Yadda Rasuwar Galadiman Kano ta Tattaro kan 'Yan Jam'iyyar APC da NNPP
- Wasu daga cikin mazauna Kano sun bayyana jin daɗinsu kan yadda aka gudanar da jana’izar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi
- Duk da jimamin da ake ciki na rasuwar babban basaraken, ana fatan za a ci gaba da samun haɗin kai tsakanin jagororin jihar
- Wannan fata na zuwa bayan fitowar bidiyo da hotunan Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – A safiyar Larabar nan aka yi jana’izar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda ya koma ga Mahaliccinsa a ranar Talata yana da shekaru 92.
Sai dai, duk da jimamin rasuwar da ake ciki, yadda aka gudanar da jana’izar ta fi daukar hankalin jama’ar Kano, musamman saboda rikicin masarauta da ke kara kamari a jihar.

Kara karanta wannan
"An yi rashi," Shugaba Tinubu ya yi magana da Allah ya karɓi rayuwar Galadiman Kano

Asali: Facebook
Bidiyon da Kwankwasiyya NNPP ta wallafa a Facebook ya nuna yadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi tsayin daka wajen halartar jana’izar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayi Abbas Sanusi mahaifi ne ga shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, wanda ke gaba-gaba a adawa da nadin Mai Martaba Muhammadu Sanusi II a jihar.
Gwamna ya halarci jana’izar Galadiman Kano
A bidyon da Jikan Oga ya wallafa a Facebook, an hango yadda gwamnan ke kokarin tsawatar wa masu tururuwar zuwa wurin Abdullahi Abbas a makabarta, kila saboda yawan jama’a da ke wurin.

Asali: Facebook
Jim kadan bayan birne marigayin, an hango gwamnan Kano ya gaggauta miƙa hannu domin musabaha da Abdullahi Abbas, yayin da ake cikin alhinin rasuwar dattijo a masarauta.
Da Abbas da Mai girma gwamna duk su na zaune ne a karamar hukumar Gwale kuma bangarorinsu su na yaki da juna a siyasa.
Yadda jama’a suka yabi gwamnatin Kano
Kanawa da wasu daga cikin masu bibiyar shafukan zumunta, musamman Facebook, sun yabi gwamna Abba Kabir Yusuf da shugaban APC, Abdullahi Abbas, kan yadda aka gudanar da jana’iza a Kano.
Wasu daga cikin mabiya NNPP Kwankwasiyya sun rika neman gafara ga duk wanda suka saba wa saboda bambancin siyasa da rikicin masarauta.
Mustapha Sa'id Idris ya ce:
"Allah ya kara hada kansu."
Nura A. Buba ya wallafa cewa:
"Dan sarki ya kyauta anan."
Muhammadu Halilu Aliyu Rimi ya ce:
"Dukkansu sun burgeni sosai."
Matawallen Bornawa ya wallafa cewa:
"Wallahi, na jidadin hakan sosai. Allah yasa hakan ke hadakan al’ummar Kano."
Comrd Jameel Dan-Madina ya ce:
"Wannan shi yasa muke kara gayawa muku ‘Kwankwasawa’ cewa siyasa ba gaba ba ce. Mu rage akidar siyasa ta banza, mu hade kanmu, mu bar gaba. Su manyanmu duk kansu a hade yake."
Mohammed Abubakar ya ce:

Kara karanta wannan
Abin da Buhari ya ce bayan rasuwar dattijo, Galadiman Kano, ya fadi giɓin da ya bari
"Ku kuke wahalar da kanku, su kuma kansu a hade yake. Harkar siyasa kamar wasan kwallo ne, in ana buga wasa kowa gidansa ya sani, in an koma bayan fage kuma kansu a hade yake."
Abdurrahman Shehu ya wallafa cewa:
"Balaraben kuma Musulmin gwamna kenan! Aky. Zuciyarsa a wanke take."
AbdulRazak Sa'id Baba ya ce:
"A yi siyasa amma cikin hankali da aiki da ilimi. Yanzu kallon wannan bidiyon da nayi, abubuwa da dama sun zo cikin raina. Allah yasa mu dace."
Ana haka ne sai fitaccen 'dan jaridar nan, Ja'afar Ja'afar ya yi wani rubutu a dandalin Facebook game da mutuwar basaraken.
Malam Ja'afar ya ba da shawarar cewa a yi amfani da wannan dama ta ta'aziyya domin kawo karshen rikicin sarautar Kano.
Galadiman Kano ya rasu
A wani labarin, mun wallafa cewa an shiga cikin wani yanayi na jimami, bayan rasuwar daya daga cikin manyan dattawan masarautar Kano, Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.
Abbas Sanusi, wanda shi ne mafi girma a cikin majalisar sarakunan Kano ya rasu ya na da shekaru 92, kuma ya rayu cikin hidima da sadaukarwa ga masarautar da al’ummar jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng