"Ku Sha Shagalin Sallah": Gwamna Abba Ya Tuna da Mutanen da Ke Ɗaure a Jihar Kano

"Ku Sha Shagalin Sallah": Gwamna Abba Ya Tuna da Mutanen da Ke Ɗaure a Jihar Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa mutanen da aka ɗaure a gidajen gyaran halin Kano kyautar tulin kayan abinci da shanu 12
  • Abba ya ba da wannan tallafin ne domin taimaka wa fursunoni su gudanar da shagalin sallah cikin farin ciki da walwala
  • Shugaban NCoS na Kano ya yaba wa Gwamna Abba bisa wannan tallafi, ya na mai cewa na ƙara masu ƙwarin guiwa su ji ana sane da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - A kokarinsa na inganta jin daɗin rayuwar ɗaurarru a Kano, Gwamnan Abba Kabir Yusuf, ya bayar da kyautar abinci da shanu 12 ga fursunonin gidajen gyaran hali a jihar.

Gwamna Abba ya ba da wannan tallafin ne domin taimaka wa fursunonin su gudanar da bukukuwan Eid-el-Fitr watau karamar sallah cikin farin ciki da jin daɗi.

Kara karanta wannan

Biyan diyya da alkawuran da Abba Kabir ya yi kan Hausawan da aka kashe a Edo

Gwamna Abba Kabir.
Gwamna Abba ya bai wa fursunoni kayan abinci da shanu don bukukuwan Sallah Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Leadership ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS), reshen Kano, CSC Musbahu Kofar-Nasarawa, ya fitar a jiya a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya ba fursunoni tallafi

A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya miƙa kayan ne ta hannun shugabar kwamitin harkokin jin ƙai na jihar Kano, Hajiya Azumi Namadi-Bebeji.

Kayan da aka bayar sun haɗa da shanu 12, buhunan shinkafa, man girki, albasa da kayan ƙamshi, domin tabbatar da cewa fursunonin sun sami abinci mai kyau a lokacin bukukuwan Sallah.

Da take bayani yayin miƙa tallafin, Hajiya Azumi Namadi-Bebeji ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatin Abba na kula da jin daɗin fursunoni da sauran raunanan mutane a cikin al’umma.

Tallafin zai inganta rayuwar fursunonin Kano

“Wannan yunƙuri yana da matuƙar muhimmanci wajen inganta kula da gidajen gyaran hali tare da tallafa wa fursunoni domin gyara da inganta rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi matsayarsa kan umarnin hana hawan Sallah a Kano

"Idan ana kula da su yadda ya dace, hakan zai taimaka wajen sauya halayensu da kyautata zamantakewa a cikin su.”

- Inji Hajiya Azumi.

Ta yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan taimako da goyon baya da take ci gaba da bai wa fursunoni, tana mai cewa hakan ya na nuni da irin kulawar da gwamnan ke nunawa ga dukkan al’ummar Kano, ciki har da fursunoni.

Kwamandan NCoS ya yabawa Gwamna Abba

Da yake karɓar kayan a madadin fursunonin, kwamandan NCoS na Kano, Mista Ado Inuwa, ya gode wa gwamnatin jihar bisa wannan tallafi.

Ya jinjina wa gwamnan bisa ƙoƙarinsa na tallafa wa fursunoni, ya na mai cewa hakan ya na sa su jin kansu a matsayin wani ɓangare na al’umma.

Ya kara da cewa irin wannan taimako yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da kyakkyawar rayuwa ga fursunoni, tare da basu damar yin rayuwa mai tsafta da cike da kyakkyawan fata.

Kara karanta wannan

"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

Kwamishina ya miƙawa Abba takardar murabus

A wani labarin, kun ji cewa kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya ajiye mukaminsa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din kwamishinan watanni uku kacal bayan naɗa shi a sabuwar ma'aikatar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng