Bayan Sauke Mele Kyari, Tinubu Ya Yi Sababbin Nade Nade 9 a Kamfanin NNPCL
- Shugaba Bola Tinubu ya nada sababbin shugabanni a kamfanin man fetur na NNPCL, bayan sauke tsohon shugaban kamfanin, Mele Kyari
- Tinubu ya amince da nadin Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban NNPCL tare da wasu sababbin daraktoci masu wakiltar shiyyoyi
- Wannan sauye-sauyen na zuwa ne yayin da kamfanin NNPCL ya dakatar da yarjejeniyar sayar da danyen mai da Naira ga matatar Dangote
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da nadin sababbin shugabanni a kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL.
Nadin ya biyo bayan tsige tsohon shugaban kamfanin, Mele Kyari, tare da wasu mambobin kamfanin, kamar yadda Legit.ng Hausa ta ruwaito.

Asali: Twitter
Bayo Onanuga, mai bai wa Tinubu shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya sanar da ci gaban a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a safiyar Laraba, 2 ga Afrilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya nada sabon shugaban NNPCL
Sanarwar ta bayyana cewa nadin ya shafi manyan daraktoci masu kula da ayyuka da kuma wadanda ba su da alhakin gudanarwa kai tsaye.
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya nada Bayo Ojulari a matsayin sabon Babban Darakta na kamfanin NNPC, domin maye gurbin Mele Kyari da aka sauke.
Haka nan, shugaban kasa ya tabbatar da nadin Adedapo Segun a matsayin mamba a kwamitin gudanarwa, wanda ya karbi mukamin babban jami’in kudi daga Umaru Isa Ajiya tun a watan Nuwamba.
Tinubu ya kuma amince da nadin Hajiya Lydia Shehu Jafiya, babbar sakatariyar ma’aikatar kudi ta tarayya, don wakiltar ma’aikatar a sabon kwamitin NNPCL. Aminu Said Ahmed kuma zai wakilci ma’aikatar albarkatun man fetur.
Sababbin daraktocin da Tinubu ya nada a NNPCL
Fadar shugaban kasa ta kuma sanar da nadin wasu mambobi shida a kwamitin NNPCL, wadanda za su wakilci shiyyoyin siyasa guda shida na Najeriya a matsayin daraktoci marasa zartarwa.
Ga sunayensu da shiyyoyinsu:
- Bello Rabiu - Arewa maso Yamma
- Yusuf Usman - Arewa maso Gabas
- Babs Omotowa - Arewa ta Tsakiya
- Austin Avuru - Kudu maso Kudu
- David Ige - Kudu maso Yamma
- Henry Obih - Kudu maso Gabas
NNPCL ta dakatar da sayar da danyen mai da Naira
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake samun sabani tsakanin NNPCL da matatar man Dangote, mata mai zaman kanta, mafi girma a Najeriya.
NNPCL ta amince a baya da sayar da danyen mai ga matatar Dangote da Naira, da nufin daidaita darajar Naira da rage farashin mai a kasar.
Sai dai yarjejeniyar ta kare tun wata daya da ya gabata, kuma bangarorin biyu ba su sabunta kwangilar ba, lamarin da ya haddasa hauhawar farashin mai.
A halin yanzu, dillalan mai sun fara shigo da man fetur daga waje maimakon saye daga Dangote, wanda shi ma ya fara sayar da mai da daloli bayan kawo karshen yarjejeniyar.

Kara karanta wannan
Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPCL
'Yan Najeriya sun yi martani kan sauke Kyari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya sun yi martani kan sauyin shugabancin da shugaba Bola Tinubu ya yi a kamfanin man Najeriya, watau NNPCL.
Wani Oladipo E.I ya yi tambaya ko yaushe ne za a kama Mele Kyari kamar yadda aka kama Godwin Emefiele? Yayin da wasu ke zargin Tinubu da Yarbantar da kasar.
Asali: Legit.ng