Baban Chinedu na Fuskantar Barazana bayan Fara Wa'azi, Ya Daina Kwana a Gida

Baban Chinedu na Fuskantar Barazana bayan Fara Wa'azi, Ya Daina Kwana a Gida

  • Baban Chinedu ya ce yana fuskantar barazana tun bayan da ya fara wa’azin kare Musulunci da kalubalantar Kiristoci
  • Ya bayyana cewa har coci ya je domin gudanar da da’awa, amma yana fuskantar matsin lamba daga wasu makiya addini
  • Duk da barazanar da ake masa, Baban Chinedu ya ce ya bar komai a hannun Allah kuma zai ci gaba da wa’azin da ya fara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Baban Chinedu ya bayyana cewa yana fuskantar barazana daga wasu mutane tun bayan da ya fara wa’azin kare addinin Musulunci da kuma kalubalantar Kiristoci.

Ya ce yanzu haka ba zai iya bayyana wajen da yake ba saboda dalilan tsaro, amma dai yana cigaba da gudanar da wa’azinsa.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Direba ya fadi ainihin yadda aka kashe 'yan Arewa a jihar Edo

Baban Chinedu
Baban Chinedu ya ce yana fuskantar barazana. Hoto: Baban Chinedu
Asali: Facebook

Legit ta gano maganganun da Baban Chinedu ya yi ne a cikin wani bidiyo da Nagudu TV ya wallafa a YouTube.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baban Chinedu ya bayyana cewa ya hakura da komai kuma ya mayar da hankali kacokan wajen kare addinin Musulunci, yana mai cewa yana rokon Allah ya tabbatar da shi a cikinta.

Baban Chinedu: "Ba zan bayyana inda na ke ba"

A yayin da mutane da dama suka lura da shiru daga gare shi a kwanakin nan, Baban Chinedu ya ce yana cigaba da wa’azi amma yana kauce wa barazanar da ake masa.

"Ba zan bayyana wajen da nake ba saboda matsalolin tsaro,"

- Baban Chinedu

Ya ce tun da ya fara wannan da’awa, akwai wasu da suka daina yi masa magana, har da wasu daga cikin iyayen gidansa da suka nesanta kansu daga gare shi.

Baban Chinedu ya ce:

"Wallahi ba na iya kwana a gida na da ke Abuja. Ana min barazana ta waya, ana cewa na zagi Yesu. Akwai Fasto da yake min barazana."

Kara karanta wannan

'An ba ni cin hancin Naira biliyan 5 domin tsige Fubara,' Ehie ya yi zazzaga

Sheikh Mabera ya karfafi Baban Chinedu

Duk da barazanar da yake fuskanta, Baban Chinedu ya ce ya tattauna da malamin addinin Musulunci, Sheikh Hussaini Yusuf Mabera, wanda ya karfafa shi kan cigaba da wa’azinsa.

Malamin ya shawarce shi da ya jajirce a kan aikin da ya fara, domin aikin da'awa kamar mai lura da maras lafiya ne.

Baban Chinedu
Asadusunnah ya yabi salon wa'azin Baban Chinedu. Hoto:Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah|Baban Chinedu
Asali: Facebook

Baban Chinedu ya ce yana da yakinin cewa akwai matasa da za su cigaba da kare addinin Allah ko da kuwa an kashe shi.

"Ina ganin yadda wasu ke kokarin dakatar da wannan aiki, amma ina tabbatar muku cewa ko da an kashe ni, akwai yara da matasan da za su cigaba da kare addinin Allah."

Baban Chinedu ya ce Allah ne ke taimakonsa

Bayanin Baban Chinedu ya nuna cewa duk da matsin lamba da barazana da yake fuskanta, yana jin dadi kan yadda yake kare Musulunci.

Kara karanta wannan

Iyalan Hausawan da aka kashe a Edo sun yi magana cikin ban tausayi

Ya ce ba ya yin hakan don neman suna ko daukaka, sai dai ma yana ganin cewa addini ne ya yi masa gata.

A cewarsa:

"Ba karfina ba ne, ba iyawa ta ba ne, addini ne ya min gata."

Ya kuma bukaci a daina nuna kyama ga masana’antar Kannywood, yana mai cewa akwai mutanen kirki da za su iya bayar da gudunmawa sosai a harkar addini da abubuwan alheri.

Baban Chinedu ya kuma nemi afuwa ga duk wanda ya taba bata wa rai, yana mai cewa a yanzu ba ya neman fada da kowa kuma yana kokarin taka tsantsan a rayuwarsa.

Babban abin da ya fi daukar hankali shi ne, yadda ya kasance dan wasan kwaikwayo da ya yi fice a Arewacin Najeriya sannan ya rikide zuwa mai da'awar addinin Islama.

Malaman addinin Kirista sun nuna rashin jin dadinsu da kalamansa, kuma sun nuna bai fahimci yadda addinin nasu yake ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya mayar da hankali kan tausaya wa talaka a sakon barka da sallah

Sheikh Jingir ya yi wa Dan Bello raddi

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Izala mai hedkwata a Jos, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya yi wa Dan Bello raddi.

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya karyata zargin da Dan Bello ya yi wa Sheikh Abdullahi Bala Lau na cewa ya karkatar da kudin kwangila.

Jingir ya yi wannan bayanin duk da sabani da ake yawan samu tsakanin Izala ta Jos da Kaduna, lamarin da ya ba mutane da yawa mamakin.

Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng