"Najeriya Ta Yi Kuskure," Gwamna Ya Tono Yadda Boko Haram da Ƴan Bindiga Suka Yi Ƙarfi
- Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa Najeriya ta yi babban kuskure da ta bari ƴan ta'adda suka yi ƙarfi
- Mutfwang ya ce lokaci ya yi da dukkan masu ruwa da tsaki za su haɗa kai a kawo ƙarshen wannan matsala ta tsaro da ake fama da ita
- Gwamnan ya yabawa dakarun sojojin Najeriya bisa namijin kokarin da suke yi a yaƙi da ƴan tada ƙayar baya a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau - Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato ya bayyana cewa Najeriya ta yi babban kuskure da ta kyale Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda suka yi ƙarfi a wasu sassan kasar nan.
Gwamna Mutfwang ya ce lokaci ya yi da shugabanni da mahukunta za su tabbatar da cewa babu wata ƙungiya da za ta iya ƙara yin tasiri iyakokin Najeriya.

Asali: Facebook
Mutfwang ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar da sababbin jiragen yaki marasa matuka da gwajin bama-bamai da aka ƙera a gida, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane kuskure Najeriya ta yi?
An kaddamar da jiragen ne a hedikwatar kamfanin fasahar Briech UAS da ke Kuje a babban birnin tarayya Abuja.
Kamfanin na cikin gida ne kuma ya ƙware wajen kera jiragen leƙen asiri da na yaki.
A tsawon fiye da shekara goma, ‘yan ta’addan Boko Haram na aiki a wasu sassan ƙasar, musamman yankin Arewa maso Gabas, ta hanyar dasa bama-bamai da haddasa fashe-fashe.
Gabanin kaddamar da sababbin na’urorin tsaro, Gwamna Mutfwang ya bukaci shugabanni su yi haɗin gwiwa da kamfanonin fasaha don magance matsalolin ƙarancin samun kayan aiki daga ƙasashen waje.
Gwamna Mutfwang ya yabi sojoji
“Ina matuƙar godiya ga sojojin Najeriya saboda irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen kare ƙasarmu.
"A matsayina na gwamna, zan iya tabbatar da ƙwarewa da nagartarsu wajen sauke nauyin da ke kansu. Wannan ne ya sa Filato ke ƙara samun zaman lafiya da ci gaba.
“Daya daga cikin hanyoyin da suka taimaka wajen cimma wannan nasara ita ce amfani da fasaha wajen yaki da barazanar tsaro.
- Inji Mutfwang.
Amfani da fasahar zamani ya taimaki Filato
Gwamnan ya kara da cewa an samu sauƙin matsalar tsaro a jihar Filato ne saboda amfani da fasahar zamani da haɗin guiwar da gwamnatinsa ta yi da kamfanin Briech UAS.
Mutfwang ya ƙara da cewa:
"Wannan ne ya sa muka shiga haɗin gwiwa da kamfanin Briech UAS, wanda ya kawo sabbin na’urori da suka taimaka sosai wajen inganta aikin hukumomin tsaro a jiharmu.
“A hakikanin gaskiya mun yi kuskure da muka kyale ‘yan ta’adda suka mallaki kayan aiki da suka kusa rinjayar na gwamnati. Yanzu lokaci ya yi da za mu gyara wannan kura-kurai.
"Dole ne mu kai matakin da babu wani ɗan ta'adda da zai iya aiki a cikin Najeriya da ƙwarewa da kayan aiki da suka kai ko wuce na jami’an tsaronmu.
Gwamnan Filato ya haɗa kai da Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Plateau ƙarƙashin jagorancin Caleb Mutfwang ta sanar da kulla yarjejeniya da kasar Isra'ila domin wasu inganta ɓangarori.
Gwamna Caleb Mutfwang ya ce yarjejeniyar ta mayar da hankali kan noma, fasaha da kiwon lafiya muhimman fannoni da ke da matukar tasiri.
Asali: Legit.ng