dai kun san cewa MNJTF an kafa ta ne bisa yarjejeniyar kasashen Tafkin Chadi domin magance matsalolin tsaro na yankin.
“Nijeriya tana kokarin tabbatar da dorewar wannan runduna, don haka, idan wata kasa ta janye, hakan zai haifar da gibin tsaro kuma zai rage karfin dakarun da muke da su daga wannan kasa.”
Sojoji sun cafke hatsabiban ƴan bindiga 2
A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun cafke wasu hatsabiban ƴan bindiga guda biyu da dillalin makamai, Shehu Bagiwaye a jihohin Zamfara da Sakkwato.
Wannan na ɗaya daga cikin nasarorin da dakarun sojin ke ci gaba da samu a yaƙi da ƴan fashin daji da suka addabi jama'a musamman a Arewa maso Yamma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng