Fulani Sun Dauki Fansa, Sun Kona Inyamurai Kurmus a Kano? Ƴan Sanda Sun Fadi Gaskiya

Fulani Sun Dauki Fansa, Sun Kona Inyamurai Kurmus a Kano? Ƴan Sanda Sun Fadi Gaskiya

  • Rundunar ‘yan sandan Kano ta karyata jita-jitar da ke cewa an tare mota dauke da ‘yan kabilar Ibo 18 a Kano, kuma aka cinna mata wuta
  • Bincike ya nuna cewa hoton da ake yadawa na motar da aka kona, an dauke shi ne a 2023 a wani hatsari a titin Legas-Ibadan, ba a Kano ba
  • Rundunar ‘yan sandan Kano ta fara farautar masu yada jita-jitar tare da gargadin jama’a su guji yada bayanan karya da ke haddasa firgici

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rundunar ‘yan sandan Kano ta karyata jita-jitar da ke yawo a soshiyal midiya cewa an tare motar fasinja, mai dauke da Inyamurai 18 a Kano, tare da kona ta kurmus.

A cewar jita-jitar da ta yadu a karshen makon jiya, babu Inyamuri ko daya da ya tsira daga harin, tare da yada hotunan wata mota da ta kone kurmus.

Kara karanta wannan

Iyalan Hausawan da aka kashe a Edo sun yi magana cikin ban tausayi

Rundunar 'yan sandan Kano ta karyata rahoton kisan Inyamurai a Kano
'Yan sanda sun magantu da aka ce an kona mota dauke da Inyamurai 18 a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Kano: An binciko asalin hoton da ake yadawa

Sai dai, binciken HumAngle ya nuna cewa an fara yada hoton ne a Satumbar 2023, bayan wani hatsarin mota a titin Legas-Ibadan, kuma fasinjoji 18 da hatsarin ya rutsa da su sun tsira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hoton ya sake bayyana a wani rahoto na watan Janairun 2024 lokacin da mutane 19 da suka halarci biki suka rasa rayukansu a hadarin mota a yankin Kwana Maciji, karamar hukumar Pankshin, Filato.

A wata hira da jaridar TheCable a ranar Litinin, kakakin ‘yan sanda na Kano, Abdullahi Kiyawa, ya musanta cewa an kai sabon hari kan ‘yan kabilar Ibo a jihar.

“Ba mu da wata matsala irin wannan a Kano, wannan labari karya ne,” inji Kiyawa.

'Yan sandan Kano sun karyata kona Inyamurai

A wata sanarwa daban, Kiyawa ya bayyana cewa ‘yan sanda sun fara bincike don gano tushen wannan jita-jita tare da daukar matakin hukunta wadanda ke yada irin wadannan bayanai.

Kara karanta wannan

Biyan diyya da alkawuran da Abba Kabir ya yi kan Hausawan da aka kashe a Edo

Sanarwar ta bukaci jama’a da su yi watsi da wannan labari na bogi, su kuma guji yada bayanan karya da ka iya haddasa tashin hankali da firgici a al’umma.

Rundunar ta jaddada kudurinta na tabbatar da doka da oda a Kano tare da kare lafiyar kowa ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

"Mun fara bincike don gano tushen wannan labari na bogi, kuma za mu dauki matakan da suka dace don gurfanar da masu yada shi a gaban shari’a."

- Abdullahi Kiyawa.

'Yan sanda sun gargadi mutane kan yada jita-jita

Kiyawa ya gargadi masu yada jita jita
Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Haka kuma, rundunar ta bukaci jama’a da su hada kai da ‘yan sanda tare da bayar da rahoton duk wani abu da ke da alaka da yada jita-jita ko haifar da rudani.

"Muna roƙon jama'a su haɗa kai da ‘yan sanda tare da bayar da rahoto kan duk wani abin da ke haifar da shakku ko masu yada ƙarya zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Kara karanta wannan

Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano

"Muna fatan za mu yi aiki tare don tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, da tsaro a jihar Kano."

- Inji sanarwar 'yan sanda

Jita-jitar ta biyo bayan wani hari da aka kai a yankin Uromi, jihar Edo, inda aka kashe mafarauta 16 ‘yan Arewa da ke kan hanyar Elele, Ribas zuwa Kano.

Kisan Hausawa: Gwamnan Edo ya ziyarci Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi bakuncin takwaransa na Edo, Monday Okpebholo, domin tattauna batun kisan da aka yi wa Hausawa.

Taron ya mayar da hankali kan hanyoyin wanzar da zaman lafiya da ƙarfafa haɗin kai tsakanin Kano da Edo bayan rikicin da ya haddasa asarar rayuka.

Gwamna Okpebholo ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Hausawa, ya na mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng