Sanata: "Akpabio Ya Buɗe Kofar Kashe Natasha, kuma Ba Za a Iya Cire Ta a Majalisa ba"
- Tsohon Sanatan Adamawa, Elisha Ishaku Abbo ya zargi Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da nuna son rai
- Haka kuma ya zarge shi da amfani da karfin iko wajen dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar dattawa
- Tsohon Sanatan ya bayyana takaicin yadda majalisar kasar nan ta raina hukuncin kotu, tare da karfa-karfa wajen gudanar da aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Sanatan Adamawa ta Arewa, Elisha Ishaku Abbo, ya bayyana cewa babu wanda zai iya yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye.
Ya soki yadda majalisar dattawa ta dakatar da Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya Natasha, tare da zargin Shugaban majalisa, Godswill Akpabio, da nuna son rai.

Asali: Facebook
A wata hira da Arise News, Sanata Abbo ya bayyana cewa hanyar da Akpabio ya bi wajen dakatar da Natasha ba ta dace ba, musamman idan aka duba yadda ya kasance a baya a majalisar dattawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya tuna yadda Akpabio, a lokacin da yake majalisar dattawa ta 8, ya samu sabani da tsohon Shugaban majalisar, Bukola Saraki, amma aka warware matsalar cikin girmamawa.
Natasha: Sanata Abbo ya caccaki Akpabio
Jaridar Leadership ta ruwaito Sanata Abbo ya kara da cewa janye jami’an tsaron Natasha da shugaban majalisar, Akpabio ya yi ya jefa rayuwarta cikin hadari.
Ya ce:
“Idan ka janye tsaron mutum—wanda bai dace ba—yana nufin ka fito da ita a fili domin a kashe ta. IGP ya fahimci cewa hakan ba abu ne mai kyau ba, domin idan gobe aka ji an kashe Natasha, lamarin zai canza.”
Abbo ya zargi Akpabio da kama karya
Yayin da yake sukar yadda majalisa ta dakatar da Natasha, Abbo ya kwatanta lamarinta da irin abin da Akpabio ya aikata a baya a majalisar dattawa.
Abbo ya ce:
“Idan ba a dakatar da Akpabio ba a majalisa ta 8, me yasa za a dakatar da Natasha har na tsawon watanni shida, idan dalilinku kawai shine gurin zama?”

Kara karanta wannan
Bayan bijirewa gwamnati, Sanata Natasha ta sake dura kan Akpabio da tsohon gwamna
Sanatan ya jaddada cewa Natasha ta samu hukuncin kotu da ya hana majalisar dattawa bincikenta har sai an kammala shari’ar da ake yi.

Asali: Twitter
Sai dai ya ce majalisar dattawa ta yi watsi da wannan hukunci, yayin da ya kuma zargi Akpabio da nuna karfin ikon siyasa.
“Majalisar dattawa ta saba wa hukuncin kotu tare da dakatar da ita—wannan raini ne ga kotu.
“Bayan sun gama dakatar da Natasha ne sannan suka garzaya kotu don su soke hukuncin da ke hana su yin hakan."
Abbo ya magantu kan yi wa Natasha kiranye
Dangane da shirin yi wa Natasha kiranye daga majalisa, Abbo ya yi watsi da cewa ana samun ci gaba a lamarin, yana mai cewa duk abin da ke faruwa wata makarkashiya ce.
Sanatan ya ce:
“Na ji suna cewa su na so su yi mata kiranye—babu wanda zai iya yi wa Natasha kiranye. Ba a kasar da babu doka muke ba. Sun tafi sun kitsa sa hannun jabu.”
INEC ta aika saƙon kiranye ga Natasha
A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta sanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, game da yunkurin yi mata kiranye daga majalisa.
Sakatariyar hukumar INEC, Ruth Oriaran Anthony, ce ta sanya wa sanarwar hannu, inda ta tabbatar da cewa an riga an isar da sakon kiranyen zuwa ga Sanatar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng