Sauki Zai Samu: An Bayyana Lokacin da Farashin Litar Fetur Zai Sauka Ƙasa da N750
- NIPSS ta tabbatar da cewa farashin man fetur zai sauka kafin ƙarshen shekarar 2025 yayin da matatun Najeriya suka fara aiki gadan gadan
- Shugaban NIPSS, Ayo Omotayo, ya ce idan matatun Dangote, Fatakwal da sauransu suka kai ƙololuwar aikinsu, fetur zai dawo ƙasa da N750
- Manajan gidan man Shade da ke Kaduna, Alhaji Mubarak Aliyu, ya yi tsokaci kan sauyin farashin fetur da ake samu a Najeriya da ma waje
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida Abuja - Cibiyar koyon dabaru da tsare tsare ta ƙasa (NIPSS) ta tabbatar da cewa farashin man fetur zai sauka sosai kafin ƙarshen shekarar 2025.
NIPSS ta ba da tabbacin cewa ƴan Najeriya za su sayi fetur da araha yayin da Dangote da sauran matatun man ƙasar za su kai ƙololuwar aikinsu.

Source: UGC
Amfanin fara aikin matatun mai na Najeriya
Shugaban NIPSS, Ayo Omotayo, yayin zantawa da Channels TV, ya ce za a ƙara samun saukar farashi idan sauran matatun ƙasar suka fara aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da biyan tallafin man fetur, sai muka samu matatar man Dangote ta fara aiki.
"Ita ma matatar man fetur ta garin Fatakwal na ci gaba da aiki, kusan kwanaki 110 kenan tana aiki ba tsayawa. Wannan ci gaba ne, kuma yanzu aka fara."
- Ayo Omotayo.
Lokacin da fetur zai koma ƙasa da N750
Shugaban NIPSS ya hasasho cewa farashin litar man fetur zai sauka zuwa ƙasa da N750 kafin ƙarshen shekarar nan, kuma farashin canjin kudi zai daidaita.
A cewar Ayo Omotayo:
"Mu na da yakinin cewa farashin litar man fetur zai sauka zuwa ƙasa da N750 kafin zuwa ƙarshen wannan shekarar.
"Hakazalika, farashin canjin kudi zai sauka zuwa kaso 1.3 kafin ƙarshen shekarar nan, kuma haka farashin zai ci gaba da sauka."

Kara karanta wannan
2027: SDP ta waiwayi manyan ƴan adawa, Atiku, Obi da Kwankwaso, ta mika masu buƙata 1
"Mu na fatan cewa za mu zama babbar kasa mai fitar da kayayyaki, nan ba da jimawa ba, za mu cimma wannan muradin."
'Sauki na nan zuwa' - Shugaban NIPSS

Source: Getty Images
Ayo Omotayo ya yarda cewa ana fama da matsin tattalin arziki, amma ya dage kan cewa tsare tsaren Shugaba Tinubu za su amfani ƴan Najeriya a nan gaba.
"Ci gaban da ake samu ba wani mai yawa ba ne a yanzu, amma a nan gaba, za a ga ci gaban da zai share hawayen wahalar da ƴan kasar ke fuskanta yanzu."
- Inji shugaban NIPSS.
Da ya ke kare cire tallafin man fetur, ya nuna cewa ƙasar za ta fuskanci kalubale a farko, amma daɗin da za a sha a gaba ya zarce wahalar da ake sha yanzu.
A cewar sa:
"Za a ga amfanin janye tallafin nan gaba kadan. A yanzu, gwamnati ta bullo da tsare-tsare na ba da tallafi domin rage raɗaɗi ga talaka. Dole mu gyara yadda muke kashe kuɗinmu."
Farashin fetur a Kaduna
A zantawar Legit Hausa da wani manajan gidan man Shade da ke Kaduna, Alhaji Mubarak Aliyu, ya shaida mana cewa ana samun saukin fetur a yanzu.
Alhaji Mubarak ya ce:
"Idan har matatar man Dangote za ta ci gaba da sauke farashin mai idan an samu saukar shi a duniya, to tabbas litar fetur za ta koma ƙasa da N700.
"Ana ci gaba da samun kasashen da ke hako mai, kasuwar duniya na ganin karuwar danyen mai, sannan kasashe da dama sun koma tace man su, dole farashi ya sauka.
"Mu ma a nan cikin gida, idan matatar man Kaduna, Fatakwal da sauransu suka dawo aiki, za a samu sauki. Yanzu litar mai tana tsakanin N950 har zuwa N980 a wasu wurare."
Gidajen mai sun ƙara farashin litar fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gidajen mai da dama a jihar Legas sun ƙara farashin litar fetur zuwa N930 daga N900.
An ce gidajen man sun yi ƙarin kudin ne a ranar Litinin, 31 ga watan Maris, 2025 yayin matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a kan Naira.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

