Uromi: An Jibge Jami'an Tsaro a Garin da aka Hallaka Hausawa 16 a Edo

Uromi: An Jibge Jami'an Tsaro a Garin da aka Hallaka Hausawa 16 a Edo

  • Mazauna yankin Uromi na Jihar Edo, garin da aka yi wa Hausawa kisan gilla, sun fada cikin fargabar harin ramuwar gayya
  • Rahotanni sun bayyana cewa wannan fargaba ta sa aka jibge tarin jami'an tsaro, ciki har da 'yan sanda da jami'an farin kaya
  • An samu raguwar ayyuka a garin, yayin da bankuna da dama ke aiki rabi da rabi saboda shirin ko ta kwana kan ramuwar gayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo – Jami’an ‘yan sanda, sojoji da kuma sauran jami’an tsaro sun mamaye manyan hanyoyi a Uromi, hedkwatar Karamar Hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo.

Uromi, garin da aka yi wa matafiya 16 daga Arewacin Najeriya kisan gilla a ranar Alhamis din da ta gabata, ya jawo fushi da Allah wadai, musamman daga 'yan Arewa.

Kara karanta wannan

Duk da kwararan matakai a Kogi, masoyan Natasha sun yi mata tarbar girma a jirgi

Yan sanda
Ana fargabar ramuwar gayya a Uromi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an gano cewa an jibge jami’an tsaron ne domin hana ramuwar gayya, domin kuwa mazauna yankin sun nuna damuwa kan yiwuwar hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce mazauna yankin suna guje wa tattauna al'amarin saboda fargabar kama su, bayan da aka cafke akalla mutane 14 da ake zargi da hannu a lamarin.

Jami’an tsaro sun mamaye titunan Uromi

Baya ga jibge ‘yan sanda, an kuma ga motocin sojoji suna sintiri a wuraren da ke kusa da babbar hanya da wasu wuraren da ake ganin akwai yiwuwar tada zaune tsaye.

Ana ganin an dauki matakin ne domin sa ido kan zirga-zirgar jama’a da tabbatar da doka da oda da dakile duk wani yunkurin ramuwar gayya.

Samar da jami’an tsaron fararen kaya a yankin ne ya kara tsananta fargabar mazauna Uromi kan sababbin fuska da ke shigowa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Edo, Moses Yamu, ya bayyana cewa helkwatar rundunar ‘yan sanda ce ta karbi ragamar binciken lamarin.

Kara karanta wannan

"Mutane sun yi takansu": Halin da ake ciki a garin da aka kashe ƴan Arewa 16 a Edo

Ya kara da bayyana cewa rundunar ta jibge karin jami’an tsaro domin hana tada zaune tsaye da kare rayukan al'umma.

Yan sanda
An jibge jami'an tsaro a Uromi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yamu ya ce:

“Helkwatar ‘yan sanda ce ke da alhakin binciken, don haka ba zan iya cewa ko an samu ci gaba ko a’a ba. Amma dai jami’anmu na nan don tabbatar da cewa ba a samu tashin hankali ba.”

An samu raguwar zirga-zirga a Uromi

Rahotanni sun nuna cewa wasu bankuna sun yi aiki ne a taƙaice a ranar Juma’a bayan afkuwar lamarin, musamman bayan da labari ya yadu cewa akwai yiwuwar ramuwar gayya.

Wani ma’aikacin banki da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

“Dole mu yi taka-tsantsan a yau, domin ranar Juma’a mun rufe banki da wuri bayan samun labari cewa ana fargabar ramuwar gayya.
“Kuna dai sane cewa idan irin haka ta faru, kadarorin gwamnati ne ke zama na farko wajen fuskantar hare-hare, don haka wasu bankuna sun bude kawai a taƙaice, wasu kuma ba su bude ba kwata-kwata.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 4 na bibiyar hakkin Hausawan da aka kashe a jihar Edo," HRN

“A ranar Laraba, za mu ci gaba da lura da halin da ake ciki, idan kuma muka fahimci alamun tashin hankali, za mu rufe. Amma dai za mu ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro domin sanin halin da ake ciki.”

Uromi: Ana son a bi hakkin Hausawa

A baya, mun wallafa cewa gamayyar kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa reshen Najeriya, ta yi Allah wadai da kisan matafiyan da su ke wuce wa ta garin Uromi a jihar Edo.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi wa matafiyan kisan wulakanci, lamarin da ya jawo shugaban gamayyar, Kwamred AA Ayagi ya nemi a kwato hakkin mutanen da aka kashe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng