Ana Jimamin Kisan 'Yan Arewa, Tinubu Zai Shilla zuwa Kasar Waje, Zai Shafe Mako 2
- Shugaba Bola Tinubu zai tafi Paris, don wata gajeriyar ziyarar aiki, inda zai duba nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun daga 2023 zuwa 2025
- Haka nan zai yi amfani da wannan lokaci wajen tantance manufofinsa kuma tsara wasu dabarun ayyuka gabanin cika shekaru biyu a mulki
- Fadar shugaban kasa ta ce duk da yana kasar waje, Tinubu zai ci gaba da kula da harkokin gwamnati, sannan zai dawo gida cikin makonni biyu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Fadar shugaban kasa, ta sanar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi zuwa birnin Paris na kasar Faransa, a yau Laraba.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, ya ce Tinubu zai je Paris domin wata gajeriyar ziyarar aiki.

Asali: Twitter
Tinubu zai shilla zuwa birnin Paris, Faransa
A sanarwar da Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, fadar shugaban kasar ta ce Tinubu zai waiwayi nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan hawansa mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kuma ce Tinubu zan tantance manya manyan ci gaban da aka samu a gwamnatinsa, domin sanin matakan da ya kamata a ya dauka a gaba.
Sanarwar ta ce:
"Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi zuwa birnin Paris, a Faransa, a yau don wata gajeriyar ziyarar aiki.
"A yayin ziyarar, shugaban kasa zai duba nasarorin da gwamnatinsa ta samu a tsakiyar wa’adinta da kuma tantance muhimman ci gaban da aka samu."
Aikin da Tinubu zai yi yayin ziyarar Faransa
Haka nan zai yi amfani da wannan lokaci wajen nazarin cigaban da aka samu a garambawul da ya ke yi, da kuma tsara dabarun aiki gabanin cika shekaru biyu a mulki.

Kara karanta wannan
A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas
Fadar shugaban kasar na ganin cewa ziyarar makonni biyun zai taimakawa Tinubu wajen sake daura damara da hanzarta aiwatar da manyan shirye-shiryen ci gaban kasa a shekara mai zuwa.
Bayo Onanuga ya ce:
Wannan lokaci na nazari zai taimaka wajen zurfafa gyare-gyaren da ake yi da kuma hanzarta manyan shirye-shiryen ci gaban kasa a shekara mai zuwa."
Sanarwar ta jaddada cewa cigaban da ake samu ta fuskar tattalin arziki kwanan nan alama ce da ke tabbatar da cewa manufofin shugaban kasar na haifar da da mai ido.
"Ana samun nasarori a tattalin arziki" - Onanuga

Asali: Twitter
A cewar sanarwar, nasarorin tattalin sun hada da karin ajiyar kudin waje zuwa dala biliyan 23.11 kamar yadda babban bankin Najeriya ya sanar.
"Ci gaban tattalin arzikin da aka samu kwanan nan na kara tabbatar da fa'idar manufofin shugaban kasa, kamar yadda Babban Bankin Najeriya ya sanar da karin kudaden ajiyar waje zuwa dala biliyan $23.11; alamar tasirin gyare-gyaren da aka aiwatar tun daga 2023, lokacin da kudaden ajiyar waje suka kasance dala biliyan $3.99."
- Bayo Onanuga.
Duk da cewa ba ya cikin kasar, sanarwar ta ce Shugaba Tinubu zai ci gaba da kula da harkokin gwamnati tare da tattaunawa da tawagarsa.
Fadar shugaban kasar ta sanar da cewa Bola Tinubu zai dawo Najeriya nan da kimanin makonni biyu.
Tinubu ya fara aikin da ya kai shi Faransa
A wani laarin, Legit Hausa ta rahoto cewa a ranar 28 ga Nuwambar 2024, Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci Faransa, inda ya samu rakiyar uwargidar shugaban kasa, Oluremi Tinubu.
A wannan ziyarar, Tinubu da shugaban Faransa, sun halarci wani zama da ‘yan kasuwar Faransa da Najeriya, da kuma kamfanoni masu zaman kansu, inda aka tattauna hanyar bunkasa tattalin arziki.
Asali: Legit.ng