Gidajen Mai Sun Ƙara Farashin Fetur, Lita Ta Haura N900 a Wasu Sassan Najeriya
- Farashin litar fetur ya tashi daga ƙasa da N900 zuwa N930 a gidajen mai da dama a jihar Legas ranar Litinin, 31 ga watan Maris, 2025
- Wannan ƙari na zuwa ne bayan matatar Ɗangote ta dakatar da tsarin sayar da man fetur da kudin Najeriya watau Naira
- Ga dukkan alamu har yanzu matatar Ɗangote ba ta kara cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan sayen ɗanyen mai da Naira ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da.kullum
Lagos - Yayin da musulmin Najeriya ke bukukuwan ƙaramar sallah bayan kammala azumin Ramadan, gidajen mai sun kara farashin litar man fetur.
A ranar Litinin, 31 ga watan Maris, 2025, rahotanni sun nuna cewa gidajen mai da dama a jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin kasar nan sun ƙara tsadar mai.

Asali: Getty Images
Gidajen mai sun kara farashi a Legas

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi rashi: Yadda Edwin Clark da fitattun ƴan siyasa 4 suka mutu a 2025
Jaridar The Cable ta tabbatar da cewa gidan man First Royal da ke kan titin College a Ogba, Lagos, ya kara farashin kowace litar fetur daga N860 zuwa N930.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma, gidan mai na AS Sallam Petroleum da ke gaban First Royal, da kuma gidan man MRS Oil a Festac, sun bi sahu, sun kara farashin lita zuwa N930.
Sai dai, gidan man Mobil da ke tashar motar Abeokuta, kusa da titin Kwaleji a Ogba, ya kara farashin duk lita guda daga N865 zuwa N935.
Menene ya jawo ƙarin farashin man fetur?
Karin farashin fetur ya biyo bayan matakin da matatar man Dangote ta ɗauka na dakatar da sayar da man fetur a Naira.
Matatar hamshaƙin ɗan kasuwar ta ɗauki wannan mataki ne bayan gaza cimma matsaya a tattauwar gudanar da kasuwanci wadda ke ba ta damar sayen ɗanyen mai da Naira.
Tun a bara, gwamnatin tarayya da matatun mai ciki har da ta Dangote suka cimma yarjejeniya cewa za a sayar da danyen mai da man fetur a Naira.

Kara karanta wannan
Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano
Sun ɗauki wannan matakin ne domin rage yawan neman Dala a kasuwar canjin kudi da kuma hana darajar Naira ci gaba da faduwa.

Asali: UGC
Halin da ake ciki kan cinikin mai da Naira
Sai dai har yanzu bangarorin da ke cikin wannan yarjejeniya ba su cimma sabon matsaya ba, bayan yarjejeniyar farko ta kare a ranar 20 ga watan Maris, 2025.
Wannan lamarin da ya tilasta wa matatar Dangote fara siyan danyen mai daga kasuwar duniya.
A hukumance, Najeriya ta fara sayar da danyen mai da kayayyakin fetur a Naira ga matatun cikin gida a ranar 1 ga Oktoba, 2024.
Karin farashin fetur da gidajen mai suka yi na zuwa ne fiye da wata guda bayan matatar Dangote ta rage farashin fetur zuwa N825 a ranar 26 ga Fabrairu.
Hakan dai ya sauke farashin kowace litar fetur a gidajen mai to amma a yanzu, daina cinikin da Naira ya kara tashin farashin, Channels tv ta rahoto.
Fetur zai iya dawowa N500 a Najeriya
A baya, kun ji cewa masana a ɓangaren man fetur sun yi hasashen hanyar da za a bi wajen rage farashin man fetur zuwa N500 a Najeriya.
Wannan hasashe na zuwa ne bayan ƴan kasuwar fetur sun fara gasar rage farashi musamman tsakanin matatar Ɗangote da kamfanin NNPCL.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng