Uba Sani Ya Je gaban Sarkin Zazzau, Ya Yi Gargadi ga Masu Sarautun Gargajiya

Uba Sani Ya Je gaban Sarkin Zazzau, Ya Yi Gargadi ga Masu Sarautun Gargajiya

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ja kunnen masu riƙe da sarautun gargajiya kan danne haƙƙin mutanen da suke wakilta
  • Sanata Uba Sani ya gargaɗi masu riƙe da sarautun gargajiyar kan su guji ƙwace filayen mutane ba bisa ƙa'ida ba a jihar Kaduna
  • Hakazalika, Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya gargaɗi hakimai da dagantai kan zaluntar mutanen da ke ƙarƙashinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi sabon gargaɗi ga masu riƙe da sarautun gargajiya.

Gwamna Uba Sani ya gargaɗi shugabannin gargajiya da su guji mamayewa tare da kwace filaye ba bisa ƙa’ida ba a yankunansu.

Gwamna Uba Sani
Gwamna Uba Sani ya gargadi masu sarautun gargajiya a Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne yayin gaisuwar ƙaramar Sallah ta bana a fadar Sarkin Zazzau da ke Zaria, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: Limamai sun tsage gaskiya ga gwamnatin Tinubu kan tsadar rayuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane gargaɗi Uba Sani ya yi a Kaduna?

Uba Sani ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna ta na samun ƙorafe-ƙorafe game da ƙwace filaye ba bisa ƙa’ida ba daga dagatai da masu unguwanni.

Ya jaddada cewa duk filaye mallakin gwamnati ne, don haka dole ne a bi ƙa’ida wajen samun su daga hukumomin da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Gwamnan, wanda Alhaji Muktar Shehu (Jarman Zazzau), mai ba da shawara na musamman kan harkokin masarautu, ya wakilta, ya kuma buƙaci shugabannin gargajiya da su mutunta zaman lafiya da ake samu a yankunansu da jihar gaba ɗaya.

Har ila yau, Gwamna Uba Sani ya buƙaci manoma da su koma gonakinsu saboda an samu ingantuwar tsaro a jihar.

Sarkin Zazzau ya ja kunnen hakimai da dagatai

A na sa jawabin, Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya sake nanata umarninsa ga hakimai, dagatai da masu unguwanni da su guji zaluntar jama’a.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya aika sako ga 'yan Najeriya, ya gano kuskuren da suke yi kan shugabanni

Ahmed Bamalli
Sarkin Zazzau ya gargadi hakimai da dagatai Hoto: Zazzau Emirate
Asali: Facebook

Ya kuma gargaɗe su kan haɗa baki da masu hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da ke zuwa yankunansu domin gudanar da haramtattun ayyuka.

Sarkin ya bayyana cewa kafin a ba da dama ga kowanne mai haƙar ma’adanai ya gudanar da wani aiki, dole ne a tabbatar da sahihancinsa daga hukumomin da suka dace, sannan a sanar da masarautar.

Ahmed Bamalli ya yi gargaɗi ga dagatai da su guji raba filayen da ke ƙarƙashin ma’aikatar kula da gandun daji, tare da umartar su da su tsaya kawai kan filayen da suka shafi masarautu.

Gwamna Uba Sani zai ɗauki ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Uba Sani ta shirya ɗaukar sababbin ma'aikata a fannin lafiya.

Gwamnatin Sani za ta ɗauki sababbin ma'aikata 1,800 waɗanda za su yi aiki a cibiyoyin lafiya matakin farko da ke faɗin jihar.

Hakazalika gwamnatin za kuma ta inganta tare da gyara cibiyoyin lafiya a matakin farko da ke jihar domin kula da marasa lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng