'Dan Sanda a Kaduna Ya Shiga Matsala game da Kiran Daukar Fansa kan Ƴan Kudu a Arewa
- Wani dan sandan Kaduna ya yi barazanar daukar mataki kan ‘yan Kudu da ke Arewa bayan kashe ‘yan yankin 16 a Uromi da ke Edo
- Hadaina Hussaini Dan-Taki ya ce dole ne su dauki mataki cikin mako guda, inda ya ke cewa ‘yan Kudu suna zaune a Arewa ba tare da matsala ba
- An ce bayan suka kan furucinsa, Dan-Taki ya canza sunansa a Facebook kuma ya takaita damar ganin wallafarsa don gujewa karin matsala
- Rahotanni sun ce yan sanda sun kama mutane 14 da ake zargi, an tura su Abuja don bincike bayan Gwamnan Edo ya ce za a hukunta masu laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Wani dan sanda a jihar Kaduna, Hadaina Hussaini Dan-Taki, ya yi barazanar kai hare-hare kan ‘yan Kudu da ke zaune a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan
"Mutane sun yi takansu": Halin da ake ciki a garin da aka kashe ƴan Arewa 16 a Edo
Dan-Taki ya yi wannan furuci ne bayan kisan gilla da aka yi wa ‘yan Arewa 16 a Uromi, karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo.

Asali: Facebook
Yadda aka hallaka ƴan Arewa a Edo
A cikin wata wallafa da aka yi a Facebook da Punch ta gano, a jiya Talata, Dan-Taki ya rantse da Allah, yana mai cewa dole ne ‘yan Arewa su dauki mataki kan ‘yan Kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin yanzu an ce an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, an tura su Abuja don bincike.
Harin ya faru ne a ranar Alhamis 28 ga watan Maris, 2025 da ta gabata lokacin da ‘yan Arewa da ke hanyarsu ta komawa Kano don bikin Sallah.
An duba motarsu, aka gano bindigogi na ƴan farauta, daga nan aka yi musu kisan gilla, lamarin da ya jawo fushi da kiran a hukunta masu laifi.

Kara karanta wannan
Fulani sun dauki fansa, sun kona Inyamurai kurmus a Kano? Ƴan sanda sun fadi gaskiya
Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya ce harin abin takaici ne kuma za a tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Asali: Twitter
Ɗan sanda ya jefa kansa a matsala
Ɗan sandan mai suna Ɗan-Taki ya yi rantsuwa cewa dole ne su dauki mataki duba da yadda yan Kudu ke zaune a Arewa lami lafiya.
Ɗan sandan ya ce:
“Na rantse da Allah, dole mu dauki mataki a kanku, kun manta akwai ‘yan uwanku da ke zaune a Arewa? Ku ba da nan da mako guda za ku ga sakamako.”
Bayan da mutane suka fara suka kan wallafarsa, Dan-Taki ya canza sunansa kuma ya takaita damar ganin shafinsa na Facebook don kaucewa karin matsala.
Wani mai amfani da X, mai suna Uche ya yi kira da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Abuja ya dauki mataki.
Olumuyiwa Adejobi wanda shi ne jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, ya amsa da cewa:
“An dauki matakin da ya dace, na gode.”
An jibge jami'an tsaro a Uromin jihar Edo
Mun ba ku labarin cewa mazauna yankin Uromi na Jihar Edo, garin da aka yi wa Hausawa kisan gilla, sun fada cikin fargabar harin ramuwar gayya.
Majiyoyi sun bayyana cewa wannan fargaba ta sa aka jibge tarin jami'an tsaro, ciki har da 'yan sanda da jami'an farin kaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng