Ojulari: Muhimman Abubuwa da Ya Kamata Ku Sani game da Sabon Shugaban NNPCL
- Shugaba Bola Tinubu ya nada Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin NNPC bayan sauke Mele Kolo Kyari
- An sauke Kyari ne a mukaminsa bayan shafe kusan shekaru shida yana jagorantar kamfanin tun lokacin Muhammadu Buhari
- Sabon shugaban NNPCL, Bayo Ojulari ya fara aiki a Elf Aquitaine, sannan ya kamfanin Shell a 1991, inda ya zama Manajan Daraktan Shell Nigeria
- Ya yi aiki a fannoni daban-daban kamar injiniyan sarrafa mai, tsara dabaru, bunkasa filayen mai, da kuma sarrafa kadarori
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL).
Nadinsa ya biyo bayan sauke Mele Kyari daga mukaminsa bayan shafe shekaru kusan shida yana jagorantar kamfanin.

Asali: Facebook
Tinubu ya yi sababbin nade-nade a NNPCL
Wannan na cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba Shugaba Tinubu shawara ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 2 ga Afrilun shekarar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya sauya Mele Kyari daga shugabancin NNPCL tare da maye gurbinsa da Injiniya Bashir Bayo Ojulari.
Hakan ya sanya ƴan Najeriya bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan wannan sauyin shugabancin da shugaba Bola Tinubu ya yi duba da tsare-tsaren kamfanin a baya.
Fadar shugaban kasa ta kuma sanar da nadin wasu mambobi shida a kwamitin NNPCL, wadanda za su wakilci shiyyoyin siyasa guda shida na Najeriya a matsayin daraktoci marasa zartarwa.
Ga jerin sunayensu da kuma shiyyoyinsu:
Bello Rabiu - Arewa maso Yamma
Yusuf Usman - Arewa maso Gabas
Babs Omotowa - Arewa ta Tsakiya
Austin Avuru - Kudu maso Kudu
David Ige - Kudu maso Yamma
Henry Obih - Kudu maso Gabas.
NNPCL kamfani ne na kasa da ke kula da albarkatun man fetur na Najeriya domin inganta bangaren samar da mai, cewar rahoton Punch.
A karkashin mulkin Muhammadu Buhari, NNPC ya zama kamfani mai zaman kansa kuma ana shirin jera hannayensa a kasuwar hada-hadar jari.
Legit Hausa ta duba wasu bayanai kan Ojulari:
1. Mahaifar sabon shugaban NNPCL, Bayo Ojulari
Ba kamar yadda wasu ke zargi ba tun farko da cewa sabon shugaban NNPCL ta fito ne daga yankin Kudu maso Yamma watau bangaren Yarbawa.
An haifi Bayo Ojulari ne a jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya wanda ya kasance daga kabilar Yarbawa.
2. Karatun sabon shugaban NNPCL
Sabon shugaban kamfanin NNPCL ya kammala karatun injiniyanji a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna.

Asali: Getty Images
3. Muƙaman da ya riƙe kafin shugabancin NNPCL
Kafin nadinsa, Ojulari ya yi aiki da shahararren kamfanin Renaissance Africa Energy Company.
Kamfaninsa ya jagoranci hadakar kamfanonin man fetur na gida wajen siyan hannun jari a Shell Petroleum Development Company of Nigeria (SPDC) da darajarsu ta kai $2.4bn.
4. Farkon fara aiki a rayuwar Ojulari
Bayo Ojulari ya fara aiki a Elf Aquitaine a matsayin injiniyan sarrafa mai na farko a Najeriya.
Daga baya ya shiga kamfanin Shell a shekarar 1991 a matsayin fasihin samar da mai da inganta ta.

Asali: Twitter
5. Zama babban darakta a kamfanin Shell
Ojulari ya ci gaba da aiki a Shell har ya zama babban daraktan Shell Nigeria Exploration and Production Company (SNEPCO), Hakanan, ya yi aiki a Nahiyar Turai da Gabas ta Tsakiya.
Har ila yau, ya yi aiki a fannoni daban-daban kamar injiniyan sarrafa mai, tsara dabaru, bunkasa filayen mai, da kuma sarrafa kadarori.
6. Muƙamai a kungiyoyin injiniyoyi

Kara karanta wannan
Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPCL
Rahotanni sun tabbatar da cewa sabon shugaban NNPCL, Ojulari ya rike mukamai a kungiyoyin injiniyoyi wanda ya ba da gagarumar gudunmawa.
Hakan ya ba sabon shugaban NNPCL din karin kwarewa a fannoni da dama domin gudanar da aikinsa ba tare da matsala ba.
Martanin ƴan Najeriya bayan sauke Mele Kyari
Idan ba ku manta ba, mun ba ku labarin cewa ƴan Najeriya da dama sun yi martani bayan sauke shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari da Bola Tinubu ya yi.
Ƴan kasar sun bayyana mabambantan ra'ayoyi game da matakin shugaban Najeriya inda wasu ke cewa Allah raka taki gona yayin da wasu ke yabon tsarin Kyari.
Hakan ya biyo bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauyin shugabanci a kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) a ranar Laraba, 2 ga watan Maris 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng