A Karon Farko, Gwamna Fubara Ya Fadi Halin da Ya Shiga bayan Dokar Ta Baci a Ribas

A Karon Farko, Gwamna Fubara Ya Fadi Halin da Ya Shiga bayan Dokar Ta Baci a Ribas

  • Dakataccen gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya bayyana yadda dokar ta bacin da shugaban kasa, Bola Tinubu ya sa a jiharsa ta jefa shi
  • A ranar 18 ga watan Maris ne gwamnatin tarayya ta yanke shawarar kakaba dokar ta baci tare da dakatar da zababbiyar gwamnatin Ribas
  • Amma dakataccen gwamnan ya bayyana cewa a a halin yanzu, ya fawwalawa Ubangiji komai domin kawo karshen matsalar da Ribas ta fada
  • Fubara ya yi kira ga magoya bayansa da su guji tayar da tarzoma, ya na mai cewa haƙuri da juriya za su taimaka wajen samun nasara a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ribas – Dakataccen gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce ya na jin ba daɗi da kuma damuwa game da ayyana dokar ta-baci a jihar.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

A ranar 18 ga watan Maris, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Ribas, ya na mai cewa rikicin siyasa da ya yi tsawo a jihar ne ya haddasa hakan.

Fubara
Gwamnan Ribas ya shiga damuwa kan dokar ta baci a Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Instagram

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Tinubu ya kuma dakatar da Fubara daga matsayin gwamna, tare da mataimakiyarsa, Ngozi Odu da 'yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasa ya kuma naɗa Ibok-Ete Ibas, tsohon hafsan sojin ruwa, a matsayin mai rikon jihar na wucin gadi.

'Ina jin babu dadi,' Dakataccen gwamnan Ribas

The Guardian ta wallafa cewa yayin ganawa da wasu shugabannin Musulmi da suka kai masa ziyara a gidansa da ke Fatakwals, Fubara ya ce shi da tawagarsa suna shiga damuwa.

Ya ce:

“Mu a matsayinmu na mutane, muna iya jin damuwa da halin da muke ciki.
Tinubu
Shugaban kasa, Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Ya kuma jaddada cewa:

“Wannan lokaci ne na soyayya, kara dankon zumunci da sadaukarwa. Kun zo don damuwa da damuwarmu, kuma wannan babban abu ne da kuka yi ta hanyar addu’o’inku.”

Kara karanta wannan

Minista ya fadi lokacin da Tinubu zai janye dokar ta baci a Ribas

“A matsayinmu na Kiristoci, mun yarda cewa komai yana faruwa da dalili, kuma ina da ƙwarin gwiwa cewa wannan halin da muke ciki zai kai mu ga wata kyakkyawar makoma.”

'Na bar lamarin Ribas ga Ubangiji,' Fubara

Dakataccen gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa ya bar dukkan al’amuran rikicin jihar a hannun Ubangiji domin kawo mafita.

Ya ce:

“Ko me muke gani, dole ne mu kasance masu juriya. A cikin komai, muna yabawa Ubangiji. Ina da yaƙinin cewa, a ƙarshe, za mu fi ƙarfin halin da muke yanzu.”

Fubara ya roƙi magoya bayansa da su kasance masu hakuri kuma su guji tayar da zaune tsaye, yana mai cewa dole ne guji sharrin waɗanda ke ruruta wutar tashin hankali a Ribas.

Rikicin jihar Ribas ya dawo sabo

A baya, mun wallafa cewa kungiyar Matasan Ijaw ta duniya (IYC) ta yi tir da matakin da mai mulkin rikon kwarya na Ribas, Ibok-Ete Ibas, ya dauka na sauke mukarraban gwamnati a jihar.

Sauke jami’an da Ibok-Ete Ibas ya yi ya shafi sakataren gwamnati, shugaban ma’aikata, kwamishinoni, shugabanni da membobin hukumomi, da mashawarta na musamman.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel