Hanyoyi 4 na Bibiyar Hakkin Hausawan da aka Kashe a Jihar Edo," HRN

Hanyoyi 4 na Bibiyar Hakkin Hausawan da aka Kashe a Jihar Edo," HRN

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa (reshen Najeriya) ta bayyana takaici bisa abin da ta bayyana da tozarta Hausawa da aka yi a jihar Edo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano A tattaunawarsa da Legit, shugaban kungiyar, Kwamred A.A Haruna Ayagi, ya ce mutuwar waɗannan bayin Allah ta munana matuka, duk da cewa ana sa ran sun yi shahada.

Kisan Edo
HRN ta zaburar da gwamnonin Arewa kan kisan Edo Hoto: Barau I Jibrin/Sunusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa yawancin daga cikin mafarautan da aka hallaka, ‘yan asalin jihar Kano ne, lamarin da Kwamred A.A Ayagi ya tabbatar.

Kisan Edo: Hanyoyin bibiyar jinin Hausawa

Jaridar Punch ta wallafa cewa tun bayan da aka yi wa Hausawa kisan gilla ne, matasan ya yankin ke neman a bi masu hakkinsu.

Kara karanta wannan

'Yadda watsi da shirin Sardauna ke jawo asarar rayukan Hausawa,' Yan kasuwa kan kisan Edo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tattaunarsa da Legit, Kwamred A.A Ayagi ya shaida cewa wannan aikin rashin imani da aka tafka a jihar Edo ba abu ne da za a zuba ido har ya wuce ba a dauki mataki ba.

Daga cikin hanyoyin da za a bi wajen kwato masu hakkinsu, Kwamred Ayagi ya ce akwai:

1. Gwamnatin Kano ta bi hakkin Hausawa a Edo

Shugaban gamayyar kungiyoyin fafutukar kare hakkin dan Adam ya bayyana cewa wadanda aka kashe sun fito daga kananan hukumomi daban-daban a Kano.

Ya ce dole ne gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauki kwakkwaran mataki da zai aika da sakon cewa ba za ta lamunci ana kashe mutanenta a gaira, babu dalili.

Kwamred Ayagi ya ce:

“An ci mutuncin ‘yan uwanmu, an ci zarafin ‘yan uwanmu, an tozarta ‘yan uwanmu, an sa sun yi mutuwa ta wulakanta, amma a addinance, mutuwar shahada suka yi da yardarm Allah.”
“Wannan abu da aka yi wa ‘yan jihar Kano, wadanda suka fito daga kananan hukumomin uku, akwai Kibiya, akwai Garko, akwai kuma Bunkure ba za mu bari ba.”

Kara karanta wannan

Alkawarin gwamnan Edo ga iyalan mafarautan Kano da aka kashe a jiharsa

“Mai girma gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir, to aikin yi ya zo. Kungiyarku ta gwamnoni ku tashi tsaye, domin a nemawa masu hakki hakkinsu.”

2. Edo: ‘Yan Majalisar Kano su tashi tsaye

Shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ya ce matakin da Sanata Barau I. Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya fara dauka abu ne mai kyau.

Barau
Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Sai dai, ya ce wannan kawai ba zai isa ba, akwai bukatar sauran ‘yan majalisa su mara masa baya domin a dabbaka neman hakkin jinin bayin Allah a zauren majalisa.

Kwamred Ayagi ya ce:

“Sanata Barau Jibrin, ya ce zai shigar da batun gaban majalisar dattijai, to Sanatoci biyu da muke da su, da wanda kananan hukumomi suka fado a bangaren shi, da wanda ma basu fado ba, ku hadu ku marawa DSP baya, domin a nemawa bayin Allah hakkinsu.”

3. An zaburar da kungiyoyi kan kisan Hausawa

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya yi magana da babbar murya kan kisan 'yan Arewa a Edo

Kwamred A.A Ayagi ya nanata cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ‘yan kasar nan dama su yi zirga-zirga ba tare da shiga fargaba ko an muzguna masu ba.

Ya ce:

“Mu na nan mu na bincike, kowace karamar hukuma mu ji adadin rayukan da nata suka rasa. Ba za mu kyale wannan abu ba, mu masu jimirin kare hakkin dan Adam, mun tashi tsaye.”
“Mu kuma za mu ci gaba da bibiya, za mu kawo jerin kananan hukumomin nan uku, na rayukan da suka rasa domin al'umma su ji su, susan su, domin ba za mu kyale ba.”

Ya ce suna ganawa da gangin mamatan domin mara musu baya wajen nemo hakkin ‘yan uwansu, ‘ya’yansu, iyayensu da mazajensu da aka salwantar.

4. An nemi hadin kan malamai, gwamnonin Arewa

Shugaban kungiyar ya bayyana bukatar da ke akwai na malaman addinin musulunci su tashi haikan wajen taimaka wa gwamnatoci da addu’a domin samun nasarar kwato hakkin jinin da aka zubar.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Kwamred Ayagi ya kuma ce kamata ya yi gwamnonin Arewa su yi magana da murya daya, domin lamarin zai iya tsallakowa kansu idan ba a yi wa tufkar hanci ba cikin gaggawa.

Ya ce:

“Domin in kaza ta ga ana jan hanjin cikin ‘yar uwarta tana dariya, watarana nata za a ja. Ragowar jihohi na Arewa, ya kamata kuma ku yi hobbasa, ku nuna damuwarku, ku nuna takaicinku, ku nuna tir-dinku da wannan abu da ya faru.”

Gwamnatin Kano ta nada kwamitin kisan Edo

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan kisan Hausawa da aka yi a jihar Edo, wanda ya fusata jama'a.

Wannan kwamiti zai gudanar da bincike akan dukkanin lamuran da suka shafi kisan gillar, tare da tabbatar da hakkin mutanen da aka yi wa wannan mummunar aika-aika.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng