'Mu Na Zaman Makoki, Su Na Hawan Sallah,' Sarki Sanusi Ya Fusata Wasu

'Mu Na Zaman Makoki, Su Na Hawan Sallah,' Sarki Sanusi Ya Fusata Wasu

  • Wasu mazauna Kano sun nuna bacin rai kan yadda Sarki Muhammadu Sanusi II, ya gudanar da hawan Nasarawa duk da haramcin 'yan sanda
  • Wasu sun fusata da cewa duk da mutuwar wani dan bijilanti a tawagar Sarki a ranar Sallah, ba a dakatar da shagulgulan bikin ba don nuna alhini
  • Duk da suka da aka yi wa hawan, wasu sun goyi bayan Sarki Sanusi II, suna mai cewa hakan ba laifi ba ne, kuma ya zo daidai da abin da su ke so

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

JiharKanoWasu mazauna Kano sun bayyana takaicinsu kan yadda Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kai ziyara gidan gwamnati.

Ana ganin Sarki Sanusi da tawagarsa sun yi wani tattaki da ke kama da Hawan Nasarawa duk da haramcin da jami’an tsaro suka gindaya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sarkin Kano, Sanusi II ya ture umarnin 'yan sanda, ya yi Hawan Nasarawa

Sallah
Gwamna, Abba Kabir Yusuf tare da Muhammadu Sunusu II a gidan gwamnati Hoto: NNPP Kwankwasiyya
Asali: Facebook

A wani sako da NNPP Kwankwasiyya ta wallafa a shafinta na Facebook, an hango Sarkin Kano zaune kusa da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a wani bangare na bikin Sallah a gidan gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fusata kan hawan Nassarawa a Kano

Wasu daga cikin masu bibiyar shafin sun bayyana bacin ransu kan yadda Sarkin Kano ya yi tattaki zuwa gidan gwamnati.

Sun bayyana bacin ransu da zargin cewa ya bijirewa umarnin rundunar 'yan sandan Kano, kodayake ba a gan shi ko ‘yan tawagarsa a kan doki ba.

Wasu sun yi fushi da cewa duk da mutuwar wani bawan Allah, ɗan bijilanti da ke rakiyar Sarkin a ranar Sallah, ba a dakatar da shagulgulan Sallar ba.

Musa Ali Nocase ya ce:

"In ya isa ya hau doki, magani ayi zagaye kamar yadda ake yi."

Sa'id H. Sa'id ya wallafa cewa:

"An kashe ‘yan uwammu, maimakon a soke hawan Sallah don nuna alhinin mutuwar su da zaman makoki, sai kawai bukukuwanku kuke yi. Baku damu da mu ba."

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya yi magana da babbar murya kan kisan 'yan Arewa a Edo

Fatin Manta kuwa ta wallafa hoto mai dauke da Sarki Aminu Ado Bayero da Gwamna Abba Kabir Yusuf, suna murmushi, tana mai cewa:

"Lokacin amana amma yanzu, kalli Sanusi da Abba—duk cikin bakin ciki, fuska ba annuri. Aminu Ado duk ya kidime su."

Musa Yusuf Kagara ya ce:

'Naga Gwamna ba annashuwa a fuskarsa.'

An samu masu goyon bayan Sarki Sanusi II

Duk da cece-kuce da suka kan ziyarar da Sarki Muhammadu Sanusi II ya kai gidan gwamnati, wasu sun goyi bayan sa, suna mai cewa hakan ba laifi ba ne.

Sallah
Yadda aka yi bikin Sallah a gidan gwamnatin Kano Hoto: NNPP Kwankwasiyya
Asali: Facebook

Warzu Dahir Mu Azu ya ce:

"Allah ya iya muku, yaja zamaninku."

Engr Ibraheem Aspa ya rubuta:

"Ale-Aminu, sai dai ya je gidan Babba Dan Agundi yayi gaisuwa."

Jiddah Halilu ta ce:

"Ba wanda ya isa ya hana wannan hadin sai Allah SWT."

Sarki Sanusi II ya yi hawan Nasarawa

A wani labarin, kun ji cewa duk da hana gudanar da Hawan Nasarawa da rundunar ‘yan sanda ta yi saboda dalilan tsaro, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya gudanar da bikin a wani sabon salo.

A al'ada, Hawan Nasarawa yana daya daga cikin muhimman al’adun da ake gudanarwa a Kano bayan Sallah, inda Sarki da manyan hakimai ke fita a kan dawakai zuwa gidan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.