Bayan Sauke Mele Kyari, NNPCL Ya Kara Kudin Man Fetur
- Kamfanin NNPCL ya ƙara farashin fetur zuwa N925 a Lagos da kuma N950 a Abuja daga ranar 2 ga Afrilu, 2025
- Karin farashin na zuwa ne bayan dakatar da sayar da danyen mai a Naira da NNPCL ya yi a matatar Dangote
- An samu karin kudin ne sa'o'i bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke shugaban NNPCL, Mele Kyari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja Kamfanin NNPCL ya ƙara farashin fetur daga N860 zuwa N925 a Lagos, yayin da a Abuja aka daga farashin daga N880 zuwa N950.
Karin farashin fetur ya zo ne bayan da wasu 'yan kasuwa masu zaman kansu suka riga NNPCL ƙara farashin su zuwa N930 a Lagos da N960 a Arewacin Najeriya.

Asali: Getty Images
Punch ta tabbatar da cewa karin kudin da NNPCL ya yi ya fara aiki ne daga ranar Laraba, 2 ga Afrilu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masana sun ce karin ya biyo bayan dakatar da sayar da danyen mai da Naira da aka yi ne ga matatar Dangote ta yi, wanda hakan ke nuna yadda tsarin kasuwar mai a Najeriya ke sauyawa.
Dalilin samun karin kudin man fetur
Sabon tsarin farashin fetur na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubalen hauhawar farashin danyen mai a duniya, da kuma sauyin canjin kudi wanda ke shafar farashin kayayyaki.
The Cable ta wallafa cewa a watan Maris 2025, NNPCL ya rage farashin fetur zuwa N860 domin dacewa da farashin matatar Dangote.
Sai dai ana ganin hauhawar farashin danyen mai da matsalolin samar da shi sun tilasta sake duba farashin.
Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa tashoshin mai na NNPCL da ke kan titin Lagos-Ibadan Expressway da Ikorodu sun fara sayar da fetur kan N925 bayan sun nuna N930 a farko.
Sauye sauye a kamfanin NNPCL
A daidai lokacin da aka samu kari kudin, Shugaba Bola Tinubu ya nada Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin NNPCL, wanda ya maye gurbin Mele Kyari.
Haka kuma, an sake fasalin hukumar gudanarwar kamfanin, lamarin da masana ke gani ka iya shafar tsare-tsaren da kamfanin zai dauka a nan gaba kan farashin man fetur.

Asali: Facebook
Karin farashin fetur a Abuja da Legas
A Abuja, tashoshin mai na NNPC da ke kan titin Kubwa sun daga farashin fetur daga N880 zuwa N950, yayin da wasu tashoshi a Wuse suma suka yi irin wannan karin.
Ko da yake, a wasu sassan Lagos, har yanzu akwai wasu tashoshin NNPC da ba su canza farashin ba saboda wasu dalilai.
Daga cikin tashoshin da suka fara aiki da sabon farashin sun hada da na Fadeyi, Ago Palace Way, Ogba da kuma College Road.
Haka kuma a Ikeja, tashoshin da ke Acme Road da hanyar Lagos-Abeokuta sun fara aiki da sabon farashin na N925.
Abubuwan da Mele Kyari ya yi a NNPCL
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man Najeriya ya samu wasu nasarori da suka hada da samar da wutar Maiduguri a lokacin Mele Kyari.
Bayan nasarorin, wasu abubuwa sun faru da suka jawo yabo da suka ga kamfanin ciki har da samun tangardar cigaba da sayar da danyen mai a Naira.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng