'Yan Najeriya Sun Dura kan Tinubu yayin da Ya Shilla Zuwa Paris
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi tafiya zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa a ranar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025
- Fadar shugaban Najeriya ta ce Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai je birnin Paris ne domin yin ƴar gajeriyar ziyarar aiki ta kwanaki 14
- Ƴan Najeriya sun yi martani bayan samun labarin cewa Shugaba Tinubu zai sake tafiya zuwa ƙasar waje watanni da dawowarsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar birnin Abuja domin zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa.
Shugaba Bola Tinubu zai yi tafiyar ne a ranar Laraba, 2 ga watan Afirilun 2025 domin gudanar da taƙaitacciyar ziyarar aiki ta kwanaki 14.

Asali: Twitter
Hadimin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan a shafinsa na X
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Bola Tinubu zai yi a Paris
A cikin sanarwar, Bayo Onanuga ya bayyana cewa Tinubu zai yi amfani da lokacin wajen yin waiwaye kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu.
Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu zai tantance manya manyan matakan da aka ɗauka a gwamnatinsa, domin ya samu damar sanin matakin da zai ɗauka a gaba.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu zai ci gaba da kula da harkokin gwamnati tare da tattaunawa da tawagarsa duk da cewa ba ya cikin ƙasar.
Ƴan Najeriya sun yi martani
Ƴan Najeriya da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan tafiyar da shugaban ƙasan zai yi zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa.
Wasu daga ciki sun yi masa fatan yin tafiyarsa cikin nasara yayin da wasu suka caccake shi kan yawan tafiye-tafiyen da yake yi.
@joejonahni:
"Yana son duba yadda ya tafiyar da Najeriya daga Faransa. Ya kamata ya je Benue, Jos, Yobe da sauran jihohin da mutane ba za su iya fita daga gidajensu ba saboda rashin tsaro, domin a nan ne za a samu ainihin bayanai kan salon mulkinsa."

Kara karanta wannan
Ana jimamin kisan 'yan Arewa, Tinubu zai shilla zuwa kasar waje, zai shafe mako 2
@omoktp:
"Faransa ma da ba ta yi masa murnar zagayowar ranar haihuwa ba 🤣🤣🤣🤣"
@uzochukwuKing1:
"Yana son ya je cajin baturinsa."
@Gdokuboye:
"Ya kamata ya miƙa mulki ga Shettima kawai, don ko da wani abu ya faru."
@areeyol:
"Allah Ya kiyaye tafiyarka, shugaban ƙasa! Allah Ya kai ka lafiya Ya dawo da kai cikin loshin lafiya domin ka cigaba da aikin gyaran ƙasa da kake yi a yanzu. Komai zai yi kyau."
@kaball32:
"Batirin Baba ya kusa ƙarewa."
@felixobioma87:
"Shin yana da ofis a Faransa ne? Me yake zuwa yi kullum? Sau nawa ya je can cikin shekaru biyu?"
@Lilymonie:
"Ku dai ce mana batirinsa ya kusa ƙarewa 😂😂😂"
@geralduc112:
"😂😂😂😂🤣🤣🤣 Ba wai tafiyar aiki ba ce, tafiyar rawa ce. Suna tunanin mu duk wawaye ne kamar su."
@davidodiri1892:
"Yanzu lokaci ne na cajin batirinsa kuma. Meyasa dole sai Faransa kullum. Meyasa ba zai je Sweden, Brazil da sauransu ba, ko a Faransa ne kaɗai ake jin daɗi?"

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi dalilin da ya sa ya ki daukar shawara, ya nada mai sukarsa minista
Peter Obi ya caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya caccaki manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Peter Obi ya bayyana cewa idan da shi ne shugaban ƙasa, da ya kawo gagarumin sauyi wajen bunƙasa tattalin arziƙi a cikin shekara biyu kacal.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng