Abin da Buhari Ya ce bayan Rasuwar Dattijo, Galadiman Kano, Ya Fadi Giɓin da Ya Bari

Abin da Buhari Ya ce bayan Rasuwar Dattijo, Galadiman Kano, Ya Fadi Giɓin da Ya Bari

  • Tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi jimamin rasuwar Abbas Sunusi, Galadiman Kano, wanda ke da matsayi mai daraja
  • Galadima shi ne matsayi mafi girma da 'ya'yan sarakunan Kano ke rike wa, kuma ya kasance ginshikin al'ada da tarihin masarautar
  • Buhari ya ce marigayin ya zama jigo a ci gaba, da ya haɗa tarihi da zamani tare da taka muhimmiyar rawa a fadar masarautar Kano
  • Ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, masarautar Kano, da gwamnatin jihar, yana addu'ar Allah Madaukaki ya jikansa da rahama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi magana kan mutuwar Galadiman Kano.

Buhari ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Alhaji Abbas Sunusi kuma babban mamba a majalisar masarautar jihar.

Buhari ya kaɗu da rashin dattijo Galadiman Kano
Muhammadu Buhari ya yi alhinin rasuwar Galadiman Kano wanda ya rasu a jiya Talata. Hoto: Sanusi II Dynasty, Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Yaushe Galadiman Kano ya rasu?

Kara karanta wannan

"An yi rashi," Shugaba Tinubu ya yi magana da Allah ya karɓi rayuwar Galadiman Kano

Wannan na cikin wata sanarwa da hadiminsa, Mallam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba 2 ga watan Afrilun, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Buhari na zuwa ne bayan sanar da rasuwar dattijon a jiya Talata 1 ga watan Afrilun 2025 da muke ciki.

Rahotanni na nuni da cewa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, ya rasu ya na da shekaru 92 a duniya.

Masarautar Kano ta bayyana cewa ya rasu ne a daren Talata 1 ga Afrilu, 2025, bayan wata jinya mai tsawo

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an yi jana’izarsa a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu da misalin karfe 10:00 na safe a yau Laraba 2 ga watan Afrilun 2025.

Galadiman Kano: Abba ya soke gaisuwar sallah

Bayan rasuwar Galadiman Kano, gwamnatin jihar Kano ta soke gaisuwar karamar Sallah da masarautun Rano da Karaye aka shirya yi.

Kara karanta wannan

Uromi: Barau ya yi alkawari bayan ziyarar iyalan Hausawan da aka kashe a Edo

Gwamnatin Kano ta umurci jami’ai su hallara a gidan gwamnati da karfe 9:30 na safe domin tafiya jana’izar marigayin da karfe 10:00 na safe.

Marigayin ya rike mukamin Galadima, wanda shi ne matsayi mafi girma da 'ya'yan sarakunan Kano ke rike wa.

Har ila yau, marigayin taka rawa wajen haɗa tarihi da zamani a masarauta musamman a Kano.

Buhari ya jajantawa al'ummar Kano bisa rashin da suka yi
Muhammadu Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Galadiman Kano a jiya Talata. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

'Mun yi babban rashi' - Buhari ga ƴan Kano

Buhari ya ce tabbas wannan babban rashi ne ba iya jihar Kano kadai ba har ma da Arewa da kuma Najeriya baki daya.

A cewarsa:

“Kano da ƙasa baki daya sun rasa jigo mai kawo zaman lafiya.
"Galadima ya kasance ginshikin al'ada da tarihin masarauta, mai matukar muhimmanci."

Tsohon shugaban ya mika ta’aziyya ga iyalan mamacin, masarautar Kano, da gwamnatin jihar, yana addu'ar Allah ya jikansa da rahama.

Kanawa sun yi martanin rasa Galadiman Kano

Mun ba ku labarin cewa tun bayan fitar sanarwar rasuwar Alhaji Abbas Sanusi, al'ummar Kano da kewaye suka shiga alhinin rasuwar Galadiman Kano.

Kara karanta wannan

Yadda rasuwar Galadiman Kano ta tattaro kan 'yan jam'iyyar APC, NNPP

Mutane da yawa sun girgiza da wannan mutuwa kasancewar Alhaji Abbas Sanusi ya dade da rawani, tun lokacin mulkin dan uwansa, Sarki Muhammadu Sanusi I.

Tun kafin zamansa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya taba rike mukamin sarkin dawakin tsakar gida, hakimin Ungogo a 1959, da Dan Iyan Kano a 1962.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel